Babban Sarki Ya Rasu a Arewa, Tinubu Ya Tuna Ƙoƙarin Basaraken kan Tsaro

Babban Sarki Ya Rasu a Arewa, Tinubu Ya Tuna Ƙoƙarin Basaraken kan Tsaro

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi alhinin rasuwar Sarkin Zamfaran Zurmi inda ya yaba da jajircewarsa wajen fuskantar matsalolin tsaro
  • Tinubu ya bayyana marigayi sarkin a matsayin jagora mai kawo zaman lafiya, wanda shawararsa ta taimaka wajen ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a Zamfara
  • Shugaban ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, masarautar Zurmi da gwamnatin Zamfara, tare da roƙon Allah Ya gafarta masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alhinin rasuwar Sarkin Zamfaran Zurmi, Alhaji Bello Sulaiman.

Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin jagora mai tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar Sarkin Zurmi
Shugaba Bola Tinubu da marigayi Sarkin Zurmi, Alhaji Bello Sulaiman. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da hadin shugaban ƙasa kan yaɗa labarai, Abdulaziz Abdulaziz ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Yadda wasu ƴan Najeriya ke tsallake garuruwansu zuwa Benin saboda hare hare

Sarkin, wanda ya hau gadon sarauta shekaru biyar da suka gabata, ya rasu ne a ranar Litinin bayan ya jagoranci masarautarsa cikin hikima.

A cikin, Tinubu ya ce marigayin ya jagoranci masarautar Zurmi cikin hikima, mutunci da jajircewa a wani lokaci mai matuƙar wahala.

Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga Majalisar Masarautar Zurmi, gwamnatin Zamfara da al’ummar jihar, da kuma daukacin masarautun gargajiya na Najeriya.

Shugaban ƙasar ya yaba musamman da rawar da Sulaiman ya taka wajen jagorantar masarautar cikin mawuyacin halin tsaro da yankin ke fuskanta.

Tinubu ya ce marigayin ya kasance mai ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai da juriya tsakanin al’ummar masarautar duk da ƙalubalen da suke fuskanta.

Ya ƙara da cewa shawarwarin marigayin da jajircewarsa wajen samar da zaman lafiya sun taimaka wajen faɗaɗa ƙoƙarin dawo da tsaro da zaman lafiya mai ɗorewa a Zamfara da Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Atiku ya ɗauki alkawarin da zai faranta wa ɗaliban Najeriya rai kan kuɗin NELFUND

Sanarwar ta ce:

“Mai Martaba ya kasance jagora da ke samar da kwanciyar hankali, wanda shawararsa mai hikima da sadaukarwarsa wajen samar da zaman lafiya suka kasance masu matuƙar amfani ga masarautar Zurmi.
“Wannan kokari bai tsaya a masarautar kaɗai ba, sun taimaka wa Zamfara da ƙoƙarin ƙasarmu na dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a Arewa maso Yamma."
Sarkin Zurmi ya rasu a Najeriya
Marigayi Sarkin Zurmi, Alhaji Bello Sulaiman. Hoto: Masarautar Gusau.
Source: Facebook

Gudunmawar da basaraken ya bayar

Tinubu ya bayyana marigayi Sarkin Zamfaran Zurmi a matsayin basarake mai matuƙar daraja, wanda mulkinsa na shekaru biyar ya kasance cike da jagoranci da sadaukarwa.

Ya ce Sulaiman ya nuna jajircewa ta musamman wajen tunkarar mawuyacin halin tsaro da ya addabi masarautar, tare da ci gaba da ƙarfafa zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya kadu kan rasuwar babban sarki mai daraja a Zamfara

Shugaban ƙasar ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kurakuransa, Ya saka masa da alherin ayyukansa, sannan Ya ba shi Aljannar Firdausi.

Ya kuma roƙi Allah Ya ba iyalan marigayin, al’ummar masarautar da duk masu alhinin rasuwarsa haƙuri, ƙarfi da juriyar jure wannan babban rashi.

Sarkin Ijebu ya rasu a Najeriya

An ji cewa Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya kai ziyara ta ta’aziyya ga dangin marigayi Awujale na Ijebu, Oba Sikiru Kayode Adetona.

Sarkin Musulmi ya fara da ziyartar kabarin marigayin inda ya yi addu’a don samun Aljanna Firdausi, kafin tarbar girmamawa daga manyan Ijebu.

Sarakunan Ijebu da iyalan marigayin, ciki har da matansa da ‘ya’yansa, sun tarbi Sarkin Musulmi cikin girmamawa tare da nuna godiya sosai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.