Kano: Bayan Mutuwar Yara 50, Abba Ya Nemi Taimako daga Gwamnatin Tarayya
- Kano ta nemi Gwamnatin Tarayya ta tallafa mata bayan an samu karin bullar cutar mashako wato 'diphteria' da ya jawo asarar rayuka da dama
- Wadanda suka rasu sun hada da yara 50 yayin da a yanzu haka wasu ke kwance suna jinya musamman a karamar hukumar Rano da ke jihar
- Hukumar kula da cututtuka ta jihar ta ce sama da yara 31,000 ne aka tabbatar suna dauke da cutar daga cikin fiye da 38,000 da aka samu tun 2022
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnatin Jihar Kano ta roki Gwamnatin Tarayya da ta kara samar mata da allurar rigakafin cutar mashako domin ba ta damar gudanar da gangamin yi wa al’umma rigakafi a fadin jihar.
Daraktan Janar na Cibiyar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC), Farfesa Muhammad Abbas, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a daren Talata 25 ga watan Agusta, 2026.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa an gudanar da taron ne bayan da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta nuna damuwa kan bullar cutar diphtheria a Rano da wasu kananan hukumomi, lamarin da aka ce ya yi sanadin mutuwar sama da yara 50.
An samu bular mashako a jihar Kano
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar, musamman iyaye, da su daina jinkirta kai marasa lafiya cibiyoyin kiwon lafiya idan suka fara nuna alamun diphtheria ko wasu cututtuka.
Ya ce:
“Jihar Kano har ta rubuta wa Gwamnatin Tarayya domin samun karin allurai, ta yadda za mu yi wa mutanenmu rigakafi."
“Muna rokon iyaye da su rika kawo marasa lafiya da wuri. Kai mutum cibiyar kiwon lafiya da zarar matsala ta fara ita ce ke taimakawa wajen ceton rai".
Gwamnatin Kano ta damu kan cutar mashako
Daraktan Janar din ya ce abin damuwa ne yadda wasu mutane ke kasa kai rahoton wadanda suka kamu da cutar zuwa asibitoci, duk da cewa jihar na da jami’an sa ido kan cututtuka a dukkan kananan hukumominta 44.

Source: Original
Farfesa Abbas ya ce cibiyar ta dade tana daukar matakan yaki da mashako tun bayan da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta hau mulkin jihar Kano.
Ya bayyana cewa daga shekarar 2022 zuwa yanzu, an samu rahotannin fiye da mutane 38,000 da ake zargin sun kamu da cutar, inda aka tabbatar da cutar a sama da 31,000 daga cikinsu.
Yara 50 sun rasu a Kano
A baya, mun kawo labarin cewa Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bukaci Gwamna Abba Yusuf ya gaggauta daukar matakan dakile cutar diphtheria da ta hallaka yara da dama.
'Dan majalisa, Ibrahim Muhammad, ya ce cutar ta yadu zuwa wasu al’ummomi a karamar hukumar Kiru, inda wani shugaban matasan APC ya rasa ‘ya’ya biyu a rana guda.
Majalisar ta umarci kwamitinta mai kula da lafiya da ya tuntubi Ma’aikatar Lafiya kan aiwatar da dokar kare lafiya da kuma samar da agajin gaggawa domin kare rayuka.
Asali: Legit.ng

