'Ya Fi Kasar Belgium Fadi,' Yadda Girman Dajin Sambisa ke Zama Kalubale
- Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya ce faɗin yankunan da ‘yan ta’adda suka mamaye na daga cikin dalilan da ke sa ayyukan ceto da dakile ta’addanci ke wahala
- Ya ce jami’an tsaro na samun nasarar ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a kai a kai, amma ‘yan ta’addan kan tsere cikin manyan dazuzzuka kafin a isa gare su
- Ministan ya ce dajin Sambisa yana da girman da ya kai na ƙasar Belgium, yana mai cewa faɗin yankin na ƙara wahalar da ayyukan sojoji da sauran jami’an tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya kare matakan da gwamnatin Najeriya ke ɗauka wajen yaƙi da rashin tsaro, yana mai cewa faɗin wuraren da ‘yan ta’adda ke fakewa na ƙara wahalar da ayyukan ceto.

Kara karanta wannan
Rashin tsaro: Janar Musa ya ce Najeriya ta yi galaba kan 'yan ta'adda, ya gabatar da dalili
Musa ya bayyana hakan ne yayin wata hira a ranar Alhamis, inda ya ce jami’an tsaro na ceto mutanen da aka yi garkuwa da su akai-akai.

Source: Twitter
Channels Television ta ruwaito cewa ministan ya ce ‘yan ta’addan kan ɓuya cikin manyan dazuzzuka kafin jami’an tsaro su samu cikakken bayani kan inda suke.
Faɗin dajin Sambisa a Borno
Ministan tsaron ya ce faɗin yankin Sambisa na daga cikin manyan ƙalubalen da jami’an tsaro ke fuskanta wajen bin sawun ‘yan ta’adda.
Ya ce dajin Sambisa yana da fadin murabba’in kilomita 923, yana mai cewa girman wurin na sa ayyukan tsaro su zama masu wahala.
“Yankunan nan suna da girma sosai. Don haka wannan gwamnati na fuskantar babban ƙalubale. dajin Sambisa yana da girman da ya kai ƙasar Belgium,”
In ji shi.
Ya ce bai kamata mutane su ɗauki Sambisa a matsayin ƙaramin fili kamar filin ƙwallon ƙafa ba, suna zargin gwamnati da ƙin ɗaukar mataki kan ‘yan ta’addan da ke fakewa a yankin.
‘Yan ta’adda kan ɓuya
Musa ya ce ‘yan ta’addan kan shiga dazuzzuka da zarar sun kammala satar mutane, musamman saboda ana iya ɗaukar lokaci kafin bayanan satar su isa ga jami’an tsaro.
Ya ce hakan na tilasta wa jami’an tsaro shafe lokaci mai tsawo wajen bin sawun masu garkuwa da mutanen da suka shiga cikin dazuzzuka.
“Idan sun sace mutane, kafin bayanin ya isa ga jama'a, mutanen nan sun riga sun shiga cikin daji. Don haka yana ɗaukar lokaci mai tsawo kafin mu bi sawunsu,”
In ji shi.

Source: Original
Sabani kan girman Sambisa
Sai dai bayanin cewa dajin Sambisa ya kai girman Belgium ya bambanta da wasu alkaluman da ake amfani da su wajen bayyana girman yankin.
Rahoton Punch ya nuna cewa Sambisa Game Reserve da aka ayyana a hukumance yana da fadin kusan kilomita 518.
Kididdiga kan faɗin daji sun bambanta sosai, inda aka samu alkaluman da suka ce ya kai kilomita 50,000 zuwa 66,000.
Idan aka yi amfani da kiyasin murabba’in kilomita 60,000, yankin zai kasance kusan ninki biyu na girman Belgium.
Maganar nasarar APC a 2027
A wani labarin, mun ruwaito cewa Christopher Musa, ya yi watsi da ikirarin cewa dan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi da abokin takararsa za su iya kayar da Bola Tinubu.
Musa ya nuna kwarin gwiwar cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da riƙe kujerar shugaban ƙasa tare da samun nasara a zaɓen gwamna da sauran kujeru a Kaduna.
Ya ce duk da ra’ayoyin da wasu ke da shi kan yiwuwar APC ta sha kaye a Kaduna, shi na da tabbacin cewa jam’iyyar za ta yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa, gwamna da sauransu.
Asali: Legit.ng

