Wa Ya Fi Gaskiya tsakanin El Rufai da Ministan Tsaro? Dattawan Arewa Sun Magantu
- Ƙungiyar dattawan Arewa ta yi magana da Ministan Tsaro Christopher Musa ya soki tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai
- Dattawan sun ce gwamnatin El-Rufai ta shekaru takwas ta bar Kaduna cikin rarrabuwar kai, manufofi masu jawo matsala
- Ƙungiyar ta bukaci a mayar da hankali kan hujjoji wajen tantance zarge-zargen, tare da guje wa amfani da ƙabila, addini ko yankin Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Ƙungiyar Coalition of Northern Elders for Peace and Development, CNEEPD, ta goyi bayan Ministan Tsaro, Christopher Musa kan sukar Nasir El-Rufai.
Ƙungiyar ta ce kalaman Musa sun bayyana abin da ta kira gaskiyar gwamnatin El-Rufai, wadda ta shafe shekaru takwas tana mulkin Kaduna.

Source: Facebook
A wata sanarwa da Injiniya Zana Goni, Dr Mohammed Suleman da Farfesa John Anaho suka sanya wa hannu, dattawan sun zargi gwamnatin El-Rufai da rarrabuwar kai, cewar The Nation.

Kara karanta wannan
Janar Christopher Musa ya kira ruwa, lauyoyin El Rufai sun nemi N10bn da wasu bukatu
Zargin da ake yi wa El-Rufai
Sun kuma zargi gwamnatin da aiwatar da wasu manufofi masu rikici da kuma rashin kyakkyawan shugabanci, waɗanda suka ce sun bar matsaloli a jihar.
Dattawan sun ce bai kamata a zargi Musa saboda ya yi magana kan tarihin gwamnatin El-Rufai ba, domin batutuwan sun cancanci binciken jama'a.
Ya ce:
“Janar Christopher Musa bai ƙirƙiri tarihin Kaduna ba, ya yi magana ne kan gaskiyar da ya kamata ’yan Najeriya su kasance da ƙarfin gwiwar fuskanta."
CNEEPD ta ce bai kamata a auna aikin tsohuwar gwamnati da ayyukan raya ƙasa da ikirarin nasarori kawai ba, har da tasirinta ga zaman lafiya.
Ta ce ya kamata a duba yadda gwamnatin ta shafi haɗin kan jama'a, cibiyoyin gwamnati da rayuwar al'ummar Kaduna a lokacin mulkinta.
Ƙungiyar ta yi zargin cewa wasu manufofi da matakan gwamnatin El-Rufai sun haifar da ƙiyayya tsakanin wasu al'ummomi, tare da ƙara rikice-rikicen siyasa.

Source: Facebook
Shawarar da dattawan suka bayar
Dattawan sun ce ya kamata a tattauna waɗannan zarge-zarge bisa hujjoji, tare da jaddada cewa barin mulki ba ya kare tsohon gwamna daga bincike.
Ƙungiyar ta kuma yi watsi da ƙoƙarin mayar da ce-ce-ku-ce kan kalaman Musa zuwa rikicin yanki, tana gargadin Arewa kada ta kare shugabanni saboda asalinsu.
Ta ƙalubalanci masu kare Nasir El-Rufai da su mayar da martani ga zarge-zargen da hujjoji, maimakon kai hari ga Ministan Tsaro saboda bayyana matsalolin, cewar Punch.
Dattawan sun sake tabbatar da goyon bayansu ga Musa, suna bayyana shi a matsayin babban jigo na ƙasa wanda ya kamata a ɗauki ra’ayinsa da muhimmanci.
Sun ce tsohon aikinsa na Babban Hafsan Tsaron Najeriya ya ba shi ƙwarewa da dama kan matsalolin tsaro da zamantakewar siyasar ƙasar.
Ta kara da cewa:
“Mun goyi bayan Janar Christopher Musa saboda yin magana kan gazawa da rarrabuwar da ta shafi Kaduna ba cin amanar Arewa ba ne.

Kara karanta wannan
‘Mulkinsa ya shafi kowa a Kaduna': Jigon APC ya kare kalaman minista kan El Rufai
“Muradin al’ummar Kaduna ya fi muradin siyasar kowane tsohon gwamna girma. Muradin Najeriya ya fi burin kowane mutum muhimmanci.”
CNEEPD ta yi kira da a gudanar da bincike na gaskiya kan ikirare-ikiraren da suka shafi gwamnatin El-Rufai, tare da mayar da hankali kan hujjoji.
El-Rufai: Dan APC ya kare kalaman ministan tsaro
An ji cewa dan jam'iyyar APC a Bauchi, Khamis Musa Darazo, ya gargadi masu sharhi kan siyasa da kada su juya kalaman Ministan Tsaro.
Darazo ya ce korafe-korafen mulkin Nasir El-Rufai, sun shafi daukacin mutanen Kaduna, ba ’yan Kudancin Kaduna kaɗai ba.
Ya bukaci ’yan Najeriya su mayar da hankali kan zaman lafiya, adalci, haɗin kai da tsaro, maimakon juya kalaman ministan.
Asali: Legit.ng
