Ganin Haya Ya Yi Tsada Gwamnati Ta Yunkuro domin Rage Kudin Gidaje a Kaduna
- Majalisar Kaduna za ta gudanar da taron sauraron ra'ayoyin jama'a da masu ruwa da tsaki kan kudirin gidan haya
- Ana so a kawo dokar da za ta lura da hakkin masu gida da kuma 'yan haya domin samar da daidaito a jihar Kaduna
- Yunkurin yana goyon bayan manufofin Gwamna Uba Sani na rage radadin tattalin arziki inganta jin dadin al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Majalisar dokokin jihar Kaduna tana kokarin kawo dokar da za ta duba sha’anin gidajen haya domin a samu saukin rayuwa.
A halin yanzu gidajen haya sun yi tsada musamman cikin birane a Kaduna, wanda hakan ya jefa magidanta a karin matsin lamba.

Source: UGC
Shugaban majalisa ya kawo kudirin gidan haya
Suraj Bamalli ya sanar a X cewa Shugaban majalisar dokoki a Kaduna, Yusuf Dahiru Liman ya gabatar da kudiri kan gidajen haya.
Kudirin Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman ya yi nufin kare masu haya daga takura na babu gaira babu dalili daga masu bada hayar gidaje.
Haka zalika kudirin zai tabbatar ba a tauye hakkin masu gidaje da masu bada haya ba.
Kudirin gidajen haya yana gaban kwamitin majalisa
Yanzu haka wannan kudiri yana gaban kwamitin majalisar dokoki inda ake sa ran za a yi la’akari da shi har ya zama doka a gwamnati.
Za a bada damar a saurari mutane da duk masu ruwa da tsaki kafin a gama aiki kan kudirin.
Wadanda aka gayyata sun kunshi masu gidaje, mutanen da ke haya, attajirai da suka mallaki kadarori da kwararru a harkar gine-gine.
Haka zalika Majalisar Kaduna za ta saurari kungiyoyi masu zaman kansu da duk wadanda ke da ta-cewa a wajen sha’anin yin gini a jihar.
Yunkurin kawo saukin rayuwa a jihar Kaduna
Business Day ta ce kudirin ya zo ne a lokacin da ake kukan tsadar rayuwa musamman daga wurin marasa karfi, dalibai da masu tasowa.

Kara karanta wannan
Gwamnan APC ya tona gaskiya, an ji yadda gwamnoni suka amfana da cire tallafin fetur
Sanarwar Malam Bamalli ta ce wannan yana cikin kokarin gwamnatin Uba Sani na ganin an rage wa al’ummar Kaduna radadin da suke ciki.
Idan aka matsa da dokoki, wannan zai iya fusata attajirai masu gina gidaje domin su bada haya.
Haka zalika kuma gwamnati ta fahimci idan aka bar harkar babu sa-ido, za a zalunci bayin Allah masu rayuwa a cikin gidajen da ba nasu ba.
Majalisar Kaduna za ta yi ta tattaunawa da wadanda abin ya shafa har zuwa lokacin da za a gama tsara kudirin da zai zama doka.
Burin shugaban majalisar shi ne kawo doka da za ta yi aiki yadda ya kamata, kuma ta magance matsalolin gidaje da ake da shi a Kaduna.
Da crypto aka koma sata a gwamnati
Shugaban EFCC ya yi bayanin sabon salon satar kudi a Najeriya, an rahoto shi yana maganar kokarin da suke yi na yakar barayi.
Hukumar EFCC tana zargin ma'aikatan gwamnati da amfani da Crypto wajen karkatar da dukiyar jama'a a rasa gane ina suka shige.
Mista Ola Olukayode ya bada misali da kudin da aka sata a wata karamar hukuma aka tura wani kamfani, a karshe suka shige crypto.
Asali: Legit.ng
