Shugaban Majalisar da Kotu Ta Tsige Ya Haye, APC ta Doke PDP da Kuri’u 600 a Kaduna

Shugaban Majalisar da Kotu Ta Tsige Ya Haye, APC ta Doke PDP da Kuri’u 600 a Kaduna

  • Yusuf Dahiru Liman ya tsallake fargaba yayin da hukumar INEC ta sake ba shi nasara a zaben Makera
  • Bayan shugaban majalisar dokoki, APC ta samu karin kujerar majalisa a mazabar Chikun a Kaduna
  • PDP ta samu kujerun majalisar wakilai da na dokoki ta hannun Nura Abubakar da Hussaini M. Jalo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Yusuf Dahiru Liman ya koma kujerarsa a sakamakon zaben cike gurbi da aka yi a mazabar Makera a jihar Kaduna.

A yammacin Lahadi, Leadership ta kawo rahoto cewa Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman ya samu galaba a kan ‘dan takaran PDP.

Zaben Kaduna
APC da PDP sun yi nasara a zaben Kaduna Hoto:@BetterKaduna, Getty
Asali: Twitter

Yadda kotu ta tsige shugaban majalisa

Tsohon shugaban majalisar dokokin na jihar Kaduna ya rasa mukaminsa ne a sakamakon hukuncin kotun daukaka kara.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ya barke a Kaduna saboda kashe wanda ya hana sace kuri’un zabe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin kotun daukaka kara ya umarci a sake zabe a mazabu biyar da ke yankin.

Legit hausa ta fahimci mazabun sun hada da Katuka, Kakuri Hausa da Barnawa inda ake zargin an sabawa ka’idojin yin zabe.

APC ta doke PDP a Kaduna ta Kudu

Da aka yi zaben ranar Asabar, hukumar INEC ta tabbatar da cewa jam’iyyar APC tayi nasara, sai PDP mai adawa ta zo na biyu.

Rahoton ya ce Dahiru Liman ya samu kuri’u 18,068 sai Solomon Katuka na PDP ya tashi da kuri’u 17,404, an ba shi ratar kuri’u 682.

Rahotanni sun ce Usman Yakuti na jam’iyyar adawa ta LP ya zo na uku da kuri’u 3, 700.

A sakamakon haka, Farfesa Jamilu Ya’u ya ce za a ba Hon. Dahiru Yusuf Liman satifiket, ma’ana zai koma majalisar dokoki.

A Chikun, David Jesse da ya yi takara a APC ya ci kuri’u 18, 566, ya doke Maria Dogo da Solomon Adamu na jam’iyyun PDP da LP.

Kara karanta wannan

Korarren kakakin Majalisa da mataimakinsa sun dawo kan kujerunsu a jihar Arewa, bayanai sun fito

PDP ta yi waje da APC a Kudan

Punch ta ce Nura Abubakar ya samu kuri’u 24,178 a zaben majalisar dokoki na Kudan, ya doke Abbas Faisal mai kuri’a 22, 438.

Kafin zaben wani ‘dan APC a Zariya ya shaidawa Legit da wahala su lashe duka kujerun saboda ratar da ke tsakaninsu da PDP.

‘Dan siyasar ya ji tsoron shugaban majalisa zai iya rasa wurinsa ya kuma ce da wahala idan PDP ba ta karbe kujerar Kudan ba.

Igabi sai dai a bar wa PDP

An ji labari an yi zanga-zanga a jihar Kaduna bayan zaben ‘dan majalisar tarayyan na Igabi da aka karasa a karshen makon jiya.

Hussaini Jalo zai cigaba da rike kujerarsa a PDP a matsayin wakilin Igabi a majalisar wakilai ta kasa bayan doke Zayyad Ibrahim.

Asali: Legit.ng

Online view pixel