An Samu Sabani tsakanin Gwamnati da Dan Majalisa kan Yawan Mutanen da Cuta ta Kashe a Kano
- Gwamnatin Kano ta musanta rahoton cewa yara 50 sun mutu sakamakon barkewar cutar mashako watau diphtheria a Rano
- KNCDC ta ce mutum biyu ne suka mutu a Rano a 2026, yayin da jimillar mutanen da suka mutu a yankin daga Yuli 2023 zuwa Agusta 2026 ta kai 29
- Cibiyar ta ce kashi 94% na masu kamuwa da cutar ba su samu allurar rigakafi ba, yayin da kashi 91% suka je neman magani ne a makare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnatin Jihar Kano ta musanta rahotannin cewa yara 50 sun mutu sakamakon barkewar cutar mashako 'diphtheria' a Karamar Hukumar Rano ta jihar.
Rahoton, wanda aka danganta shi da dan majalisar da ke wakiltar mazabar Rano, Ibrahim Muhammad, ya yi zargin cewa cutar ta yi sanadin mutuwar yara 50 a yankin.

Source: Facebook
Sai dai a rahoton Channels tv, shugaban hukumar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC), Muhammad Abbas, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ya bayyana ikirarin a matsayin wanda ba a tantance ba.
Mutum nawa cutar ta kashe a Kano?
Abbas ya amince cewa barkewar cutar gaskiya ce kuma ta yi sanadin mutuwar wasu mutane, amma ya ce adadin wadanda ake yadawa bai dace da bayanan da suka tattara ba.
Ya ce bayanan da ake da su sun nuna cewa mutum biyu ne suka mutu sakamakon cutar diphtheria a Rano a shekarar 2026, yayin da jimillar mutanen da suka mutu sakamakon cutar tsakanin Yuli 2023 da Agusta 2026 ta kai 29.
A cewarsa, KNCDC ta samu mutane 32 da suka kamu da cutar a Rano, inda aka yi wa marasa lafiya 25 magani a Cibiyar Kula da Cutar Diphtheria da ke Babban Asibitin Rano, yayin da aka yi wa sauran bakwai magani a Kano.
Dalilin kamuwa da cutar mashako
Shugaban KNCDC ya kuma bayyana cewa kashi 94 cikin 100 na wadanda cutar ta kama ba su samu allurar rigakafi ba, yayin da kashi 91 cikin 100 suka je neman magani ne a makare.
Ya nuna damuwa kan jinkirin kai rahoton wadanda ake zargin sun kamu da cutar zuwa cibiyoyin lafiya, yana mai jaddada cewa gano cutar da wuri da fara magani cikin lokaci na da matukar muhimmanci wajen dakile yaduwarta.

Source: Original
Abbas ya kuma soki dan majalisar bisa zargin yin ikirarin da ba a tantance ba ba tare da tuntubar hukumomin da abin ya shafa ba, ciki har da Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano da KNCDC.
Ya tambayi yadda mutane 50 za su mutu ba tare da an kai rahotonsu ta hanyoyin da ake amfani da su wajen sa ido kan cututtuka a al’umma ba.
Kano ta nemi agajin gwamnatin tarayya
A wani rahoton, kun ji cewa Kano ta nemi Gwamnatin Tarayya ta tallafa mata bayan an samu karin bullar cutar mashako wato 'diphteria' da ya jawo asarar rayuka da dama.
Daraktan Janar na Cibiyar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC), Farfesa Muhammad Abbas, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar.
Asali: Legit.ng

