Rigimar El Rufai da Ministan Tsaro: Jama'atu Nasril Islam da CAN Sun Tsoma Baki

Rigimar El Rufai da Ministan Tsaro: Jama'atu Nasril Islam da CAN Sun Tsoma Baki

  • Shugabannin addinai Musulmi da Kirista a Kudancin Kaduna sun yi kira ga zaman lafiya, yayin da Nasir El-Rufai ya nemi N10bn
  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya nemi Ministan Tsaro, Christopher Musa ya ba shi hakuri, tare da biyan N10bn saboda zargin bata masa suna
  • Kungiyar JNI da CAN sun bukaci jama'a su guji mayar da rikicin zuwa na addini ko kabilanci, yayin da wata kungiya ta goyi bayan Musa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Shugabannin addinan Musulunci da Kiristanci a Kudancin Kaduna sun yi kira ga zaman lafiya da fahimtar juna, bayan kalaman Ministan Tsaro, Christopher Musa.

Shugabannin addinan, karkashin kungiyoyin Jama’atu Nasril Islam da CAN, sun yi wannan kiran yayin taron zaman lafiya a Kafanchan, Kaduna.

Kungiyoyin Musulmi da Kirista sun shiga rigimar El-Rufai da ministan tsaro
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da ake tsare da shi. Hoto: Nasir El-Rufai.
Source: Facebook

Matakin da iyalan El-Rufai ke shirin dauka

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa bai kamata a aminta da Pantami ya mulki jihar Gombe ba'

Wannan na zuwa ne yayin da El-Rufai ya bukaci a biya shi N10bn tare da ba shi hakurin jama'a saboda zargin bata masa suna, cewar Punch.

Bukatar ta kunshi wata wasika da lauyoyin El-Rufai suka aike wa Musa a ranar Litinin, 7 ga Satumba, 2026, daga Chambers of Ubong Akpan.

An wallafa wasikar ne ta Bello El-Rufai, dan tsohon gwamnan Kaduna kuma dan majalisar wakilai ta tarayya a Najeriya.

Matakin shari’ar ya biyo bayan bayyanar Musa a shirin Politics Today na Channels Television ranar 3 ga Satumba, inda ya yi magana kan rashin tsaro.

Lauyoyin El-Rufai sun bayyana wadannan kalamai a matsayin karya da bata suna, suna cewa sun nuna tsohon gwamnan a matsayin wanda ya shirya kisan mutane.

Sun ce kalaman sun kuma nuna El-Rufai a matsayin wanda ya biya 'yan bindiga, ya zalunci abokan hamayya ta hanyar rushe gidaje, sannan ya raba Kaduna bisa addini.

Kalaman ministan tsaro sun bar baya da kura
Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Twitter

El-Rufai vs Musa: Martanin JNI da CAN

Da suke magana kan lamarin, shugabannin addinan CAN da JNI a Kudancin Kaduna sun bukaci a magance sabanin ta hanyar tattaunawa, ba tada zaune tsaye ba.

Kara karanta wannan

Tirkashi: An samu kungiyar da za ta ba Janar Musa hujjoji kan zarge zargen sa ya yi wa El Rufai

Shugaban Majalisar Limamai ta Kudancin Kaduna, Imam Muhammed Kabir Kasim, ya bayyana Musa a matsayin gogaggen jami’in soja da ma’aikacin gwamnati.

Kasim ya bukaci 'yan Najeriya su yi la’akari da mahallin kalaman Musa kafin su yanke hukunci ko fassara su ta wata hanya.

Haka kuma, shugaban JNI na Kudancin Kaduna da Jema’a, Mallam Garba Alhassan Adamu, ya ce mu’amalarsa da Musa ta nuna masa cewa ministan ya damu da zaman lafiya.

A cewarsa, tarihin ministan da kuma saninsa da kalubalen Kudancin Kaduna ya kamata su sa masu ruwa da tsaki su tuntube shi cikin lumana.

Adamu ya bukaci shugabannin addinai su yi taka-tsantsan da kalaman da suke amfani da su wajen tattauna batutuwan kasa masu matukar sarkakiya.

Shugaban CAN na Karamar Hukumar Kachia, Rabaran Ezekiel Jock, ya ce jami’an gwamnati ma mutane ne, don haka kalamansu na iya samun fassarori daban-daban.

Jock ya bukaci Musulmai da Kiristoci su guji mayar da sabani kan kalaman jami’an gwamnati zuwa rikicin addini ko na yankuna.

Dattawan Arewa sun kare kalaman ministan tsaro

An ji cewa wata kungiyar dattawan Arewa ta yi magana da Ministan Tsaro Christopher Musa ya soki tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai.

Kara karanta wannan

Wa ya fi gaskiya tsakanin El Rufai da ministan tsaro? Dattawan Arewa sun magantu

Dattawan sun ce gwamnatin El-Rufai ta shekaru takwas ta bar Kaduna cikin rarrabuwar kai, manufofi masu jawo matsala.

Kungiyar ta bukaci a mayar da hankali kan hujjoji wajen tantance zarge-zargen, tare da guje wa amfani da ƙabila, addini ko yankin Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.