Da hannun Gwamnatin Tinubu a Yunkurin Juyin Mulki a Nijar? An Gano Gaskiya

Da hannun Gwamnatin Tinubu a Yunkurin Juyin Mulki a Nijar? An Gano Gaskiya

  • Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin cewa Najeriya ko ECOWAS sun goyi bayan yunƙurin juyin mulkin da ya gaza a Jamhuriyar Nijar
  • Ma’aikatar Harkokin Waje ta ce Najeriya ba za ta taɓa goyon bayan haramtacciyar hanya ko sauya gwamnati ta hanyar da ta saɓa wa kundin tsarin mulki ba
  • Najeriya ta sake bayyana buƙatarta ta ganin an samu zaman lafiya, tsaro, dimokuraɗiyya da ci gaba a Nijar da sauran ƙasashen yankin Sahel

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin cewa Najeriya ta goyi bayan yunƙurin juyin mulkin da ya gaza a Jamhuriyar Nijar.

Ministan Harkokin Wajen Ƙasa, Ambasada Sola Enikanolaye, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 3 ga watan Satumban 2026.

Abin da Najeriya ta ce kan yunkurin juyin mulki a Nijar
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ministan ya ce Ma’aikatar Harkokin Waje ta lura da wasu bayanai na ƙarya da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta game da lamarin, kamar yadda aka sanya sanarwar a shafin X.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Janar Musa ya ce Najeriya ta yi galaba kan 'yan ta'adda, ya gabatar da dalili

Ya bayyana zargin a matsayin wani yunƙuri na yaɗa bayanan da za su rikitar da jama’a tare da ɓata sunan Najeriya.

Najeriya ta ƙaryata zargin da kakkausar murya

A cewar Enikanolaye, wasu bayanan da ake yaɗawa na nuna cewa ECOWAS ta goyi bayan yunƙurin juyin mulkin, wanda hakan ke nufin cewa Najeriya ma ta amince da shi.

"Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da waɗannan zarge-zarge baki ɗaya, saboda ba su da tushe, ba su dace ba, kuma yunƙuri ne da gangan na yaudarar jama’a da ɓata sunan Najeriya.” In ji sanarwar.

Ministan ya bayyana Najeriya a matsayin ƙasa mai son zaman lafiya, mai kare tsarin mulkin dimokuraɗiyya da kuma ɗaya daga cikin ƙasashen da ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali.

Ya ce hakan ya shafi ba kawai Yammacin Afirka ba, har ma da yankin Sahel da nahiyar Afirka baki ɗaya.

Najeriya ba za ta goyi bayan juyin mulki ba

Kara karanta wannan

INEC ta fadi abin da ake tsoro ya hana zaben 2027 zama sahihi

Enikanolaye ya jaddada cewa Najeriya ba za ta goyi bayan haramtacciyar hanya ko sauya gwamnati ta hanyar da ta saɓa wa kundin tsarin mulki a kowace ƙasa ba.

Ya ce ba za a yi la’akari da wanda ke da hannu ko ƙasar da abin ya shafa ba wajen yanke wannan matsaya.

Ya kuma yi nuni da sanarwar Ma’aikatar Harkokin Waje mai lamba MFA/PR/2026/220 ta ranar 30 ga Agusta 2026, wadda ta bayyana matsayar Najeriya kan halin da ake ciki a Nijar.

A cikin sanarwar, Najeriya ta bayyana matuƙar damuwa kan halin da ake ciki, tare da yin kira da a samu hanyar zaman lafiya, haɗa kai da kuma komawa ga kwanciyar hankali da tsarin mulkin dimokuraɗiyya.

Najeriya ta damu da sauyin gwamnati ba bisa ƙa’ida ba

Ministan ya ce Najeriya na kallon duk wani yunƙurin sauya gwamnati ba bisa ƙa’ida ba a matsayin abin damuwa.

Ya ce saboda kusancin tarihi, zumunci da al’adu tsakanin Najeriya da Nijar, abin da Najeriya ke muradi shi ne zaman lafiya, tsaro, dimokuraɗiyya da ci gaba ga ƙasar.

Ya ce amfani da ƙarfi wajen warware rikicin siyasa ya saɓa wa wannan buri da kuma doguwar manufar harkokin wajen Najeriya.

Kara karanta wannan

Kamfanin Opay ya nemi agajin DSS, ƴan sanda kan jita jitar zai gudu a Najeriya

Najeriya ta kare matsayinta a ECOWAS

Enikanolaye ya ce Najeriya na alfahari da kasancewarta ƙasa mai cikakken himma a cikin Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS).

Sai dai ya ce ba daidai ba ne kuma ƙarya ce a ce Najeriya ta amince da juyin mulkin soja ko kuma tana goyon bayansa.

“Muna roƙon ’yan Najeriya, da ke cikin ƙasa da waɗanda ke ƙasashen waje, da su yi watsi da bidiyoyi da bayanan da wasu mutane ke yaɗawa a intanet domin haddasa rarrabuwar kawuna,” in ji sanarwar.
Najeriya ta ce ba hannunta a yunkurin juyin mulki a Nijar
Mai girma Bola Tinubu, shugaban kasar Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Fintiri ya kare Tinubu

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya kare Shugaba Bola Tinubu kan matsalar rashin tsaro a Arewa.

Gwamnan ya ƙalubalanci shugabannin Arewacin ƙasar da su yarda cewa laifinsu ne tare da neman mafita mai dorewa kan matsalolin tsaron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng