Yan Bindiga Suna Lokacinsu a Arewa, Sun Ƙaƙaba wa Ƴan Sokoto Tarar N40m

Yan Bindiga Suna Lokacinsu a Arewa, Sun Ƙaƙaba wa Ƴan Sokoto Tarar N40m

  • ‘Yan bindiga sun nemi al’ummar Kebbe ta Sokoto su biya harajin Naira miliyan 40, tare da barazanar kai hari da kona gidaje
  • Barazanar ta jefa mazauna garin cikin fargaba, inda wasu suka fara barin gidajensu, yayin da kasuwanci ya samu koma baya
  • Yan bindigar sun tuntubi wakilin Sarkin Kabin Kebbe ta waya, yayin da ‘yan sanda suka ce suna sane da lamarin kuma suna aiki a kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kebbe, Sokoto - Mazauna garin Kebbe da ke ƙaramar hukumar Kebbe a Sokoto na cikin fargaba, bayan‘yan bindiga ne sun nemi Naira miliyan 40.

‘Yan bindigar sun kuma yi barazanar kai hari garin tare da kona kadarori idan al’ummar ba ta biya kuɗin da suka nema ba.

Yan bindiga sun saka harajin N40m ga wasu ƴan Sokoto
Taswirar jihar Sokoto da yan bindiga ke yawan kai hare-hare da sace mutane. Hoto: Legit.
Source: Original

Sokoto: Yan bindiga sun saka harajin N40m

Kara karanta wannan

Magidanta za su iya zuwa gidan yari kan aukawa matansu ba tare da yardarsu ba

Wata majiya da ta san abin da ya faru ta shaida wa Daily Trust cewa Jaji yana tafiya ne ta wata hanya da ake zargin ‘yan bindigar suna amfani da ita.

An ce Abara Jaji, wani mazaunin garin, ne ya isar da wannan saƙo bayan ‘yan bindigar sun tare shi a lokacin da yake neman itacen girki.

Majiyar ta ce lokacin da Jaji ya hangi ‘yan bindigar, sai ya gudu ya bar babur ɗinsa, amma su kuma suka bi shi a kan babura.

Daga bisani, sun cim masa tare da kewaye shi, sannan suka tambaye shi garin da ya fito.

Jaji, wanda ake zargin tsoro ya kama shi, ya ce shi ɗan Kebbe ne, tare da roƙonsu cewa ba shi da kuɗi.

Daga nan ‘yan bindigar suka ba shi wayar Tecno mai ɗauke da katin SIM, suka umarce shi ya kai wa Sarkin Kabin Kebbe ko wakilinsa.

Sun kuma nemi al’ummar Kebbe ta biya Naira miliyan 40, tare da barazanar shiga garin, kashe mutane da kona kadarori idan ba a biya ba.

Yan bindiga sun takurawa mazauna Sokoto
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto. Hoto: @aliyuskt.
Source: Facebook

Abin da mazauna yankin ke cewa

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace shugaban APC a Kano bayan kai kazamin hari

Wani shaida da ya nemi a sakaya sunansa ya ce Jaji ya isa gidan Sarkin Kabin Kebbe, Alhaji Muhammad Labbo Margai, da misalin ƙarfe 9:30 na safe ranar Talata.

Sai dai ya tarar da wakilin sarkin, Murtala Muhammad, wanda ya bayyana masa cewa ‘yan bindigar sun aiko shi da wayar.

Shaidan ya ce daga baya ‘yan bindigar suka kira wayar, inda suka sake maimaita buƙatarsu ta Naira miliyan 40.

Murtala ya gaya wa masu kiran cewa lamarin ya shafi daukacin al’umma, don haka ba zai iya yanke hukunci shi kaɗai ba.

Daga nan ya kai Jaji wajen DPO, inda wasu jami’an tsaro da ke ƙaramar hukumar su ma suke.

Majiyar ta ce:

“Yayin da suke bayyana abin da ya faru ga jami’an tsaron, ‘yan bindigar suka sake kira. Aka saka wayar a hands-free, don haka kowa ya ji abin da suke nema."

Wani mazaunin garin ya ce mahaifiyarsa da ƙanwarsa, wadda ta zo gida domin yin wankan jego, sun bar garin saboda tsoron abin da ka iya faruwa.

Ya ce wasu mazauna garin ma ba sa kwana a gidajensu saboda fargabar harin ‘yan bindigar, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya kawo sabon rikici a ADC kan yadda Atiku ke sukar Tinubu

A cewarsa, tun farko ‘yan bindigar sun bukaci a biya kuɗin ranar Talata, amma wakilin Sarkin Kabin Kebbe ya nemi a ba shi lokaci domin tuntubar al’umma kafin yanke shawara.

Yan bindiga sun kai farmaki a Sokoto

Mun ba ku labarin cewa a kashe manoma akalla takwas, yayin da wasu biyar suka samu raunuka bayan ’yan bindiga sun kai hari Ghandi da ke karamar hukumar Rabah ta Sokoto.

Yan bindigar sun mamaye garin da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar Lahadi, inda suka rika harbin mazauna garin da manoma.

Wani mazaunin yankin ya ce ana zargin harin ramuwar gayya ne bayan jami’an tsaro sun kashe wasu daga cikin ’yan bindigar a wasu samame.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.