Magidanta Za Su Iya Zuwa Gidan Yari kan Aukawa Matansu ba Tare da Yardarsu ba

Magidanta Za Su Iya Zuwa Gidan Yari kan Aukawa Matansu ba Tare da Yardarsu ba

  • Gwamnatin Lagos ta kawo wata sabuwar doka da ta shafi magidanta wacce za ta iya jefa su a gidan gyaran hali
  • Hukumomi sun gargadi mazaje cewa tilasta wa mata yin jima’i ba tare da yardarsu ba na iya kaiwa ga hukuncin daurin rai da rai
  • Daraktan Masu Shigar da Ƙara na Lagos, Dr Babajide Martins, ya ce doka ba ta kira hakan fyaɗe ba, amma tana hukunta shi matsayin cin zarafin jima’i

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Gwamnatin Lagos ta gargadi mazaje kan tilasta wa matansu yin jima’i ba tare da yardarsu ba.

Gwamnatin Lagos ta sha alwashin daure mazaje da dama tana mai cewa hakan na iya jawo hukuncin daurin rai da rai.

Lagos za ta daure magidanta da ke aukawa matansu ba tare da amincewarsu ba
Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos. Hoto: Babajide Sanwo-Olu.
Source: Twitter

Daraktan Masu Shigar da Ƙara na Ma’aikatar Shari’a ta Lagos, Dr Babajide Martins, ne ya yi wannan gargadin yayin wani taron manema labarai, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Mata ta kalli tawagar APC ido da ido, ta ce ko kuri'a 1 ba za su samu ba

Yadda mata za ta iya karar mijinta

Taron na daga cikin shirye-shiryen fara watan wayar da kan jama’a kan cin zarafin cikin gida da na jima’i a Lagos.

Hukumar Kula da Cin Zarafin Cikin Gida da Na Jima’i (DSVA) ce ta shirya kamfen ɗin domin wayar da kan jama’a kan matsalar.

Yayin zaman tambayoyi da amsoshi, DPP Martins ya bayyana matsayin doka kan yin jima’i ba tare da yardar mace ba a cikin aure.

Da aka tambaye shi ko matar aure za ta iya kai karar mijinta bisa zargin fyaɗe saboda ya yi jima’i da ita ba tare da yardarta ba, Martins ya yi bayani.

Ya ce, duk da cewa dokar Najeriya ba ta amince da laifin fyaɗe tsakanin ma’aurata a irin wannan yanayi ba, dokar laifuka ta Lagos ta tanadi wani laifi.

A cewarsa, mijin da ya tilasta wa matarsa yin jima’i bayan ta nuna ba ta yarda ba, na iya fuskantar tuhuma karkashin wannan tanadi na doka.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace shugaban APC a Kano bayan kai kazamin hari

Za a tura wasu magidanta gidan yari
Taswirar jihar Lagos da ke Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Gargadin da aka yi wa mazaje

Martins ya ce yardar mace muhimmin abu ce a duk wata hulɗar jima’i, ciki har da tsakanin ma’aurata, musamman idan akwai rashin jituwa tsakaninsu.

Ya ce:

"Duk mutumin da yake ganin saboda ya biya sadakin matarsa, babu wanda zai iya kalubalantarsa kan cin zarafin cikin gida, ya kamata matar ta kai rahoton irin wannan mutumin ga Hukumar Kula da Cin Zarafin Cikin Gida da Na Jima’i.
“A karkashin dokar laifuka ta Lagos, ba za a zargi mutum da yi wa matarsa fyaɗe ba idan suna tare kuma suna zaman lafiya.”

Martins ya kara bayyana cewa doka ta bambanta tsakanin fyaɗe da cin zarafin jima’i ta hanyar shigar da gabobin jima’i idan lamarin ya shafi ma’aurata.

Sai dai ya ce idan wata matsala ta taso tsakanin ma’auratan, matar ta ƙi yin jima’i, mijin ba shi da ikon tilasta mata.

Ya bukaci matan da ke fuskantar kowace irin cin zarafi na cikin gida ko na jima’i da su kai rahoto ga hukumar DSVA, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya kawo sabon rikici a ADC kan yadda Atiku ke sukar Tinubu

Gwamnatin Lagos ta rufe otal da coci

An ji cewa Gwamnatin jihar Legas ta kara rufe wani cocin RCCG, gidan burodi da otal saboda karya dokar kare muhalli da hayaniya.

ukumar kula da muhalli ta jihar Legas watau LASEPA ce ta ce ba za ta ɗagawa duk wani wanda ya karya doka ƙafa ba.

Shugaban hukumar, Dr. Babatunde Ajayi, ya buƙaci mazauna su bi dokar kare muhalli sau da ƙafa domin gudun matsala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.