Najeriya Ta Yi Rashi: Babban Jami'in Dan Sanda Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Najeriya Ta Yi Rashi: Babban Jami'in Dan Sanda Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi rashi na daya daga cikin manyan jami'an da take da su a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Mataimakin kwamishinan ’yan sanda na Zamfara mai kula da ayyuka, DCP Asbagu Aliyu Muhammad, ya rasu da misalin ƙarfe 1:30 na dare
  • DCP Muhammad ya rasu ne a Asibitin Kwararru na Ahmed Sani Yariman Bakura da ke Gusau, bayan ya yi jinya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda (DCP) mai kula da ayyuka a rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara, Asbagu Aliyu Muhammad, ya rasu.

DCP Muhammad ya rasu ne da misalin ƙarfe 1:30 na dare a Asibitin Kwararru na Ahmed Sani Yariman Bakura da ke Gusau.

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda a Zamfara ya rasu
Mataimakin kwamishinan 'yan sanda a Zamfara, marigayi DCP Asbagu Aliyu Muhammad
Source: Facebook

Ya rasu bayan jinya Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya fitar, wadda Legit Hausa ta samu.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: ADC ta fitar da sunayen 'yan takararta na gwamna a jihohi 28

A cewar sanarwar da kakakin ya fitar, marigayin yana jinya ne sakamakon wata rashin lafiya da ba a bayyana sunanta ba.

Sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin babban jami’in ’yan sanda wanda ya yi wa Rundunar ’Yan Sandan Najeriya hidima cikin sadaukarwa, ƙwarewa da kuma jajircewa wajen gudanar da aikinsa.

Rundunar ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi

Rundunar ta ce rasuwar DCP Muhammad babban rashi ne ga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, abokan aikinsa da kuma daukacin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, CP Ahmad Muhammad Bello, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, ’yan uwansa da abokan aikinsa.

Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kurakuransa, Ya karɓi kyawawan ayyukansa.

An shirya jana’izarsa

CP Bello ya kuma roƙi Allah Ya ba marigayin Aljannatul Firdaus, tare da bai wa iyalansa da abokan aikinsa haƙurin jure wannan babban rashi.

An tsara gudanar da jana’izar marigayin da ƙarfe 2:00 na rana a yau, Lahadi, 6 ga watan Satumban 2026 a masallacin Sheikh Ibn Umar Kanoma, bisa tsarin jana’izar Musulunci.

Kara karanta wannan

An kama dalolin bogi na Naira miliyan 30 ana kokarin shiga da su jama'a

Rundunar ’yan sandan Zamfara ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, tare da roƙon Allah Ya sa ruhinsa ya huta cikin aminci.

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda a Zamfara ya rasu
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan 'yan sanda

Dan sanda ya yi murabus a Bauchi

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ’yan sandan Bauchi ta fara bincike kan lamarin wani jami’i da ya sanar da murabus, yana zargin hana shi samun albashinsa shekaru biyu.

Jami’in mai lamba F/No. 524180, CPL Yusuf Aliyu, ya bayyana murabus ɗinsa daga rundunar ’yan sandan Najeriya ta kafafen sada zumunta.

Dan sandan ya yi ikirarin cewa tsawon wannan lokaci bai samu damar cire albashin da ake biya masa ba, lamarin da ya sa ya bayyana damuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng