'Yan Bindiga Sun Kai Hari Kano, an Sace Babban Mai Rike da Sarautar Gargajiya da Kashe Mutane
- ‘Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da jikkata wasu biyar yayin wani hari da suka kai garin Chiromawa da ke Jihar Kano
- Maharan sun yi garkuwa da Sarkin Noma na Kano, Alhaji Yusuf Nadabo Chiromawa, bayan sun kai farmaki gidansa
- Jami’an tsaro sun fara bin sawun maharan, yayin da gwamnatin Kano ta yi alkawarin kara tsaro a yankin domin hana sake kai hare-hare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - ‘Yan bindiga sun kashe mutane uku, sun jikkata wasu biyar tare da yin garkuwa da Sarkin Noma na Kano, Alhaji Yusuf Nadabo Chiromawa.
An ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na daren Asabar, 29 ga watan Agustan 2026 a garin Chiromawa, da ke Karamar Hukumar Garun Malam ta Jihar Kano.

Source: Original
Jaridar Daily Trust ta ce shugaban Karamar Hukumar Garun Malam, Alhaji Aminu Salisu Kadawa, ne ya tabbatar da faruwar harin.
Maharan sun bude wuta
Alhaji Aminu Salisu Kadawa ya ce ‘yan bindigar sun shiga garin sannan suka nufi gidan Sarkin Noma, inda suka bude wuta ba tare da nuna bambanci ba.
Ya ce mutane uku sun mutu sakamakon harin, yayin da wasu biyar suka samu raunuka daban-daban.
Shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa wadanda suka jikkata suna karbar magani a wani asibiti.
An fara neman basaraken
Alhaji Aminu Salisu Kadawa ya ce an tura jami’an tsaro domin bin sawun maharan da kuma kokarin kubutar da Sarkin Noma da aka yi garkuwa da shi.
Ya ce shi da kansa ya jagoranci jami’an karamar hukumar zuwa asibitin, inda suka zauna har tsawon dare domin tabbatar da cewa wadanda suka jikkata sun samu kulawar da ta dace.
Gwamnati ta kara daukar matakan tsaro
Shugaban karamar hukumar ya kara da cewa gwamnatin Jihar Kano za ta kara tsaurara matakan tsaro a yankin domin dakile sake aukuwar hare-haren ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun kai harin ta'addanci bayan gwamnati ta bayar da tallafin kudi a Sokoto
Ya kuma yi kira ga mazauna garin da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da addu’a.
Alhaji Aminu Salisu Kadawa ya bukaci jama’a su hada kai da jami’an tsaro ta hanyar bayar da bayanan da za su taimaka wajen gano maharan da kuma ceto Sarkin Noma.
Ya ce hadin kan al’umma da jami’an tsaro na da matukar muhimmanci wajen ganin an kamo wadanda suka kai harin tare da dawo da basaraken cikin koshin lafiya.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun kashe mutane
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kashe mutane huɗu tare da yin garkuwa da wasu huɗu a ƙauyen Gorau da ke ƙaramar hukumar Goronyo a Jihar Sokoto.
Harin da 'yan bindigan dauke da makamai suka kai ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren Laraba, 26 ga watan Agustan 2026.
Maharan sun fi mayar da hankali ne kan iyalan da suka kasance cikin waɗanda gwamnatin Jihar Sokoto ta sanar da ba wa tallafin N1m ga kowannen su bayan aukuwar hatsarin jirgin ruwa da ya kashe mutane 65.
Asali: Legit.ng
