Dakarun Sojoji Sun Ritsa 'Yan Ta'adda a Katsina, an Kashe Babban Kwamanda

Dakarun Sojoji Sun Ritsa 'Yan Ta'adda a Katsina, an Kashe Babban Kwamanda

  • Sojojin Operation Fansan Yamma sun kashe Smally, wani kwamandan ‘yan ta’adda da ke aiki ƙarƙashin Kachalla Muhammadu Filani
  • Rundunar sojojin ta kwato manyan bindigogi guda uku, AK-47 guda biyu, magazin 11 da harsasai 180 a hannun 'yan ta'adda
  • Sojojin sun kuma ƙwace babura shida yayin wani samame da suka gudanar a ƙaramar hukumar Matazu ta jihar Katsina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Dakarun hadin gwiwar na rundunar Operation Fansan Yamma sun kashe wani muhimmin kwamandan ‘yan ta’adda da aka fi sani da “Smally” a Jihar Katsina.

An kashe Smally ne yayin wani samame da sojojin Sector 2 suka gudanar a ranar 29 ga Agusta, 2026, domin share wasu wuraren da ake zargin ‘yan ta’adda sun mayar da sansanoni a ƙaramar hukumar Matazu.

Sojoji sun kashe kwamandan 'yan ta'adda a Katsina
Taswirar jihar Katsina, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Laftanar Kanal Aliyu Danja, Jami’in Yaɗa Labarai na Operation Fansan Yamma, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ranar Lahadi, 30 ga watan Agustan 2026 a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: 'Yan mata 'yan gida daya sun rasu a hatsarin kwale kwale a Kano

‘Yan ta’adda sun yi artabu da sojoji

Laftanar Kanal Aliyu Danja ya ce yayin da sojojin ke gudanar da aikin share yankin, sun yi arangama da ‘yan ta’addan da suka yi musu tsayayya da makamai.

Sai dai ya ce dakarun sun mayar da martani da ƙarfi, inda suka yi amfani da ƙarin ƙarfin wuta wajen tilasta wa ‘yan ta’addan tserewa daga yankin.

Bayan da sojojin suka mamaye wurin, sun gudanar da bincike tare da tabbatar da kashe wani daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar.

“Yayin binciken yankin, sojoji sun tabbatar da kashe wani ɗan ta’adda mai suna Smally, wanda yake kwamanda ƙarƙashin fitaccen shugaban ‘yan ta’adda Kachalla Muhammadu Filani,” In ji shi.

An kwato makamai da babura

A yayin aikin, sojojin sun kwato makamai da dama da ake zargin ‘yan ta’addan ke amfani da su wajen kai hare-hare.

Kayayyakin da aka kwato sun haɗa da bindigogin mashina guda uku, bindigogin AK-47 guda biyu da magazin 11.

Kara karanta wannan

Tashin hankali da 'yan bindiga suka hallaka shugaban APC a Kano

Rundunar ta kuma ce ta kwato harsasai 180 da babura shida waɗanda ake amfani da su wajen zirga-zirga da gudanar da ayyukan ‘yan ta’addan.

Sojoji za su ci gaba da matsa lamba

Operation Fansan Yamma ta ce aikin wani ɓangare ne na ci gaba da kai hare-hare domin matsa wa ƙungiyoyin ‘yan ta’adda lamba da kuma wargaza ƙarfin ayyukansu.

Rundunar ta tabbatar da cewa dakarunta za su ci gaba da kai farmaki kan wuraren da ake zargin ‘yan ta’adda sun kafa sansanoni a yankin da take gudanar da ayyukanta.

Ta ce manufar ita ce rage ƙarfin ‘yan ta’adda da hana su damar gudanar da hare-hare da sauran ayyukan ta’addanci.

Sojoji sun.kashe kwamandan 'yan ta'adda a Katsina
Dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai sun kashe sama da ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP 21 a jihar Adamawa.

Dakarun sojojin sun kashe 'yan ta'addan ne a wani samame da suka kai kan sansanin ’yan ta’addan a yankin tsaunin Kopre Mountain da ke karamar hukumar Hong ta jihar Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng