Akwai Matsala: An Jero Jihohi 19 da Ake Hasashen Suna Fuskantar Babban Haɗari a Najeriya
- Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa garuruwa 915 na cikin hadarin yiwuwar afkuwar ambaliyar ruwa a jihohi 19 da Abuja
- Gwamnatin ta bayyana Kogi, Benue, Rivers da wasu jihohi 16 a matsayin wuraren da ke cikin babban hadarin ambaliya
- Gwamnati ta bukaci mazauna wuraren da abin ya shafa su tanadi hanyoyin ficewa daga yankunansu domin tsira da rayuwarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta yi gargadi cewa garuruwa 915 da ke cikin jihohi 19 da Babban Birnin Tarayya (FCT) na cikin babban hadarin ambaliyar ruwa tsakanin 27 ga Agusta zuwa 9 ga Satumba, 2026.
Cibiyar Tsarin Gargadi na Farko kan Ambaliyar Ruwa ta Kasa ce ta bayyana hakan a sabon rahotonta kan hadarin ambaliya, inda ta ce garuruwan na bukatar kulawa ta gaggawa, shiri da daukar matakan kariya.

Source: Getty Images
Jihohin da ke fuskantar babban hadari
The Cable ta ce rahoton ya ware garuruwa 429 da ke cikin jihohi bakwai a cikin babban hadari, yayin da aka sanya wasu kauyuka 656 da ke cikin jihohi 13 cikin jerin wuraren da ke cikin matsakaicin hadarin ambaliya.
Jihohin da ke fuskantar hadarin sun hada da Kogi, Benue, Rivers, Edo, Delta, Cross River, Bayelsa, Akwa Ibom, Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu, Imo, Ekiti, Lagos, Ogun, Ondo, Osun da Oyo.
Manyan biranen da ke cikin hadari
Manyan birane da ke cikin jerin wuraren da ke cikin babban haɗarin sun hada da Lokoja, Makurdi, Fatakwal, Benin, Asaba, Calabar, Yenagoa, Uyo, Aba, Onitsha, Enugu, Owerri, Lagos Island, Abeokuta, Akure, Osogbo da Ibadan.
Gwamnatin ta danganta hasashen hadarin ambaliyar da yawan danshin kasa, ruwan sama mai yawa, saurin kwararar ruwa a saman kasa, cunkoson ruwa a magudanan ruwa da kuma karuwar cikar koguna.
A cikin sanarwar da darektan sashen kula da zaizayar kasa, ambaliyar ruwa da yankunan bakin teku, Usman Abdullahi Bokani, ya sanya wa hannu, an bukaci mazauna yankunan da ke cikin babban hadari su kasance cikin shirin ko-ta-kwana.
An kuma shawarci jama’a da su kare gidaje da muhimman kayayyaki, tare da guje wa zama, ajiye motoci, kasuwanci ko adana kaya a filayen da ambaliya ke mamaye wa, dausayi, gefen koguna da kuma wuraren da ruwa ke taruwa.
Gwamnati ta ba jama'a shawara
Gwamnati ta umarci hukumomin kula da aukuwar iftila’i na jihohi, jami’an kula da muhalli da masu sa ido kan ambaliya a al’umma da su kara sanya ido a koguna, rafuka, magudanan ruwa, gadoji, bututun ruwa, tafkunan ruwa da wuraren da ke fuskantar zaizayar kasa.
An shawarci garuruwan da aka sanya cikin babban hadari a jihohin Benue, Kogi, Kwara, Niger, Adamawa, Taraba da Kebbi su kara tsaftace magudanan ruwa tare da sanya ido kan bututun ruwa da hanyoyin kwararar ruwa.

Source: Facebook
An sanya Abuja da kuma Nasarawa, Plateau, Bauchi, Borno, Gombe, Yobe, Zamfara, Sokoto, Katsina, Kano da Kaduna cikin jerin wuraren da ke cikin matsakaicin hadarin ambaliya, in ji rahoton Daily Post.
Gwamnati ta yi gargadin cewa ci gaba da ruwan sama na tsawon lokaci ko ruwan sama a jere na iya kara hadarin ambaliya cikin gaggawa a al’ummomin da yanzu aka sanya cikin matsakaicin hadari.
Ambaliya ta kashe mutane a Nepal, China
Kun ji cewa masu aikin ceto a Nepal da China na ci gaba da neman kusan mutane 3,000 da suka ɓace bayan ambaliyar ruwa da ta mamaye wasu yankunan Himalaya.
Rahotanni sun ce an gano gawarwaki 633 a kasashen biyu, yayin da ake fargabar wasu daga cikin mutanen da suka mutu za su iya gangarawa zuwa India
Asali: Legit.ng


