An Yi Rashi: Babban Sarki Mai Daraja a Arewa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

An Yi Rashi: Babban Sarki Mai Daraja a Arewa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Sarkin Gumel, Alhaji Dr. Ahmed Muhammad Sani II, CON, ya rasu ranar Alhamis a ƙasar Masar bayan ya shafe shekaru yana jagorantar masarautar
  • Rasuwar mai mataba sarkin ta jefa al’ummar Masarautar Gumel da mazauna Jihar Jigawa cikin jimami da alhini
  • Alhaji Dr. Ahmed Muhammad Sani ya rasu ne 'yan kwanaki kadan bayan rasuwar mai martaba sarkin Zurmi a jihar Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Jigawa - An yi babban rashi na sarkin Gumel da ke jihar Jigawa, Alhaji Dr Ahmed Muhammad Sani, wanda ya yi bankwana da duniya.

Marigayin ya koma ga Mahaliccinsa ne a birnin Cairo na kasar Egypt kamar yadda majiyoyi suka sanar.

Tashar TRT Afrika ta bayar da rahoton cewa majiyoyi daga fadar Gumel sun tabbatar mata da rasuwar sarkin a ranar Alhamis, 3 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan

Babban Sarki ya rasu a Arewa, Tinubu ya tuna ƙoƙarin basaraken kan tsaro

Babban rashi ga Masarautar Gumel

Rasuwar sarkin na nufin babban rashi ga iyalansa, ’yan uwansa, abokan hulɗarsa da kuma al’ummar Masarautar Gumel baki ɗaya.

An gudanar da addu’o’i tare da roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya jiƙansa da rahama, Ya kuma ba shi Aljannatul Firdausi.

A sakon ta'aziyyarsa, Babandi Ibrahim Gumel, ya rubuta cewa:

"Innalillahi wainnailaihirrajiun"
"Cikin Alhini nake mika taaziyata ga iyalai, yan uwa, hakimai, dagatai, alummar masarautar Gumel, da alummar jihar Jigawa bisa rasuwar Maimartaba Sarkin Gumel, Alhaji Ahmed Mohammed Sani II, wanda ya rasu a yau a asibiti a garin Cairo dake kasar Misra. Allah ya jikansa da rahama, ya sanya mutuwa ta zamo hutu a gareshi. Allah ya bamu hakurin rashinsa, Amin."

Gudummawarsa masarautar gargajiya

Rasuwar Sarkin Gumel ta zama babban rashi ga masarautar, musamman saboda muhimmiyar rawar da cibiyoyin gargajiya ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan al’umma.

Masarautun gargajiya na kuma taka rawa wajen kare al’adu da ɗabi’un jama’a, da kuma tallafa wa ayyukan ci gaban al’umma.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya kadu kan rasuwar babban sarki mai daraja a Zamfara

Masarautar Gumel na daga cikin tsofaffin cibiyoyin gargajiya a Arewacin Najeriya, tana da tarihi daɗaɗɗe da kuma muhimmiyar rawa a harkokin zamantakewa da al’adun mutanenta.

Marigayin ya jagoranci masarautar

A matsayinsa na Sarkin Gumel, marigayi Alhaji Dr. Ahmed Muhammad Sani II, CON, ya kasance mai kula da gadon masarautar tare da jagorantar al’ummar yankin.

Rasuwarsa na daga cikin manyan abubuwan da za su shafi ’yan gidan sarauta, masu riƙe da sarautun gargajiya, shugabannin al’umma da mazauna sassan Masarautar Gumel.

Za a ci gaba da jin tasirin rashinsa yayin da al’ummar masarautar ke jimamin rasuwar daya daga cikin manyan shugabanninta na gargajiya.

Legit Hausa ta tuntubi wani dan garin Gumel, Ibrahim Babangida Gumel, wanda ya tabbatar da rasuwar mai martaba sarkin.

"Eh da gaske wallahi. Allah ya gafarta masa." In ji shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng