EFCC Ta Gano Bakuwar Dabarar da Ma’aikata Suke Bi Su Sace Kudin Gwamnati
- Hukumar EFCC ta gano ma'aikatan gwamnati na tura kudin sata zuwa asusun intanet irinsu Crypto
- Ma'aikatan gwamnatin suna amfani da matasa wajen taimaka masu su karkatar da dukiyar a yanar gizo
- Ola Olukoyede ya ce hukumarsa ta fara samun nasarar binciko asusun na Crypto domin dakile sace-sace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Shugaban hukumar EFCC na kasa, Ola Olukoyede, ya yi bayanin kokarin da suke yi na hana satar kudi tun wuri.
EFCC ta maida hankali wajen yin rigakafi, ta yadda za a hana aikata laifi maimakon ta zo tana bincike bayan an yi barna.

Source: UGC
Shugaban EFCC ya kira taron manema labarai
Mista Ola Olukoyede ya bayyana haka yayin zanta wa da manema labarai kamar yada hukumar dillacin labarai ta labarto.
Shugaban na EFCC ya ce sun kafa sashen FRAC mai alhakin bin duk kudin da ake zargin na sata ne, sai a dauki mataki.

Kara karanta wannan
Lauya ya tsage gaskiya, an ji dalilin da ya sa Amurka ba ta kama Shugaba Tinubu ba
Aikin FRAC shi ne ta gano wasu kudi masu alamun tambaya da ake yawo da su, daga nan sai ta rufefe asusun da aka kai su.
EFCC ta daina jira sai an yi sata
Shugaban na EFCC yake bayanin dabarun da suke bi a yau:
"Meyasa za mu jira har sai an saci kudi? Idan muka kudi da ake da zargi a kan su, za mu rufe su.
"Za a shafe awanni 72, sai mu tambaya mu ji ina za a kai kudin?"
Kudin karamar hukuma sun shiga Crypto
Vanguard ta rahoto shi yana bada misali da wasu kudi da aka dauka daga asusun karamar hukuma, aka aika zuwa wani kamfani.
Daga kamfanin kuma sai aka shigar da su cikin wani asusun Crypto, ya ce irin haka ya zaburar da jami'an EFCC su dauki mataki.
A wajen taron ya yi bayanin yadda ma’aikatan gwamnati suka koma sace dukiyar jama’a, suna awon gaba da su ta fasahar Crypto.
Gano kudi yana kara yi wa EFCC wahala
Olukoyede yake cewa cikin awanni 24 da satar kudi sai a tura su wannan asusu, lamarin da ya sa ake shan wahalar a gano su.

Kara karanta wannan
Jita jitar Opay da shahararrun labaran bogi da suka rika yawo makon jiya a Najeriya
21st Century Chronicle ta ce an ji shi yana bayanin yadda fasahar zamani a yau ta jawo ake shan wahala wajen gano kudin sata.
Saboda haka ne yanzu aka yi wa irin wadannan kamfanoni har 40 rajista da gwamnati, kuma har ake iya binciken asusu na Crypto.
Ta fuskar doka kuwa, EFCC ta fito da dabara da ta ke bi domin karbo kudin haramun, maimakon a yi shekaru 10 zuwa 15 ana shari’a.
A karshe hukumar ta nemi ‘yan jarida su cigaba da sa-ido wajen yakar rashin gaskiya akasa.

Source: Facebook
Zancen rufe Opay da wasu labaran karya
Labaran kanzon kurege da rahotanni marasa makama sun cika shafukan sada zumunta a makon da ya gabata kamar yadda aka karanta.
Manyan labaran karya da aka ji sun hada har da jita-jitar cewa bankin Opay zai tafi hutu da kuma soke kwamitin yakin zaben APC.
Haka zalika, an karyata da'awar cewa hafsan tsaro ya yi wa Bola Tinubu mubaya'a daidai lokacin da aka kada gangar siyasar 2027.
Asali: Legit.ng