Gwamna Ya Kadu da Aka Tabbatar da Rasuwar Mai Martaba Sarki bayan Ya Tafi Kasar Masar

Gwamna Ya Kadu da Aka Tabbatar da Rasuwar Mai Martaba Sarki bayan Ya Tafi Kasar Masar

  • Gwamna Umar Namadi ya bayyana rasuwar Sarkin Gumel, Alhaji Dr Ahmed Muhammad Sani II, a matsayin babban rashi ga jihar Jigawa
  • Rahotanni sun ce Sarkin ya rasu yana da shekara 82 a birnin Alkahira na kasar Masar bayan gajeriyar rashin lafiya
  • Marigayin ya shafe sama da shekaru 45 yana sarautar Gumel, inda ya ba da gudunmawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Dutse, Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya bayyana rasuwar Sarkin Gumel, Alhaji Dr Ahmed Muhammad Sani II, a matsayin babban rashi ga jihar Jigawa da Najeriya baki daya.

Gwamna Namadi ya bayyana hakan ne ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Bala Ibrahim, yayin da yake ganawa da manema labarai kan rasuwar Sarkin a ofishinsa da ke Dutse ranar Alhamis da yamma.

Kara karanta wannan

An yi rashi: Babban sarki mai daraja a Arewa ya riga mu gidan gaskiya

Gwamnan Jigawa.
Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi a fdar gwamnatinsa da ke Dutse Hoto: Garma Mohammed
Source: Twitter

Punch ta ruwaito cewa Sarkin Gumel na 16 ya rasu ne a birnin Alkahira na kasar Masar ranar Alhamis, 3 ga watan Satumba, 2026 bayan gajeriyar rashin lafiya.

Gwamnatin Jigawa ta shiga alhini

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Sakataren Gwamnatin Jihar ya ce gwamnati ta samu labarin rasuwar cikin kaduwa.

Ya ce:

“Cikin matukar alhini da mika wuya ga nufin Allah Madaukakin Sarki, gwamnatin jihar Jigawa ke sanar da rasuwar Mai Martaba Sarkin Gumel, Alhaji Dr Ahmed Muhammad Sani II, CON, wanda ya rasu da safiyar Alhamis a kasar Masar.”

Da yake magana a madadin Gwamna Namadi, Bala Ibrahim ya bayyana marigayin a matsayin uba kuma ginshikin hadin kai.

Ya ce marigayi Sarkin ya kasance babban shugaban gargajiya mai kima, wanda ya sadaukar da shekaru 45 na rayuwarsa wajen yi wa al'ummarsa hidima.

Gwamna Namadi ya yabi Sarkin Gumel

Sakataren gwamnatin jihar ya ce marigayi Sarkin Gumel ya taka rawar gani wajen inganta zaman lafiya, ilimi da ci gaba a Masarautar Gumel da jihar Jigawa baki daya.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya kadu kan rasuwar babban sarki mai daraja a Zamfara

Ya ce gwamnatin Namadi tana tare da Masarautar Gumel da daukacin al'ummar jihar Jigawa a wannan lokaci na jimami.

“Gwamnati tana mika sakon ta'aziyya daga zuciya ga iyalansa, Majalisar Masarautar Gumel da daukacin al'ummar jihar Jigawa. Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa kura-kuransa, ya kuma sanya shi a Aljannatul Firdaus," in ji shi.

Tarihin marigayi Sarkin Gumel

An haifi marigayi Alhaji Dr Ahmed Muhammad Sani II a ranar 12 ga watan Disamban 1942. Ya kasance daya daga cikin sarakunan gargajiya da suka fi dadewa kan karagar mulki a Arewacin Najeriya.

Ya hau karagar Sarkin Gumel ne a ranar 16 ga watan Disamban 1980 bayan rasuwar mahaifinsa, Alhaji Muhammad Sani, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Sarkin Gumel.
Mai martaba Sarkin Gumel da ke jihar Jigawa, Marigayi Dr Ahmed Muhammad Sani II Hoto: Masarautar Gumel
Source: Facebook

A watan Mayun 1981 ne ya karbi sandar mulki daga hannun tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kano, Alhaji Abubakar Rimi.

A cikin sama da shekaru 45 da ya shafe kan karagar mulki, marigayi Sarkin ya shahara wajen samar da zaman lafiya da karfafa ilimi tare da kare al'adun gargajiya.

Mai martaba Sarkin Zurmi ya rasu

Kara karanta wannan

Najeriya ta tafka rashi, Allah ya yi wa mai martaba Sarkin Zurmi rasuwa

Kun ji cewa mai martaba Sarkin Zurmi da ke jihar Zamfara a shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya, Bello Suleiman, ya riga mu gidan gaskiya.

A wata sanarwa da fadar masarautar ta fitar ta bayyana cewa mai martaba ya rasu ne da yammacin Litinin, 31 ga watan Agustan 2027 a asibiti gwamnatin tarayya (FMC), da ke Gusau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262