Yadda Wasu Ƴan Najeriya ke Tsallake Garuruwansu zuwa Nijar saboda Hare Hare

Yadda Wasu Ƴan Najeriya ke Tsallake Garuruwansu zuwa Nijar saboda Hare Hare

  • Mazauna Borgu a Niger sun fara barin gidajensu zuwa Jamhuriyar Benin saboda hare-haren ’yan bindiga da suka addabi yankin tsawon lokaci
  • Dan takarar ADC, Murtala Haliru Dantoro, ya roƙi Tinubu ya tura dakarun tsaro na dindindin domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma
  • Dantoro ya ce rugujewar gada mai muhimmanci da ke haɗa Borgu da Benin, Kebbi da Sokoto ta ƙara dagula harkokin kasuwanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Borgu, Niger - Mazauna ƙaramar hukumar Borgu ta Niger sun fara barin gidajensu zuwa Jamhuriyar Benin, sakamakon hare-haren ’yan bindiga.

Dan takarar jam’iyyar ADC na Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Borgu/Agwara, Murtala Haliru Dantoro ya bayyana haka a matsayin abin takaici.

Wasu Ƴan Niger na tserewa zuwa Nijar
Taswirar jihar Niger da ke fama da matsalar yan bindiga. Hoto: Legit.
Source: Original

Dantoro ya yi wannan gargaɗin ne yayin wani taron manema labarai kan tabarbarewar tsaro a yankin, inda ya ce al’ummar yankin na ƙara rayuwa cikin wani yanayi na killacewa, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Babbar nasara: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin ’yan ta’adda 2 a Katsina

Kiran dan takara a ADC ga Tinubu

Dan takarar ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da Gwamnatin Tarayya da su gaggauta tura jami’an tsaro na dindindin zuwa yankin.

Ya ce kisa, garkuwa da mutane, ƙaurar da jama’a daga gidajensu, da kuma hana noma da zirga-zirga, na ci gaba da shafar al’ummomi a faɗin masarautar.

Ya buƙaci gwamnati ta ɗauki matakan kariya tun kafin hare-hare su faru, maimakon jiran afkuwar lamarin sannan ta mayar da martani bayan an rasa rayuka da dukiyoyi.

A cewarsa, al’ummar Borgu ba sa neman gwamnati ta zo ta ceto su bayan an kai hari, sai dai suna buƙatar isasshen tsaro da zai hana hare-haren faruwa.

Ya ce:

“Ba muna neman a zo a cece mu bayan abin ya faru ba. Muna neman tsaro kafin abin ya faru.”
An bukaci agajin Tinubu kan rashin tsaro a Niger
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yana jawabi a taro. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Abin da yankin Niger ke bukata

Dantoro ya jaddada cewa Borgu ba ta neman tallafi ko sadaka daga gwamnati, sai dai kariya da tsaron da doka ta bai wa kowane ɗan Najeriya.

Kara karanta wannan

INEC ta fitar da sunayen yan takarar gwamna na jihohi a zaben 2027, an canza wasu

Dan siyasar ya nuna damuwa kan lalacewar wata babbar gada da ke haɗa Borgu da Jamhuriyar Benin, da kuma jihohin Kebbi da Sokoto.

Ya bayyana gadar a matsayin muhimmiyar hanyar tattalin arziki ga al’ummar masarautar, yana mai cewa lalacewarta ta kawo cikas ga zirga-zirga, kasuwanci da sauran harkokin tattalin arziki.

Ya ce matsalar gadar ta ƙara tsananta wahalhalun da mazauna yankin ke fuskanta, musamman yayin da matsalar tsaro ke ci gaba da tabarbarewa.

Dan takarar ADC ya yi gargaɗin cewa tabarbarewar tsaro yanzu ta tilasta wa wasu mazauna yankin tsallakawa zuwa Jamhuriyar Benin domin neman mafaka da tsira.

Ya bayyana wannan lamari a matsayin matsalar jin ƙai da kuma barazana ga tsaron ƙasa, yana kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Niger su ɗauki mataki cikin gaggawa.

Sojoji sun shiga daji ceto mutane

An ji cewa rndunar tsaro ta Najeriya ta shiga Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Niger domin ceto daruruwan mutanen da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su.

Matakin ya biyo bayan umarnin shugaba Bola Tinubu ga jami'an tsaro da su tabbatar da tsaron al'ummomin da lamarin ya shafa.

Yan sanda sun ce adadin waɗanda aka sace ya kai tsakanin 155 zuwa 164, yayin da 'yan ta'addan suka yi iƙirarin cewa suna riƙe da mutane sama da 500.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.