'Kowa zai Iya Saye,' Dangote Ya Bude Kofar Sayar da Hannun Jari a Matatar Shi

'Kowa zai Iya Saye,' Dangote Ya Bude Kofar Sayar da Hannun Jari a Matatar Shi

  • Aliko Dangote ya bayyana cewa direbobi, leburori, ma’aikata, ’yan kasuwa da sauransu za su samu damar mallakar hannun jari a matatar shi
  • Dan kasuwar ya ce shirin sayar da hannun jarin matatar zai kunshi hannun jari biliyan 4.1, inda za a sayar da kowanne a kan N525.
  • Dangote ya bayyana shirin a matsayin wani tsari na bai wa mutane dama su mallaki wani kaso na matatar, yayin da ake sa ran zai tara sama da Naira tiriliyan 2

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos – Aliko Dangote ya rattaba hannu kan takardun rajistar shirin fara sayar da hannun jarin matatar shi da Kamfanin Petrochemicals FZE.

Dangote ya bayyana cewa shirin zai bai wa mutane daga sassa daban-daban damar mallakar hannun jari a matatar, ciki har da direbobi, leburori, ma’aikata da sauransu.

Kara karanta wannan

Yadda aka jefar da jarirai a kango cikin ban tausayi bayan an haife su a Abuja

Matatar Dangote da ke jihar Legas
Alhaji Aliko Dangote da matatar shi da ke Legas. Hoto: Getty Images|Dangote Industries
Source: Facebook

Punch ta rahoto cewa Dangote ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin bikin rattaba hannu kan takardun shirin a Lagos, inda ya kira shirin “sayar da hannun jari ga jama’a”.

Hannun jari biliyan 4.1 za a sayar

Rahoton da kamfanin ya wallafa a Facebook ya nuna cewa shirin ya kunshi hannun jari na yau da kullum biliyan 4.1, inda za a sayar da kowanne a kan N525.

A cewar Dangote, ana sa ran shirin zai tara sama da Naira tiriliyan 2, yayin da mafi ƙarancin adadin hannun jarin da mutum zai iya saya shi ne guda 10.

Ya ce manufar shirin ba wai tara kuɗin faɗaɗa matatar kawai ba ce, illa kuma bai wa jama'a dama su mallaki wani kaso a cikin wannan babbar masana'anta.

“Abin da muke ƙoƙarin yi shi ne tabbatar da cewa yawancin direbobinmu, masu girkinmu, ma’aikatanmu, manajojinmu da kowa sun samu damar mallakar wani kaso a wannan matatar,”

Kara karanta wannan

An kama Kirista ta yi shigar Musulunci tana satar yara a Abuja

In ji Dangote.

Mutanen da za su samu dama

Dangote ya bayyana cewa babu wariya wajen mallakar hannun jarin, yana mai cewa ana son bai wa mutane da ke zaune a nahiyar Afirka dama su kasance cikin shirin.

Ya ce hakan zai ba mutane damar amfana da ci gaban matatar a yanzu da kuma nan gaba. Dangote ya kuma bayyana yiwuwar masu hannun jarin samun riba da za a biya a dalar Amurka nan gaba.

Ya ce hakan na iya bai wa masu hannun jari damar amfani da ribar wajen biyan wasu buƙatun da ake gudanarwa a wajen Najeriya.

Yaushe za a fara sayarwa?

Takardar shirin ta nuna cewa an kimanta darajar hannun jarin da ake bayarwa da kusan dala biliyan 1.6, yayin da aka kimanta darajar matatar da kusan dala biliyan 49.

Ana sa ran za a buɗe shirin sayar da hannun jarin ranar 14 ga Satumba, 2026, sannan a rufe shi ranar 13 ga Oktoba.

Kara karanta wannan

Bashin biliyoyi ya taru a kan Kiyosaki da ke koya wa mutane dabarun yin kudi

Aliko Dangote a matatar shi
Aliko Dangoe tare da wasu ma'aikanatan shi. Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Dan kasuwar ya nuna godiya ga Allah da ya ba shi damar ganin matatar ta kai matakin fara sayar da hannun jari.

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da sauran ‘yan Afirka da su jajirce wajen jagorantar sauye-sauyen tattalin arziki da samar da dama ga jama'a.

Batun raba mai a jihohi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Matatar Dangote ta faɗaɗa shirin kai kayayyakin man fetur kyauta zuwa jihohin Kano, Imo, Anambra da Nasarawa.

Matatar ta ce shirin zai taimaka wajen rage kuɗin jigilar man fetur da ‘yan kasuwar mai masu zaman kansu ke kashewa, tare da samar da damar rage farashin man fetur.

Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Mai ta Najeriya, IPMAN, ta yi maraba da matakin, tana mai cewa zai rage wasu daga cikin matsalolin kuɗi da na sufuri da ke fuskantar ‘yan kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng