Maimakon Dawo da Tallafin Mai, Gwamna Ya Kawo Hanyar Karya Farashin Fetur a Najeriya

Maimakon Dawo da Tallafin Mai, Gwamna Ya Kawo Hanyar Karya Farashin Fetur a Najeriya

  • Gwamna Seyi Makinde ya ce ba ya goyon bayan dawo da tallafin man fetur, sai dai a rage farashin fetur ga 'yan Najeriya
  • Dan takarar shugaban kasa na APM ya ce bai kamata a sayar wa 'yan Najeriya danyen mai kamar kasar ba ta samar da shi ba
  • Makinde ya bukaci a samar da cikakken bayani kan yadda ake kayyade farashin fetur a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APM, Gwamna Seyi Makinde, ya yi watsi da batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya.

Makinde, wanda shi ne gwamnan jihar Oyo, ya ce kamata ya yi a mayar da hankali wajen nemo hanyoyin da za a rage farashin fetur ga 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

2027: An samu gwamna na farko da ya goyi bayan tsarin Atiku na rage tsadar fetur a Najeriya

Gwamna Makinde.
Gwamna Seyi Makinde a wurin kaddamar da yakin neman zabensa na shugaban kasa Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin kaddamar da ofishin yakin neman zabensa na shugaban kasa a Abuja, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Makinde ya yi bayani kan tallafin fetur

Makinde yana mayar da martani ne kan yadda wasu suka fahimci wata takarda da ya wallafa kwanan nan, inda ya bayyana matsayarsa kan tallafin man fetur da kuma tsarinsa mai suna Reset Nigeria Agenda.

A cikin takardar da ya wallafa ranar Alhamis, Makinde ya ce 'yan Najeriya suna tambayar tambayoyin da ba su dace ba kan amfanin cire tallafin man fetur.

Ya ce bai kamata a dauki batun a matsayin zabi tsakanin ba da tallafin man fetur ko kuma barin 'yan Najeriya su biya cikakken farashin kasuwa ba.

A cewarsa, ya kamata a mayar da hankali kan yadda ake kayyade farashin fetur a kasa mai samar da danyen mai kamar Najeriya.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya ware gwamnonin Arewa, ya fadi matsalan da za su fuskanta a zaben 2027

"Ba na son a dawo da tallafi"

Gwamna Makinde ya ce wasu 'yan Najeriya sun yi kuskuren fahimtar matsayarsa, inda suka dauka cewa yana kira ne a dawo da tallafin man fetur.

Makinde ya yi amfani da wani misali wajen bayyana matsayarsa kan batun, inda ya ce:

"Bari in bayyana matsayina cikin sauki da wannan misalin. Idan wata al'umma ce ke noma abinci, bai kamata mutanen wannan al'ummar su rika sayen abincin kamar an yi tafiyar rabin duniya da shi kafin ya isa gare su ba."

Makinde ya yi magana kan danyen mai

Dan takarar shugaban kasa ya tambayi dalilin da ya sa ake kayyade farashin danyen mai da ake bai wa matatun Najeriya kamar kasar ba ta samar da danyen mai.

Ya ce wajibi ne man Najeriya ya samar wa 'yan kasar wani anfani na zahiri da za a iya gani da aunawa.

Makinde.
Magoya bayan APM a wurin kaddamar da kamfen dan takarar shugaban kasa, Seyi Makinde Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

SoGwamnan Oyo ya ce akwai bukatar a kara bayyana komai a fili a tsarin harkar man fetur domin 'yan Najeriya su fahimci yadda ake tantance farashin fetur.

Kara karanta wannan

Atiku ya nuna yadda kalaman IPMAN suka 'kunyata' Tinubu kan dawo da tallafin fetur a Najeriya

"Muna bukatar cikakken bayani kan tsarin man fetur, daga samarwa da ware danyen mai domin amfani a gida, zuwa tacewa, sufuri, rarrabawa, haraji da ribar masu sayarwa."

Peter Obi ya hango cancantar Makinde

Kun ji cewa ɗan takarar shugaban kass na NDC, Peter Obi ya bayyana cewa dan takarar APM, Seyi Makinde, ya cancanci zama shugaban Najeriya.

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya yi kira ga 'yan siyasa su hada kai gabanin babban zaben shekarar 2027, yana mai cewa bai kamata neman shugabancin Najeriya ya kasance bisa son rai ko gaba tsakanin 'yan siyasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262