‘Mulkinsa Ya Shafi Kowa a Kaduna’: Jigon APC Ya Kare Kalaman Minista kan El Rufai
- Jigon APC a Bauchi, Khamis Musa Darazo, ya gargadi masu sharhi kan siyasa da kada su juya kalaman Ministan Tsaro
- Darazo ya ce korafe-korafen mulkin Nasir El-Rufai, sun shafi daukacin mutanen Kaduna, ba ’yan Kudancin Kaduna kaɗai ba
- Ya bukaci ’yan Najeriya su mayar da hankali kan zaman lafiya, adalci, haɗin kai da tsaro, maimakon juya kalaman ministan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Dan jam’iyyar APC a Bauchi, Khamis Musa Darazo, ya tabo batun ce-ce-ku-ce game da kalaman ministan tsaro kan Nasir El-Rufai.
Darazo ya gargadi masu sharhi kan al’amuran jama’a da kada su danganta kalaman Ministan Tsaro da kabilanci ko addini.

Source: Facebook
Dan a mutun APC da Bola Tinubu ya bayyana haka ne yayin zantawa da wakilin Legit Hausa a yau Asabar 5 ga watan Satumbar 2026.
An gargadi mutane kan juya kalaman ministan tsaro
Darazon ya ce bai dace a fassara kalaman Janar Christopher Musa ta fuskar ƙabila, yanki ko addini ba, bayan kalaman da ya yi yayin wata tattaunawar talabijin.
Ya bayyana haka ne ranar Asabar a Bauchi, inda ya ce salon mulkin tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ya shafi mutane a faɗin jihar.
Ya ce abin takaici ne yadda wasu masu sharhi ke ƙoƙarin juya kalaman ministan fassarar da ta shafi wani yanki ko addini.
Darazo ya ce lokacin da ministan ya yi amfani da kalmar “mutanenmu”, ya kamata a fahimci cewa yana magana ne kan daukacin mutanen Kaduna.
Ya ce:
“Gaskiyar magana ita ce, korafe-korafen da suka shafi salon mulkin Nasir El-Rufai sun shafi mutanen Kaduna baki ɗaya, ba ’yan Kudancin Kaduna kaɗai ba.
“Ministan bai soki Nasiru El-Rufai ba ne saboda shi Musulmi ne. Wannan fassara ba ta da tushe ko kaɗan.”
Khamis Musa Darazo ya jaddada cewa Christopher Musa bai soki Nasir El-Rufai saboda addininsa ba, yana mai cewa irin wannan fassara ba ta dace ba.
Darazo ya ce bai kamata a karkatar da batun zuwa wani labari na addini ko na yanki ba, domin hakan na iya ƙara rarraba al’umma.

Source: Twitter
'Kokartin da Tinubu, Uba Sani ke yi'
Darazo ya kammala da cewa, “Kaduna mallakin dukkan mutanenta ce, kuma babu wata al’umma da ya kamata a sa ta ji cewa abubuwan da ta fuskanta ba su da muhimmanci.”
Ya ce:
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani duk Musulmai ne, amma dukansu suna ƙoƙarin rage rarrabuwar kai da kuma inganta haɗin kan jama’a.
“A matsayina na mai goyon bayan Shugaba Tinubu kuma wanda ya yi imani sosai da haɗin kan ƙasa, ba zan goyi bayan ƙoƙarin mayar da wannan batu rikicin addini ko na yanki ba.
“Al’ummomi daban-daban sun fuskanci ƙalubale iri-iri, kuma ba adalci ba ne a share abubuwan da wasu suka fuskanta ta hanyar gabatar da batun kamar ya shafi wani ɓangare kaɗai.”

Kara karanta wannan
Dan Majalisa ya kai ƙorafi gaban shugaban Amurka kan abin da ake wa Tinubu a Najeriya
Jigon APC ya bukaci ’yan Najeriya da su guji mayar da batun rikicin addini ko na yanki, yana mai cewa ba zai goyi bayan duk wani yunƙuri ba.
Darazo ya ƙara bayyana cewa kalmar “mutanenmu” ya kamata a fahimce ta da ma’anar daukacin mutanen Kaduna, ba wani yanki na jihar kaɗai ba.
Muslim/Muslim: Darazo ya kare kalaman Jingir
Mun ba ku labarin cewa matashin ɗan siyasa Khamis Musa Darazo ya soki masu zagin Sheikh Sani Yahaya Jingir, yana mai cewa irin wannan hali rashin tarbiyya ne.
Darazo ya ce bai kare Sheikh Jingir ba saboda goyon bayan gwamnatin Tinubu kawai, sai dai ya yi Allah wadai da cin mutuncinsa.
Ya bayyana cewa malamin na da ’yancin bayyana ra’ayinsa, tare da yi masa addu’ar Allah Ya ƙara masa lafiya, daraja da tsawon rai.
Asali: Legit.ng

