Tinubu Zai Cigaba da Aiki daga Turai, Babu Zancen Mika wa Kashim Ragamar Mulki
- Shugaban Najeriya ya tafi hutun makonni uku a ketare amma bai ba Kashim Shettima mulkin rikon kwarya ba
- Bola Tinubu zai rika karbar rahotannin kullum daga ministoci da shugabannin tsaro yayin da yake hutu a Ingila
- Zaman zai ba shugaban kasar damar shan iska gabanin fara shirye-shiryen kamfen na zaben shekara ta 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya dauki hutun makonni uku da nufin ya huta kamar yadda shugabanni suka saba.
Ana sa ran shugaban na Najeriya zai dawo cikin watan Satumban 2026 da karfinsa domin tunkarar aikin ofis da yakin neman zabe.

Source: Getty Images
Hutun da Bola Tinubu zai yi a Birtaniya
Da yake yi wa ‘yan jarida bayani a filin jirgi, The Nation ta rahoto Sunday Dare yana karin haske game da hutun uban gidansa.

Kara karanta wannan
Peter Obi ya kinkimo batun da yan Najeriya suka daɗe suna son sani game da Tinubu
Mista Dare wanda yake taimaka wa Shugaban kasa a harkokin yada labarai da sadarwa ya ce aiki ba zai tsaya wa Bola Tinubu.
Dare yana cikin mutanen da za su tallata takarar Bola Tinubu/Kashim Shettima a zaben 2027.
Shugaba Tinubu zai tsaida aiki lokacin hutu?
Ko da yake ya tafi kasar waje, hadimin ya ce shugaba Tinubu zai rika karbar bayanai a kowace rana daga manyan jami’an gwamnati.
Shugaban na Najeriya zai rika samun muhimman bayanai game da sha’anin kasa daga ministoci, hafsoshin tsaro da sauransu.
Dare ya yi wannan bayani lokacin da jirgin shugaban kasa yake babban filin Nnamdi Azikiwe a Abuja kan hanyarsa ta zuwa Ingila.
Atiku ya soki yadda za a bar Najeriya
Wannan karin haske yana zuwa ne lokacin da su Atiku Abubakar suke korafin cewa an bar kasa babu shugaban da zai kula da ita.
'Dan takaran ADC ya fadi hakan ne saboda a lokacin Mai girma Kashim Shettima bai Najeriya.
Dare ya ce hutun da shugaban kasa ya tafi bai nufin shikenan ya rabu da harkokin gudaanr da mulki, zai cigaba da aiki daga Bitaniya.
“Duk da hutu zai tafi, mun san cewa zai cigaba da kula da harkokin kasa a kowace rana.
"Zai rika samun bayanai daga ministocinsa, daga hafsoshin tsaro da kuma duk wanda yake rike da muhimmin matsaya a kasar mu daidai gwargwadon bukata."
- Sunday Dare

Source: Getty Images
Dalilin tafiyar Tinubu hutu zuwa kasar waje
The Guardian ta rahoto hadimin yana kokarin nuna dacewar hutun makonni ukun da Mai girma Bola Tinubu zai yi a Birtaniya.
Tsohon ministan yana ganin tun da saura watanni kadan a yi zabe, babu laifi Tinubu mai shekara 74 a duniya ya samu ya sarara.
Yake cewa ya shafe watanni masu yawa yana neman yadda za a magance rashin tsaro, matsalar tattalin arziki da sauran matsaloli.
Tafiye-tafiyen Tinubu sun ci N36bn
Tafiye tafiyen Bola Tinubu sun sa fadar shugaban kasa ta batar da biliyoyin kudi. An kuma ji cewa mai dakinsa ta kashe N700m a shekara.
Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kashe N37.64bn wajen tafiye-tafiye a cikin shekaru uku, yayin da 'yan Najeriya ke fama da matsin tattali.
Kudin sun tafi ne wajen sayen tikiti, man jirgi, dawainiya da jiragen fadar shugaban kasa, canjin dala makamantansu daga 2023 zuwa yau.
Asali: Legit.ng

