Kungiyar APC Ta Cika Umarnin Shettima, Ta Dauki Nauyin Marayu 60
- Kungiyar APC Youth Parliament ta ce za ta ɗauki nauyin karatun yara 60 marasa galihu a Bauchi na tsawon shekara guda domin murnar Shettima
- Shugaban ƙungiyar, Kabiru Garba Kobi, ya ce adadin yaran ya yi daidai da shekaru 60 da Mataimakin Shugaban Ƙasar ya cika
- Kobi ya bayyana Shettima a matsayin jagora mai hangen nesa, tare da cewa matasan Arewa maso Gabas za su ci gaba da mara wa APC baya a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bauchi - APC Youth Parliament ta sanar da shirin ɗaukar nauyin karatun yara 60 marayu na tsawon shekara guda a matsayin wani ɓangare na bikin cikar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima shekaru 60.
Shugaban ƙungiyar, Kabiru Garba Kobi, ya bayyana hakan ne ranar Juma’a, 4 ga Satumba 2026, yayin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi.

Source: Twitter
Kobi ya sanarwa Legit Hausa cewa an ƙirƙiri shirin ne domin nuna godiya ga Allah kan rayuwa da hidimar Shettima ga al’umma.
Ya bayyana Mataimakin Shugaban Ƙasar a matsayin jagoran da ya himmatu wajen ci gaban Arewa maso Gabas da Najeriya baki ɗaya.
Dalilin zaɓar yara 60
Kobi ya ce zaɓar yara 60 da za a tallafa wa ba abu ne da aka yi kwatsam ba, domin adadin ya yi daidai da shekaru 60 da Shettima ya cika.
“Yayin da jagoranmu mai girma ke murnar cika shekaru 60, mun yanke shawarar ɗaukar nauyin karatun yara 60 a Bauchi, domin adadin ya yi daidai da shekarun da Allah ya albarkace shi da su,” in ji Kobi.
Ya ce ƙungiyar tana alfahari da nasarorin Shettima da irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban ƙasa.
A cewarsa, Shettima ya kasance mai haɗa kan al’umma a Arewa maso Gabas kuma ɗaya daga cikin masu taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban Najeriya.

Kara karanta wannan
Kwankwasiyya ta fallasa shirin da aka yi wajen tarbar dumbin mutane zuwa APC a Kano
An yaba da gudunmawar Shettima
Shugaban APC Youth Parliament ya ce cikar Shettima shekaru 60 dama ce ta waiwayen tafiyarsa a aikin gwamnati da siyasa.
Ya bayyana shi a matsayin mutum mai zurfin ilimi, ƙarfin hali, hangen nesa, tawali’u da jajircewa wajen yi wa jama’a hidima.
Kobi ya kuma yaba wa Shettima kan haɗin gwiwarsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen aiwatar da manufofin Renewed Hope Agenda na gwamnatin tarayya.
APC Youth Parliament ta yi magana kan 2027
Kobi ya ce yana da yakinin Shettima zai ci gaba da amfani da ƙwarewarsa wajen taimaka wa Shugaba Tinubu da kuma kare muradun ’yan Najeriya.
Ya yi masa addu’ar samun lafiya, hikima, ƙarfi da shiriya daga Allah yayin da yake ci gaba da yi wa ƙasar hidima.
Dangane da zaɓen 2027, shugaban ƙungiyar ya ce Shugaba Tinubu ba zai yi nadamar zaɓar Shettima a matsayin mataimakinsa ba.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa Shettima zai taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar APC a zaɓen.
Kobi ya ce matasa da sauran masu ruwa da tsaki a Arewa maso Gabas suna kallon Shettima a matsayin amintaccen jagora.
Ya yi alkawarin cewa ƙungiyarsa za ta ci gaba da wayar da kan jama’a da tattara goyon baya ga APC a yankin.

Source: Facebook
Tinubu ya taya Shettima murna
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya mataimakinsa, Kashim Shettima, murnar cika shekaru 60 da haihuwa.
Mai girma Bola Tinubu ya bayyana mataimakin na sa a matsayin ɗan kishin ƙasa kuma abokin hulɗa amintacce.
Asali: Legit.ng

