Sojojin Najeriya Sun Tarfa Yan Ta'adda Fiye da 20 a Daji, Sun Yanke Masu Hukunci nan Take
- Dakarun sojojin Operation HADIN KAI sun kashe ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP 21 a jihar Adamawa
- Rahotanni sun ce jami'an tsaro sun kai samamen ne a maboyar ‘yan ta’addan da ke yankin tsaunin Kopre
- Baya ga kashe mayakan, dakarun sojin sun lalata sansanin ‘yan ta’addan tare da kwato bindigogin AK-47 da alburusai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Adamawa - Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation HADIN KAI, sun kashe ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP 21 a wani samame da suka kai a tsaunin Kopre, Karamar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa.
An gudanar da aikin ne a wani samamen bincike da ceto da ake ci gaba da yi domin gano tare da kubutar da mutanen da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su.

Source: Facebook
Leadership ta rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa, Mukaddashin Jami’in Yada Labaran Sojoji na Operation HADIN KAI, Kyaftin Mohammed Goni.
Ya ce dakarun ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da sababbin sojojin Bataliya ta 226 ne suka gudanar da samamen.
Goni ya ce dakarun, bisa sahihan bayanan sirri da umarnin Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, sun kutsa cikin yankin mai matukar wahalar shiga tare da kaddamar da hari kan sansanin ‘yan ta’addan da safiyar ranar 27 ga Agusta, 2026.
Ya ce aikin wani bangare ne na kokarin gano tare da ceto mutanen da ‘yan ta’addan ke tsare da su, ciki har da mutanen da aka yi garkuwa da su daga Mussa a watan Mayu da kuma daliban makarantar Lassa da aka sace a watan Yuni.
Sojoji sun fafata da ‘yan ta’addan
A cewar Goni, dakarun sun yi arangama da ‘yan ta’addan a lokuta biyu daban-daban bayan sun yi nasarar isa kusa da sansanin.
“Bayan kazamin gumurzu, an hallaka ‘yan ta’adda sama da 21, yayin da wasu da dama suka tsere dauke da raunukan harbin bindiga,” in ji shi.
Goni ya ce daga bisani dakarun sun mamaye yankin, suka rusa sansanin ‘yan ta’addan tare da lalata kayayyakin aikin da ke da alaka da shi, lamarin da ya kara raunana karfin kungiyar na gudanar da ayyukanta a yankin.

Source: Original
Sojoji sun rage karfin yan ta'adda
A yayin binciken wurin, dakarun sun kuma lalata babura da dama, kekuna da jarkunan man fetur, wadanda ake kyautata zaton ‘yan ta’addan na amfani da su wajen jigilar kayayyaki da zirga-zirga.
Dakarun sun kwato bindigogin AK-47 da dama, harsasai na AK-47 da kuma dimbin alburusai kirar 7.62mm Special.
Motar sojoji ta kashe mutane a Taraba
A wani labarin, kun ji cewa wasu ’yan kasuwa biyar sun rasa rayukansu bayan wata motar sojoji kirar Hilux ta kwace wa direba, ta afka cikin wata kasuwa a Taraba.
Motar tana rakiyar ’yan kasuwa ne daga Wukari zuwa Takum saboda yawaitar hare-haren ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a hanyar.
Asali: Legit.ng

