Atiku Ya Yi Alkawarin ba Dan Najeriya da Zai Biya Kudin Haya idan Ya Zama Shugaban Kasa?
- Tawagar yaɗa labaran Atiku Abubakar ta yi martani kan labarin da ke cewa ya yi alkawarin soke biyan kudin haya
- Wani rubutu a X ya wallafa hoton shafin farko na wata jarida, yana zargin Atiku da yin alkawarin ɗaure masu gidaje shekaru 10
- Abdul Rasheeth, mai taimaka wa Atiku kan harkokin yaɗa labarai, ya bukaci jama’a su yi watsi da labarin tare da dogaro da hanyoyin sadarwar Atiku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Abuja, Najeriya - Tawagar yaɗa labaran ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ta musanta wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta.
Labarin na zargin cewa tsohon mataimakin shugaban Najeriya ya yi alkawarin cewa babu wani ɗan Najeriya da zai sake biyan kuɗin haya idan ya zama shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Source: Twitter
Abdul Rasheeth, mai taimaka wa Atiku na musamman kan harkokin yaɗa labarai, ne ya yi watsi da zargin a ranar Laraba, 2 ga Satumba, 2026 a shafinsa na X.
Yadda labarin ƙaryar ya yaɗu
Rasheeth ya mayar da martani ne ga wani rubutu da wani mai amfani da X mai suna @HighChiefOkoro ya wallafa.
Rubutun ya ƙunshi hoton abin da ya yi kama da shafin farko na jaridar Daily Tribune mai kwanan wata Talata, 1 ga Satumba, 2026.
A jikin shafin an rubuta babban kanun labari mai cewa: “Atiku: Babu ɗan Najeriya da zai biya kuɗin haya.”
Wani rubutu da aka haɗa da hoton ya kuma yi zargin cewa Atiku ya yi alkawarin ɗaure masu gidaje da suka karɓi kudin haya na tsawon shekaru 10 idan ya zama shugaban ƙasa.
Atiku ya ce labarin ƙarya ne
Da yake mayar da martani ta shafinsa na X, @Rasheethe, Rasheeth ya bayyana labarin a matsayin wanda aka ƙirƙira gaba ɗaya.
“An jawo hankalinmu kan wani ƙagaggen bayani da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda aka danganta shi da Mai Girma Atiku Abubakar, yana cewa ‘babu ɗan Najeriya da zai biya kudin haya idan na zama shugaban ƙasa’.”
Rasheeth ya ƙara da cewa wannan ikirari ƙarya ne kuma bai wakilci ra’ayi ko matsayin manufofin Atiku Abubakar ba.
An buƙaci jama’a su yi watsi da bayanin
Tawagar yada labaran Atiku ta shawarci jama’a da su yi watsi da bayanin da ake yaɗawa, tare da dogaro da tashoshin sadarwar Atiku na hukuma wajen samun sahihan bayanai.
A cewar tawagar, duk wata sanarwa ko manufa ta siyasa da ta shafi Atiku za ta fito ne daga hanyoyin sadarwarsa na hukuma.
Atiku ya yi magana kan tallafin man fetur
Legit Hausa ta ruwaito cewa Atiku Abubakar ya bayyana cewa zai dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce matakin zai kasance wani bangare na manufofin da zai aiwatar idan aka ba shi damar jagorantar Najeriya.

Source: Facebook
FBI ta taba bincikar gidan Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar FBI ta taba bincikar gidan Atiku Abubakar na Amurka a lokacin da yake mataimakin shugaban kasa.
Jami'an na FBI sun kai samame a gidan Atiku kan wani bincike da hukumomin Amurka ke yi kan ɗan majalisar wakilan Amurka, William Jefferson.
Asali: Legit.ng

