Tirkashi: An Samu Kungiyar da Za Ta ba Janar Musa Hujjoji kan Zarge Zargen da Ya Yi Wa El Rufai

Tirkashi: An Samu Kungiyar da Za Ta ba Janar Musa Hujjoji kan Zarge Zargen da Ya Yi Wa El Rufai

  • Kungiyar Middle Belt Forum ta bukaci Christopher Musa ya yi watsi da buƙatar iyalan Nasir El-Rufai ta janye zargin da aka yi wa tsohon gwamnan
  • Iyalan El-Rufai sun ba Musa wa’adin kwanaki bakwai ya gabatar da hujjoji kan zargin shirya kisan mutane a Kudancin Kaduna
  • MBF ta ce tana da isassun hujjoji da za su goyi bayan kalaman ministan, yayin da El-Rufai ya yi barazanar kai ƙara kan Janar Musa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Kungiyar Middle Belt Forum (MBF) ta bukaci Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), da ya yi watsi da buƙatar iyalan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

Kungiyar ta ce Musa bai kamata ya janye zargin cewa El-Rufai yana da hannu wajen kashe-kashen da suka faru a Kudancin Kaduna a lokacin mulkinsa ba.

Kara karanta wannan

Wa ya fi gaskiya tsakanin El Rufai da ministan tsaro? Dattawan Arewa sun magantu

Lauyoyin El-Rufai sun taso Janar Musa a gaba
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai Hoto: Bello El-Rufai
Source: Facebook

Mai magana da yawun MBF, Luka Binniyat, ya ce kungiyar tana da isassun hujjojin da za su tabbatar da zargin da ministan ya yi, cewar rahoton jaridar Leadership.

Iyalan El-Rufai sun ba Musa kwanaki 7

A baya, iyalan El-Rufai sun bai wa Janar Musa wa’adin kwanaki bakwai da ya gabatar da hujjojin da ke tabbatar da zargin cewa tsohon gwamnan ya shirya kisan mutane a Kudancin Kaduna.

Iyalan sun kuma yi barazanar ɗaukar matakin shari’a a kan ministan idan ya gaza tabbatar da zargin ko kuma ya janye shi tare da ba da haƙuri a bainar jama’a cikin wa’adin da suka kayyade.

MBF ta goyi bayan Janar Musa

Sai dai MBF ta ce ya kamata Janar Musa ya tsaya kan kalamansa maimakon janyewa ko neman afuwa.

Luka Binniyat ya ce MBF tana goyon bayan ministan kan kalaman da ya yi game da El-Rufai.

“Middle Belt Forum tana tsaye tsayin daka tare da ministan tsaro kan zarge-zargen da ya yi wa Rufai kwanan nan. Abin da ministan ya fada gaskiya ne, kuma muna da isassun hujjojin da za su goyi bayansa.” In ji shi.

Kara karanta wannan

Janar Christopher Musa ya kira ruwa, lauyoyin El Rufai sun nemi N10bn da wasu bukatu

Ya ƙara da cewa bai kamata Janar Musa ya janye kalamansa ko ya nemi afuwa ba.

Kungiyar ta kuma yi zargin cewa ayyuka da kalaman El-Rufai, ko rashin ɗaukar mataki a lokacin da ya dace, sun taimaka wajen ƙara yawaitar kashe-kashen jama’a a Kudancin Kaduna.

MBF ta yi wani ƙarin zargi mai tsanani cewa El-Rufai ya kamata ya fuskanci tuhume-tuhume a gaban Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) kan zargin aikata laifukan cin zarafin bil’adama.

Janar Musa bai mayar da martani ba

Har zuwa lokacin kammala rahoton, Ministan Tsaro, Christopher Musa, bai fito ya mayar da martani kan buƙatun iyalan El-Rufai ko barazanar shari’ar ba.

Haka kuma, Leah Katung-Babatunde, mataimakiyar Janar Musa ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, ba ta amsa saƙonni ko kiran waya da aka yi mata domin jin ta’addamar da ministan kan lamarin ba.

Janar Musa ya samu goyon baya
Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa Hoto: Ministry of Defence Nigeria
Source: Facebook

Kungiyar Arewa ta goyi bayan Janar Musa

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Coalition of Northern Elders for Peace and Development, CNEEPD, ta goyi bayan Ministan Tsaro, Christopher Musa kan sukar Nasir El-Rufai.

Ƙungiyar ta ce kalaman Musa sun bayyana abin da ta kira gaskiyar gwamnatin El-Rufai, wadda ta shafe shekaru takwas tana mulkin Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng