Tsohon Gwamna Ya Yi Kokarin Hure Wa Yan Najeriya Kunne kan Shirin Dawo da Tallafin Fetur
- Tsohon gwamnan Plateau, Fidelis Tapgun, ya ce maido da tallafin man fetur zai zama babban koma baya ga Najeriya
- Ya bukaci 'yan Najeriya su tambayi gwamnoni yadda suka kashe karin kudaden da suke samu tun bayan cire tallafin mai
- Tapgun ya soki Atiku Abubakar kan alkawarin maido da tallafin mai idan ya lashe zaben shugaban kasa na 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jos, Plateau - Tsohon gwamnan jihar Plateau, Ambasada Fidelis Tapgun, ya ce duk wani yunkurin dawo da tallafin man fetur zai jawo babban koma baya ga Najeriya.
Tapgun ya bukaci 'yan Najeriya su daina kallon gwamnatin tarayya kawai, su kuma tambayi gwamnonin jihohi yadda suke amfani da dimbin kudaden da suka samu sakamakon cire tallafin man fetur.

Source: Facebook
Leadership ta ruwaito cewa tsohon gwamnan ya soki alkawarin dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar, na cewa zai dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaben 2027.

Kara karanta wannan
Tsohon gwamna ya fito ya fadi gaskiyar dalilin da ya sa yake neman mulkin Najeriya a 2027
Tapgun ya yabawa cire tallafin mai
Da yake zantawa da manema labarai a gidansa da ke Jos, Tapgun ya ce cire tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi yana daga cikin matakan da aka dauka domin farfado da tattalin arzikin Najeriya.
Ya ce gwamnatocin baya sun gaji tattalin arzikin kasar cikin mawuyacin hali, kuma cire tallafin na daga cikin matakan gyara.
Tsohon gwamnan ya kuma tambayi inda Atiku zai samo kudaden da zai rika kashewa wajen biyan tallafin idan aka dawo da tsarin.
Abin da dawo da tallafi zai jawo a Najeriya
A cewarsa, komawa tsarin tallafin zai kara jefa 'yan Najeriya cikin wahala tare da rusa ci gaban da gwamnatin yanzu ta samu.
Ya ce:
“Gwamnatocin baya ba su da karfin halin cire tallafin, hatta gwamnatocin soja ba su iya yi ba. Amma gwamnatin Shugaba Tinubu ta dauki matakin da ya dace, kuma kasa ta fara gyaruwa.

Kara karanta wannan
"Na san komai," Tsohon gwamna ya 'tsoratar' da yan Najeriya kan shirin dawo da tallafin fetur
“Babu yadda dan takarar shugaban kasa na ADC zai iya mayar da tsarin, domin yin hakan tamkar mayar da Najeriya baya ne.
“Cire tallafin ya kawo makudan kudade ga jihohi da kananan hukumomi domin ayyukan raya kasa. Ina ganin lokaci ya yi da 'yan Najeriya za su tambayi shugabannin wadannan matakai yadda suke amfani da albarkatun da suke hannunsu.”

Source: Facebook
Ya tambayi jihohi yadda suka kashe kudade
Tapgun, wanda ya taba zama jakadan Najeriya a Kenya kuma Ministan Masana'antu, ya nuna damuwa cewa abubuwan da ake gani a kasa ba su dace da yawan kudaden da jihohi da kananan hukumomi suka samu ba.
Ya ce babu wasu manyan ayyukan raya kasa da za su tabbatar da yadda aka kashe karin kudaden da jihohin suka rika samu.
Tapgun ya ce bai dace a dora wa gwamnatin tarayya alhakin yadda jihohi ke amfani da kudaden da aka ba su ba, kamar yadda Guardian ta ruwaito.
Atiku ya yaba wa kungiyar IPMAN
A wani rahoton, kun ji cewa Atiku Abubakar ya ce kungiyar dillalan mai ta IPMAN ta fahimci manufarsa ta tallafa wa matatun cikin gida domin rage farashin fetur.
Atiku ya ce kungiyar, ko da yake ta makara, ta fahimci babban ka'idar tattalin arzikin da ke bayan shirinsa na sake sanya makamashi ya kasance mai saukin farashi ga 'yan Najeriya.
Asali: Legit.ng