Atiku Ya Yi Fallasa a Karin Kudin da Gwamnati Ta Ke Samu a Mulkin Tinubu

Atiku Ya Yi Fallasa a Karin Kudin da Gwamnati Ta Ke Samu a Mulkin Tinubu

  • Karin kudi a lalitar FAAC da Bola Tinubu yake yawan wakar ana samu yaudara ce a ra’ayin Atiku Abubakar
  • Faduwar darajar naira ta rage ainihin darajar kudaden da ake rabawa gwamnatoci duk da cewa adadinsu ya karu
  • Atiku Abubakar ya ce karin albashi zuwa N70,000 ragi ne idan aka yi lissafin darajar dala a 2019 da kuma 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Atiku Abubakar wanda yake fatan zama shugaban Najeriya a badi ya yi watsi da zancen cewa kudin da ake samu a yau ya karu.

Babban ‘dan adawar ya ce surutun da ake yawon yi cewa kudin da ake raba wa daga asusun FAAC ya kara yawa, duk zance ne kawai.

Bola Tinubu da Atiku Abubakar
Shugaba Bola Tinubu da Atiku Abubakar a gidansa Hoto: @DOlusegun/Atiku Abubakar
Source: Twitter

Atiku Abubakar bai ganin kudi sun karu

Alhaji Atiku ya fitar da wani dogon rubutu a daren yau da ke shafinsa na X, yana cewa karin kudin bai inganta rayuwar jama’a ba.

Kara karanta wannan

Pantami ya ce ba ya fargabar cin zaben 2027, ya fadi irin mulkin da zai yi a Gombe

Idan za a yi batun samun karin kudi, ‘dan takaran na ADC yana so a yi la’akari da karya darajar Naira da yawan bashin da ake ciki yanzu.

Atiku ya koka da cewa kudin kasar nan ya rage daraja a lokacin da ake tunkaho cewa kudin da yake zuwa wajen jihohi ya kara yawa.

Bincike daga Agora Policy ya nuna yadda abin da aka raba a FAAC ya karu daga N4.43tr a farkon 2021 zuwa N18.72tr a farkon bana.

Wannan lamari bai burge Atiku ba, ya ce karin kason da ake yi bai nufin tattalin arziki ya kara kyau a karkashin Bola Ahmed Tinubu.

Kudin da suka shigo FAAC sun ragu/karu?

A rubutun, Atiku ya ce a shekarar 2019 an raba $25.6bn a FAAC, hakan yana nufin gwamnatocin tarayya da jihohi sun samu N7.85tr.

Amma a yanzu da ake cewa kudi ya karu har an raba N21.9tr, ainihin abin da aka raba daga asusun FAAC ya ma ragu ne zuwa $14.6bn.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta shiga Aso Rock ta dauke ma’aikacin da ya yi aiki da shugabannin kasa 3

‘Dan dawar ya ce hauhawar farashin kaya ya shafe wannan rudu da ake gani, yake sanar da mutane cewa cigaban mai hakin rijiya ne.

Ashe albashin 'yan Najeriya raguwa ya yi

Atiku ya rubuta:

"Ba za ka karya kudinka ba, ka kyale hauhawar farashi ya yi kaca-kaca da darajarsa sai kuma ka rika yi wa ‘yan Najeriya tunkaho da tulin nairori a matsayin hujjar cewa kasar ta kara arziki."

A 2019 da mafi karancin albashi yake N30, 000 kusan $83 kenan, amma a Mayun 2023 da kudin ya kai N70, 000, a dala bai wuce $53 ba.

Saboda haka ya ce a suna ne kawai albashin ma’aikata ya karu, amma a zahiri raguwa ya yi da $30 tun da yanzu dala ta haura N1, 300.

Idan da gaske ne an ga sauyi a FAAC, Atiku ya ce kamata ya yi a ga wutar lantarki, a samu saukin sufuri, gidaje, asibiti da kuma sana’o’i.

Ta bakin Phrank Shuaibu, ya kuma nemi jin me ya jawo bashin da ake bin gwamnati ya karu alhali ana fada wa mutane kudi ya karu.

Kara karanta wannan

‘Dan takarar shugaban kasa a PRP ya ce gara mulkin soja da tsarin yau

'Yan takaran ADC sun dauki alkawura

Kai albashi fiye da N100, 000 na cikin alkawura takwas da aka ji labari ‘yan takaran ADC a Arewa maso yamma suka dauka a makon nan.

Gwamnatocin ADC a jihohin Arewa maso yamma za su goyi bayan rage kudin man fetur, karin albashi da kuma samar da tsaro a yankin.

'Yan takaran sun sha alwashin ganin sun inganta tsaro kuma za su duba lamarin matsalar ilmin boko a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng