Lauya Ya Jawo Matsala a Karar da Atiku Ya Kai Kotu kan Takarar Tinubu a Zaben 2027

Lauya Ya Jawo Matsala a Karar da Atiku Ya Kai Kotu kan Takarar Tinubu a Zaben 2027

  • An samu tsaiko a karar da dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar ya shigar da Shugaba Bola Tinubu a babbar kotun tarayya da ke Abuja
  • Lauyan Atiku ne ya jawo tsaikon da aka samu sakamakon ƙim mika takardun ƙarar ga lauyan Shugaba Tinubu
  • Mai shari’a Inyang Ekwo ya dage shari’ar zuwa 28 ga Satumba, 2026 domin Atiku da jam’iyyarsa su gyara kura-kuransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - An samu wata matsala a ƙarar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya shigar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Kotu ta dauki mataki kan bukatar Atiku ta hana Tinubu takara a 2027

Zaman da kotun ta shirya yau Talata ya karkare ba tare da shiga shari'ar ka'in da na'in ba saboda lauyan Atiku bai mika takardun fara shari’ar ga lauyan Shugaba Bola Tinubu ba.

Tinubu da Atiku.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a bangaren dama da dan takarar ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar a bangaren hagu Hoto: @aonanuga1956, Atiku Abubakar
Source: Twitter

The Nation ta ruwaito cewa karar Atiku mai lamba FHC/ABJ/CS/1888/2026 an shigar da ita da sunansa da kuma na jam’iyyar ADC, inda suke neman, cikin wasu abubuwa, kotu ta hana Shugaba Tinubu tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

An sanya Shugaba Tinubu, APC da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a matsayin waɗanda ake ƙara tare da wasu.

Lauyan Atiku ya jawo tsaiko a kotu

A farkon zaman kotun ranar Talata, lauyan Atiku, Joseph Onu Silas, ya shaida wa kotun cewa har yanzu ba a miƙa wa Shugaba Tinubu takardun fara shari’ar ba.

Silas ya ce yana buƙatar umarnin kotu domin a miƙa wa shugaban ƙasa takardun ta wata hanyar da ba kai tsaye ba.

A wannan lokacin ne wani babban lauya mai darajar SAN, Omosanya Popoola, wanda ya jagoranci tawagar lauyoyin Shugaba Tinubu da APC, ya ce a shirye yake ya karɓi takardun a madadin shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Kano da wasu jihohi 19 sun fito a wuraren da Bola Tinubu zai samu nasara a zaben 2027

Popoola ya roƙi kotun ta umarci lauyan Atiku ya miƙa masa takardun a gaban kotu domin ya kai su ga Shugaba Tinubu. Sai dai lauyan Atiku ya yi adawa da wannan buƙata.

Lauyan Atiku ya nemi rubutacciyar shaida

Lauyan Atiku ya buƙaci Popoola ya gabatar da rubutacciyar shaida cewa yana da izinin Shugaba Tinubu na wakiltarsa a kotu kafin ya miƙa masa takardun.

Wani babban lauya, Alex Izinyon, wanda ya wakilci INEC, ya yi ƙoƙarin shiga tsakani, amma Silas bai amince da hakan ba.

Kotu.
Gudumar daa'kalai ke amfani da ita a zaman kotunan Najeriya Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Daga bisani, Mai shari’a Inyang Ekwo ya shiga lamarin, inda ya ce zai dage shari’ar zuwa wani lokaci domin bai wa Atiku da jam’iyyarsa damar daidaita harkokinsu.

Mai shari’a Ekwo ya daga shari’ar zuwa 28 ga Satumba domin ci gaba da ambaton ƙarar, kamr yadda tashar Channels tv ta ruwaito.

Atiku ya soki tafiya hutun Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan tafiyarsa Turai domin hutun mako uku.

Ya bayyana cewa tafiyar Tinubu ta zo ne a lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa, tsadar man fetur, tashin kuɗin sufuri da matsalar tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262