Kwamishina Ya Yi Amai Ya Lashe kan Barazana ga Masu Adawa da APC

Kwamishina Ya Yi Amai Ya Lashe kan Barazana ga Masu Adawa da APC

  • Kwamishinan Borno Saina Buba ya nemi afuwar jama’a, musamman magoya bayan adawa, kan wata magana da ya yi a wani taron City Boy Movement
  • Buba ya ce maganar tasa ba ta nufin barazana ko tauye haƙƙin kowa ba, amma ya janye ta saboda damuwar da ta haifar a tsakanin jama’a
  • Kwamishinan ya ce kalaman nasa ba sa wakiltar matsayar APC ko gwamnatin Gwamna Babagana Umara Zulum kan dimokuraɗiyya da haƙƙin ’yan ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Maiduguri, Borno - Kwamishinan Yaƙi da Talauci, Matasa da Wasanni na Jihar Borno, Hon. Sainna Buba, ya nemi afuwar jama’a, musamman magoya bayan jam’iyyun adawa, kan wata magana da ya yi wadda ta jawo cece-kuce.

Buba ya yi kalaman ne yayin wani taron da City Boy Movement ta shirya a Maiduguri, inda ya yi barazanar karya yatsan duk wanda ya daga masu yatsa.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ba 'yan Najeriya shawara da ya sanya kansa cikin wadanda suka jefa kasar a matsala

Kwamishinan Borno ya janye kalamansa
Kwamishinan matasa da wasanni na Borno, Sainna Buba Hoto: Tijjani Mohammed Mohammed
Source: Facebook

Buba ya janye kalaman tare da neman afuwa

Da yake magana da manema labarai a ofishinsa da ke Maiduguri ranar Laraba, Buba ya janye kalaman a hukumance tare da neman afuwar duk wanda maganar ta ɓata wa rai, cewar rahoton jaridar Leadership.

Ya ce kalaman da ya yi a shirin ƙarfafa gwiwa da City Boy Movement ta shirya sun haifar da damuwa a tsakanin jama’a a cikin ‘yan kwanakin nan.

Kwamishinan ya ce bai taɓa nufin kalaman nasa su cutar da wani ko su tauye haƙƙin al’ummar jihar na zaɓi da shiga ƙungiyoyi ba, jaridar Vanguard ta kawo labarin.

“Ina so na bayyana ba tare da wata shakka ba cewa maganata ba ta taɓa nufin cutarwa ko tauye muhimman haƙƙoƙin mutanen jihar mu na ‘yancin zaɓi da haɗa kai ba, kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya ya tanada,” in ji shi.

Ya ce ba a fahimce shi ba

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da 'yan bindiga suka hallaka shugaban APC a Kano

Ya ƙara da cewa a baya ya yi bayanin cewa bai kamata a ɗauki maganar a ma’anarta ta zahiri ba.

Sai dai ya ce saboda damuwar da kalaman suka ci gaba da haifarwa, ya ga ya dace ya janye su a hukumance.

“Saboda damuwar da wannan magana ta ci gaba da haifarwa, ina amfani da wannan dama wajen janye maganata a hukumance tare da neman afuwar al’ummar Jihar Borno da ma sauran jama’a kan duk wani laifi ko ɓacin rai da ta haifar,” in ji Buba.

Ya ce kalamansa ba sa wakiltar APC

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa maganar da ya yi ba ta wakiltar matsayar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ko gwamnatin Gwamna Babagana Umara Zulum ba.

“Ina so nabayyana cewa maganata ta kowace fuska bata wakiltar manufofi da akidar APC ko gwamnatin Mai Girma Gwamna, Farfesa Babagana Umara Zulum,” in ji shi.

Buba ya ce gwamnatin jihar ta himmatu wajen kare haƙƙoƙin jama’a tare da inganta ƙa’idojin dimokuraɗiyya.

Ya ce gwamnatin ba ta da niyyar tauye haƙƙin kowane ɗan ƙasa, yana mai cewa APC da gwamnatin Zulum suna mutunta kowane ɓangare na al’umma, musamman matasa.

Kara karanta wannan

"Gwamnatinmu ce"; Kwamishina ya yi barazanar guntile 'yan yatsun masu adawa da APC

Kwamishinan Borno ya fito ya bayar da hakuri
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An bukaci cafke ciyaman a Abuja

A wani labarin kuma, kun ji cewa Jam'iyyar ADC ta bukaci hukumomin tsaro su gaggauta kama shugaban karamar hukumar Kuje da ke Abuja, Danjuma Shekwolo.

Jam'iyyar ADC mai adawa ta bukaci a cafke Danjuma ne bisa wasu kalamai da ya yi kan masu adawa da jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng