Murna: Hotunan Atiku da Daya Daga Cikin 'Yan Matan Chibok Lokacin da Ta Kammala Digiri
- Shekaru bakwai bayan kubuta daga hannun 'yan Boko Haram, 'yan matan Chibok sun tsunduma karatu
- An ruwaito a bayan yadda wasu daga cikin ukun da suka kubuta a 2014 suka kammala karatu a Amurka
- An sake samun wata daga cikinsu ta kammala wata jami'a a Najeriya, an kuma taya ta murna sosai
Mary Katambi, daya daga cikin ‘yan matan Chibok da ta kubuta daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram a shekarar 2014, ta kammala karatun ta a jami’ar Amurka ta Najeriya (AUN) da digiri a ilimin lissafi.
Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma wanda ya kirkiri jami'ar AUN, ya bayyana a dandalinshi na sada zumunta inda ya watsa hotuna daga bikin wanda aka gabatar a ranar Asabar a Yola, babban birnin jihar Adamawa.
Katambi, wanda ta sanya rigar kammala karatun, ta samu taya murna daga Atiku Abubakar da Akinwumi Adesina, shugaban Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) wanda ya kasance babban mai jawabi.
KARANTA WANNAN: Sabon hari: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu yara bayan raba su da mahaifiyarsu a Kaduna
Legit.ng Hausa ta gano Atiku Abubakar rubutun da ya yi Facebook, inda yake cewa:
“Mary Katambi, ina alfahari da cewa shekaru bakwai bayan kubutarki daga hannun Boko Haram, kin yi nasara bisa kammala karatun digiri a fannin lissafi daga Jami’ar Amurka ta Najeriya. Ina miki fatan nasara a shekarunki na gaba."
Yadda sauran 'yan matan da suka kubuta daga hannun Boko Haram suka kasance
Mary na daya daga cikin ‘yan mata 276 da kungiyar Boko Haram ta sace a makarantar sakandaren gwamnati ta (GGSS), Chibok a jihar Borno.
Jaridar TheCable a baya ta ruwaito cewa Joy Bishara da Lydia Pogu, tsoffin daliban GGSS Chibok wadanda suma suka tsere daga hannun kungiyar Boko Haram a shekarar 2014, sun kammala karatu a jami’ar kudu maso gabashin Amurka.
Ga hotuna daga bikin kammala karatun Katambi.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin El-Rufa'i Ta Garkame Bankin Fidelity a Kaduna Saboda Kudin Haraji
Jerin Ministocin Buhari da Basu da Kwalin NYSC da Kuma Dalilan da Suka Jawo
A wani labarin, Ana ta cece-kuce game da takardar NYSC na tsohuwar ministar kudi Kemi Adeosun, lamarin da ya kai ga ta mika takardar ajiye aiki a matsayinta na minista a shekarar 2018.
Mutane da dama sun kagu cewa, ta yiwu akwai wasu daga cikin jigogin gwamnatin Buhari da basu mallaki takardar NYSC ba, wannan yasa wannan rahoton na Legit.ng Hausa ya tattaro sunayen wasu ministocin Buhari da basu takardar da kuma dalilan da suka jawo haka.
Asali: Legit.ng