Gwamnatin Buhari tace batun karin albashin Ma’aikata zuwa N30, 000 ba sha yanzu magani yanzu bane

Gwamnatin Buhari tace batun karin albashin Ma’aikata zuwa N30, 000 ba sha yanzu magani yanzu bane

- Fadar Shugaban kasa tayi gargadi cewa har yanzu Buhari bai yi na’am da karin albashi ba

– Wata Majiya daga Fadar Shugabar kasar tayi karin haske game da abin da ya faru a jiya

- Majiyar tace Shugaban kasa ya karbi rahoton aikin da aka yi ne sannan ya kuma mika jinjina

Gwamnatin Buhari b ta amince da karin albashin Ma’aikata zuwa N30, 000 ba tukuna
Akwai sauran aiki kafin Gwamnatin Buhari ta kara albashin Ma’aikata
Asali: UGC

Fadar Shugaban kasa ta ce ana yi wa jawabin da Shugaban kasa Buhari yayi wajen karbar rahoton karin albashin Ma’aikatan Najeriya daga hannun shugaban kwamitin da aka nada Ama Peple wani irin fassaran da bai dace ba.

Wata Majiya daga fadara Shugaban kasar tace Shugaba Muhammadu Buhari bai bayyana cewa yayi amanna da wannan mataki da kwamiti ta dauka na kara albashi ba, illa iyaka dai ya yabawa aikin da kwamitin tayi ne kurum.

KU KARANTA: Cikakken jawabin Shugaba Buhari game da karin albashin Ma’aikata

Wani da ya ki bari a bayyana sunan sa a cikin fadar Shugaban kasar ya bayyanawa menama labarai wannan. Wannan Bawan Allah yace ana ta azarbabin rahoto cewa Shugaba Buhari ya kara albashi nan take wanda sam ba haka bane.

A cewar wannan mutumi, dole sai an mikawa Majalisar zartarwa na Gwamnatin Tarayya watau FEC da kuma Majalisar da ke aiki kan tattalin arzikin Najeriya na NEC domin duba aikin da wannan kwamiti tayi kafin a je ko ina a Gwamnati.

Haka-zalika mun kuma samu labari cewa sai an aikawa Majalisar Tarayya kudirin game da karin albashin kafin Gwamnati ta soma biyan Ma’aikatan kasar sabon albashi. Majiyar tace ba Shugaban kasa bane kurum ke da iko a lamarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng