Masu Biyan Haya Za Su Cigaba da Wahala a 2022, Kudin Gida Zai Cigaba da Tashi

Masu Biyan Haya Za Su Cigaba da Wahala a 2022, Kudin Gida Zai Cigaba da Tashi

  • Rahoton UbosiEleh na shekarar 2021 da ta wuce ya yi hasashen yadda farashin gidaje za su kasance
  • Masana sun nuna har yanzu kudin gidajen haya ba za su sauko ba, sai dai abin da ya kara yin gaba
  • Duk da halin da aka shiga a lokacin annobar COVID-19, darajar filaye da gidaje na haya bai fadi ba

Wani rahoto da ya zo a Punch ya nuna tashin da kudin hayar gidaje yake yi bai zo karshe ba. Kudin gidaje za su cigaba da tashi zuwa karshen 2022.

Rahoton UbosiEleh na shekarar 2021 da aka wallafa ya nuna tun bayan annobar cutar Coronavirus kudin haya yake tashi kowace shekara a Najeriya.

Tun lokacin annobar, kamfanoni da kungiyoyi suka fara aiki daga gida, a maimakon zuwa ofis.

Duk da karancin bukatar gidaje saboda rashin zuwa ofis, harkar gidaje ya motsa da 2.81% a karshen 2020, hakan ya kawo karshen matsin tattali.

Kudin haya da filaye na tashi

Duk da karancin neman gidajen haya da aka yi a lokacin COVID-19, farashin filaye da kama haya bai ragu ba, sai ma suka karu daga 1.77% zuwa 3.5%.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masana suna tunanin cigaban da aka samu ba zai daure ba, musamman idan aka duba matsalar tsaro da tashin farashin kayan gine-gine da 50%.

Gida.
Zanen wani gida a Najeriya Hoto: mercy-homes.com
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar ta fada, masana tattalin sun yi hasashen abin da zai faru da gidaje a shekarar bana. A halin yanzu an shiga wata na takwas.

A watannin farko na shekarar 2021, binciken da aka yi a kan gidaje ya nuna kudin da ake biya wajen hayan ofisoshi a biranen kasar nan yana tashi.

Rububin gidaje masu daki 2-3

A hasashen da aka yi, kudin hayan gidaje da farashin filaye zai kara tsada. Sannan ana sa ran za a rika yawan neman gidaje 'yan daki biyu ko uku.

Irin wadannan gidaje masu dakuna biyu ko uku za su fi kasuwa a kan sauran gidaje.

Canji a Legas da Abuja

Wannan dogon rahoto mai shafi 128 ya nuna masu neman gidajen haya za su karu da 25%. A Legas za a samu karin 10-20% na masu bukatar gidan haya.

A birnin tarayya Abuja, ana tunanin bukatar gidajen haya da kadarori zai tashi da 15 zuwa 20%.

An kama Fasto da kwaya

Dazu aka ji labari jami'a hukumar NDLEA sun kama wani Fasto mai suna Anietie Okon Effiong da hannu a harkar shigo da kwayoyi daga kasar Indiya.

NDLEA ta kuma yi nasarar cafke masu safarar kwayoyi a jihohin Legas, Kaduna da Sokoto. Wannan na cikin nasarorin da ake samu a 'yan kwanakin nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel