Ma'aikatan Gwamnati Sun Hada kai, Sun Bukaci Maido Tallafin Man Fetur

Ma'aikatan Gwamnati Sun Hada kai, Sun Bukaci Maido Tallafin Man Fetur

  • Ƙungiyar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ta buƙaci gwamnatin tarayya ta dawo da tallafin man fetur domin rage tsadar rayuwa a Najeriya
  • Ƙungiyar ta kuma buƙaci a fara biyan alawus ɗin tsadar rayuwa na dindindin da kuma basussuka da alawus da suke bin gwamnati
  • Ma’aikatan sun kuma nemi a aiwatar da cikakken sabon mafi ƙarancin albashi da biyan dukkan basussukan da suka taso tun daga watan Yulin 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ƙungiyar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dawo da tallafin man fetur tare da samar da wani alawus na dindindin da zai taimaka wa ma’aikata wajen fuskantar hauhawar farashi.

Buƙatun na kunshe cikin wata takarda da jagoran ta, Andrew Emelieze, ya sanya wa hannu ranar Litinin kuma aka rabawa manema labarai a Abuja.

Kara karanta wannan

'Trump na goyon bayan shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur

Gidan mai da shugaba Bola Tinubu
Gidan mai a hagu, shugaba Bola Tinubu a dama. Hoto: Getty ImagesBayo Onanuga
Source: Getty Images

Korafin ma'aikatan Najeriya

Punch ta wallafa cewa kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya ta samar da “alawus na tsadar rayuwa na dindindin” wanda za a rika daidaita shi bisa halin da tattalin arzikin ƙasa ke ciki.

Ta kuma bukaci a dawo da tallafin man fetur domin rage matsalar tsadar rayuwa, tare da samar da tsarin kula da farashin kayayyaki da kuma ɗaukar matakan ƙarfafa darajar naira.

Rahoto ya nuna cewa ma’aikatan sun nuna damuwa kan yadda farashin kayayyaki ke ci gaba da tashi, musamman farashin siminti.

Sun yi kira ga gwamnati da ta shiga samar da wasu muhimman abubuwan buƙata na jama’a da yawa, domin samar da guraben ayyukan yi da kuma bunƙasa masana’antu.

Batun albashi da alawus

Ƙungiyar ta kuma nemi a fara aiwatar da kashi 40 cikin 100 na alawus na musamman da kuma biyan ragowar kuɗin d asuke bin gwamnati tun bayan aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi a watan Yulin 2024.

Kara karanta wannan

Zaɓe ya zo, Gwamna Uba Sani ya juyo kan sarakunan gargajiya, zai masu abin alheri

Ta kuma buƙaci cikakken aiwatar da gyaran albashi da ya biyo bayan sabon mafi ƙarancin albashi tare da biyan dukkan bashin da ya taso tun daga Yulin 2024.

A bangaren jin daɗin ma’aikata, ƙungiyar ta bukaci a samar da wani alawus na tallafa wa iyalan ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Ta ce irin wannan tallafi na daga cikin matakan da za su inganta rayuwar ma’aikata a daidai lokacin da ake fama da matsin tattalin arziki.

Wani mutum a gidan mai
Mai sayar da fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ƙungiyar ta kuma nemi a biya dukkan albashi da sauran basussukan da ake bin gwamnatin tarayya, musamman basussukan ƙarin girma da suka taru.

Dangote na sayar da hannun jari

A wani labarin, mun ruwaito cewa attajirin Afrika, Aliko Dangote, ya bayyana cewa a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa zai fara sayar da hannun jarin matatar man fetur din shi.

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ne ya bayyana hakan yayin bikin sanya hannu kan takardun sayar da hannun jarin a Legas.

Dangote ya kuma ce yana son mutanen da ba su da kuɗi masu yawa su samu damar zama masu hannun jari a matatar, inda ya bayyana mafi ƙarancin adadin hannun jarin da mutum zai iya saya.

Wanda ya tantance Ibrahim Yusuf, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng