Magana Ta Girma: Iyalan El Rufai Sun Yi Martani Mai Zafi ga Janar Christopher Musa

Magana Ta Girma: Iyalan El Rufai Sun Yi Martani Mai Zafi ga Janar Christopher Musa

  • Iyalan tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai sun musanta zargin Janar Christopher Musa cewa tsohon gwamnan ya shirya kashe-kashe a Kudancin Kaduna
  • Iyalan sun buƙaci Ministan Tsaron ya gabatar da sahihiyar hujja ko ya janye zargin tare da ba da haƙuri a bainar jama’a cikin kwanaki bakwai
  • Sun yi barazanar ɗaukar matakan shari’a idan Janar Musa bai gabatar da hujja ko ya janye zargin da aka yi ba kan tsohon gwamnan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Iyalan Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), tsohon Gwamnan Kaduna kuma jagoran adawa na ADC, sun nuna matuƙar damuwa kan wani zargi da Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya yi

Iyalan sun ce Janar Musa ya yi zargin ne a ranar 3 ga Satumba 2026 yayin wata hira kai tsaye da aka gudanar a shirin Politics Today na Channels Tv.

Kara karanta wannan

Dalung ya jefawa Christopher Musa tambayoyi kan zargin Nasir El Rufa'i

Iyalan El Rufai sun ta so Janar Musa a gaba
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai Hoto: Bello El-Rufai
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bello El-Rufai ya fitar a ​shafinsa na Facebook ranar Litinin, 7 ga watan Satumban 2026.

An zargi El-Rufai da shirya kashe-kashe

A cewar sanarwar iyalan, yayin shirin, Janar Musa ya yi zargin cewa Mallam Nasir El-Rufai ya shirya kashe-kashe a Kudancin Kaduna a lokacin da yake matsayin Gwamnan Kaduna.

Iyalan sun bayyana zargin a matsayin babban tuhuma, suna cewa Ministan bai gabatar da wata hujja da za ta tabbatar da ikirarinsa ba.

Sun ce duk da cewa Janar Musa yana da ’yancin samu da bayyana ra’ayinsa na kashin kansa, su ma iyalan El-Rufai suna da haƙƙin neman a tabbatar da irin wannan zargi mai girma da sahihiyar hujja.

An bai wa Janar Musa kwanaki 7

Iyalan sun ce idan babu hujjar da za ta tabbatar da zargin, suna kira ga Janar Musa da ya janye kalaman nasa a bainar jama’a ta hanyar amfani da kafar da aka yi zargin a kanta.

Kara karanta wannan

APC ta shiga matsala, manyan jam'iyya sun fita za su fara adawa da Tinubu

Saboda haka, iyalan sun bai wa Ministan Tsaron wa’adin kwanaki bakwai daga ranar fitar da sanarwar domin ya gabatar da hujjar da ke tabbatar da zargin ko kuma ya yi cikakken bayani na janye zargin tare da ba da haƙuri a bainar jama’a.

“A yayin da babu irin wannan hujja, muna kira gare shi da ya janye zargin a bainar jama’a ta hanyar kafar da aka yi kalaman a kanta.”

Iyalan El-Rufai sun yi barazanar zuwa kotu

Iyalan El-Rufai sun ce idan Janar Musa bai cika ɗaya daga cikin waɗannan buƙatun ba cikin wa’adin da aka ba shi, ba za su samu wani zaɓi ba face amfani da dukkan matakan shari’a da doka ta tanada.

Sun ce za su ɗauki matakan ne domin mayar da martani kan abin da suka bayyana a matsayin zarge-zargen da ba a tabbatar da su da hujja ba.

Christopher Musa ya yi zarge-zarge kan El-Rufai
Miniatan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa Hoto: Ministry of Defence Nigeria
Source: Twitter

Hadimin Uba Sani ya kare Janar Musa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Victor Mathew Bobai, ya kare Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), kan kalamansa game da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai.

Bobai wanda hadimin Gwamna Uba Sani ne, ya ce bai dace a fassara kalaman Janar Musa da ya yi yayin wata hira tattaunawa ba a matsayin hari na kashin kai ko kuma siyasa kan El-Rufai ba..

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng