Gwamna Ya ba da Umarnin Rufe Makarantu sakamakon Barkewar Cuta, An Fara Rasa Rayuka

Gwamna Ya ba da Umarnin Rufe Makarantu sakamakon Barkewar Cuta, An Fara Rasa Rayuka

  • Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya ba da umarnin rufe makarantun firamare da sakandire na gwamnati da na kudi saboda cutar diphtheria
  • Kwamishinar Yada Labarai da Sadarwa ta jihar Filato, Joyce Lohya Ramnap ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar yau Asabar
  • Ta bukaci masu makarantun kudi, shugabannin makarantu, malamai, iyaye da masu kula da yara da su tabbatar dalibai sun zauna a gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Plateau, Nigeria - Gwamnatin jihar Filato ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati da na kudi na wani dan lokaci sakamakon barkewar cutar mashako watau diphtheria.

Gwamnatin ta ce an dauki matakin ne domin kare dalibai daga kamuwa da cutar, wacce ke kara yaduwa a wasu sassan jihar Filato.

Gwamnan Filato.
Gwamnan jihar Filato, Barista Caleb Mutfwang a fadar gwamnati da ke Jos Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Twitter

Dalilin rufe makarantu a jihar Filato

Kara karanta wannan

Amurka ta kaddamar da sababbin hare hare kan jirgin Iran

Daily Trust ta ruwaito cewa rufe makarantun ya zo ne kwanaki kadan bayan jami’an lafiya sun tabbatar da mutuwar wasu mutne a karamar hukumar Jos ta Arewa sakamakon abin da ake zargin matsalolin cutar diphtheria ne.

Kwamishinan lafiya na jihar Plateau, Dakta Nicholas Baamlong, ya bayyana cewa mutane kusan 23 sun mutu sakamakon cutar.

Ya ce gwamnatin jihar ta kara zage damtse wajen dakile yaduwar cutar mai saurin yaduwa.

Baamlong ya ce an kwantar da marasa lafiya tara a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) da Asibitin Kwararru na Plateau.

Matakin rufe makarantun na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishiniyar Yada Labarai da Sadarwa ta jihar Filato, Joyce Lohya Ramnap, ta sanya wa hannu ranar Asabar.

Ta ce umarnin zai fara aiki daga ranar Litinin, 7 ga watan Satumban 2026, kuma zai ci gaba da aiki har sai an sake bayar da wani umarni.

Kwamishiniyar ta ce Gwamna Caleb Manaseh Mutfwang ne ya bayar da umarnin bayan samun rahotannin wadanda ake zargin sun kamu da cutar diphtheria a kananan hukumomin Jos ta Arewa, Wase, Jos ta Kudu da Bassa.

Gwamnatin ta ce makarantun da suka riga suka koma karatu su ma za su rufe daga ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Pantami ya ci zaben gwamnan Gombe na gwaji da aka yi a intanet

Ta bukaci masu makarantun kudi, shugabannin makarantu, malamai, iyaye da masu kula da yara da su tabbatar dalibai sun zauna a gida a tsawon lokacin domin kare lafiyarsu.

Sanarwar ta ce:

“Gwamnati ta yaba da fahimta da cikakken hadin kan dukkan masu ruwa da tsaki yayin da take ci gaba da daukar matakan da suka dace domin kare muradun al’ummar jihar Plateau.”

Lamarin ya haifar da damuwa a tsakanin iyaye da ma’aikatan lafiya, saboda fargabar cewa cutar mai saurin yaduwa na iya bazuwa cikin sauki a dakunan karatu masu cunkoso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262