Zaɓe Ya Zo, Gwamna Uba Sani Ya Juyo kan Sarakunan Gargajiya, Zai Masu Abin Alheri

Zaɓe Ya Zo, Gwamna Uba Sani Ya Juyo kan Sarakunan Gargajiya, Zai Masu Abin Alheri

  • Gwamna Uba Sani na Kaduna ya amince da ƙarin albashi da alawus-alawus ga sarakunan gargajiya domin inganta jin daɗinsu
  • Gwamnan ya kuma amince da biyan alawus ɗin tsaro kowane wata ga masarautu da masarautun ƙabilu 35, wanda ya fara aiki tun Satumba
  • Gwamnatin Kaduna ta ce matakin zai ƙarfafa tattara bayanan sirri daga al’umma, tare da taimaka wa jami’an tsaro wajen yaƙi da laifuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya amince da ƙarin albashi da alawus-alawus ga dukkan sarakunan gargajiya a faɗin jihar.

Matakin ya shafi sarakuna, hakimai da dagatai a dukkan gundumomin sanatan jihar guda uku, da nufin inganta jin daɗinsu da ƙarfafa aikinsu.

Uba Sani ya kara wa sarakunan gargajiya albashi
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna. Hoto: Uba Sani.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na Kaduna, Ahmed Maiyaki, ya fitar, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu ke kokarin tabbatar da dimukradiyya da tsaya da kafafunta

Yadda masarautu za su samu alawus

Sanarwar ta ce gwamnan ya kuma amince da biyan alawus ɗin tsaro kowane wata ga dukkan masarautu da masarautun ƙabilu 35 na Kaduna.

Ya ce za a fara biyan alawus ɗin daga ranar 1 ga Satumbar wannan shekara ta 2026 da muke ciki.

A cewar kwamishinan, ana sa ran matakin zai ƙarfafa tattara bayanan tsaro daga al’umma, tare da taimaka wa hukumomin tsaro wajen yaƙi da miyagun laifuka da sauran barazanar tsaro.

Shirin Uba Sani ga masarautu
Taswirar jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Twitter

Muhimmancin sarakunan gargajiya a Kaduna

Shi ma Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Sarautar Gargajiya na Kaduna, Sadiq Mamman-Lagos, ya bayyana cibiyoyin sarautun gargajiya a matsayin muhimman abokan hulɗa wajen gudanar da mulki a matakin ƙasa, samar da zaman lafiya, warware rikice-rikice da inganta tsaro.

Ya ce kusancin sarakunan gargajiya da al’ummominsu ya sanya su cikin wani muhimmin matsayi na gano barazanar da ke tasowa, samar da bayanan sirri cikin lokaci da kuma warware rikice-rikice kafin su ƙara muni.

Kara karanta wannan

Oluremi Tinubu ta ware jiha 1 a Najeriya, za ta rage wa mutane 5,000 talauci

Kwamishinan ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya da su yi amfani da ƙarin tallafin wajen ƙarfafa zaman lafiya, amincewa da juna da kuma haɗin kai tsakanin al’ummomi daban-daban na jihar.

A halin yanzu, gwamnatin Kaduna ta buƙaci mazauna jihar da su ci gaba da ba da haɗin kai ga cibiyoyin sarautun gargajiya da hukumomin tsaro, ta hanyar samar da sahihan bayanai cikin lokaci domin kare rayuka da dukiyoyi.

Gwamnatin ta ce amincewar ƙarin albashi da alawus-alawus na ƙara nuna jajircewarta wajen ƙarfafa cibiyoyin sarautun gargajiya da kuma inganta rawar da suke takawa wajen zaman lafiya, tsaro da ci gaban Kaduna, cewar Daily Post.

Uba Sani ya musanta karbar basuka

An ji cewa Gwamna Uba Sani ya ce bai ciwo ko sisi na sabon bashi ba tun lokacin da ya zama gwamnan Kaduna.

Gwamnatin Kaduna na kashe kusan Naira biliyan 6.7 a kowane wata wajen biyan bashin da gwamnatocin baya suka karbo.

Uba Sani ya ce an gano yara kusan 550,000 da ba sa zuwa makaranta, yayin da sama da 300,000 daga cikinsu aka mayar da su makarantu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.