Sojoji Sun Kewaye Dajin da 'Yan Bindiga Suka Buya don Ceto Mutane
- Rundunar tsaro ta Najeriya ta shiga Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Niger domin ceto daruruwan mutanen da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su
- Matakin ya biyo bayan umarnin shugaba Bola Tinubu ga jami'an tsaro da su tabbatar da tsaron al'ummomin da lamarin ya shafa
- 'Yan sanda sun ce adadin waɗanda aka sace ya kai tsakanin 155 zuwa 164, yayin da 'yan ta'addan suka yi iƙirarin cewa suna riƙe da mutane sama da 500
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jami'an tsaro da suka haɗa da sojoji, 'yan sanda DSS sun isa Borgu a Jihar Niger domin gudanar da aikin ceto daruruwan mutanen da ake zargin 'yan ta'adda sun yi garkuwa da su.
Matakin ya biyo bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu ga jami'an tsaro na shiga yankin domin tabbatar da tsaron al'ummomin da abin ya shafa da kuma ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan
An yi abin kirki: Jami'an 'yan sanda sun ceto 'yan bautar kasa 11 a hannun 'yan bindiga

Source: Facebook
Punch ta ruwaito cewa wani shugaban al'umma a Babanna, Idris Shiyaki, ya tabbatar da isowar jami'an tsaron yankin, yana mai cewa an fara faɗaɗa sansanin sojojin da aka tura wurin.
An fara aikin ceto jama'a
Wani babban jami'in DSS ya tabbatar da cewa tawagar jami'an ta isa yankin tun ranar Laraba, yayin da ake sa ran wasu jami'ai za su ƙara zuwa.
Wani babban jami'in tsaro ya kuma ce Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa ta tura jami'ai yankin nan take bayan umarnin Shugaban Ƙasa.
Ya ce aikin farko shi ne tattara bayanan sirri domin fahimtar halin da ake ciki kafin fara cikakken aikin ceto.
"Ba a gudanar da aikin ceto cikin gaggawa ba. Wannan wani tsari ne, amma zan iya tabbatar muku cewa za a ceto waɗanda aka sace,"
In ji jami'in.
Channesl TV ta wallafa cewa 'yan sanda sun ce aikin ceto ya riga ya fara, amma jami'an tsaro na taka-tsantsan domin tabbatar da cewa ba a jefa rayuwar waɗanda aka sace cikin haɗari ba.

Source: Original
Hare-haren da aka kai
Hare-haren na ranar 21 ga Agusta sun shafi al'ummomi da dama a Borgu, inda ake zargin ƙungiyoyin 'yan ta'adda na Lakurawa da Boko Haram ne suka kai farmakin.
An ce maharan sun shiga Masallacin Kpenya da ke yankin Dekara da kuma ƙauyukan Gidan-Zana da Kpenya, inda suka kashe wasu mazauna yankin, suka yi garkuwa da wasu tare da kona gidaje.
Shiyaki ya ce kusan al'ummomi biyar da suka haɗa da Mayanga, Dekara, Kapubara, Gbagbazhi da Yagba ne lamarin ya shafa.
'Yan bindiga na kara karfi
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani rahoton ƙungiyar leƙen asiri ta SBM Intelligence ya nuna cewa an biya sama da dala miliyan 5.8 a matsayin kuɗin fansa a Najeriya
Rahoton ya ce jimillar kuɗin da aka biya ya kai naira biliyan 7.78, yayin da mutane 7,825 suka faɗa hannun masu garkuwa da mutane a cikin wannan lokacin.
Ƙungiyar ta ce adadin mutanen da aka sace ya ƙaru da kashi 66 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, tana mai gargadin cewa biyan kuɗin fansa ya yi yawa.
Asali: Legit.ng
