Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'addan Boko Haram da ISWAP, an Kashe Mayaka da Dama
- Dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ’yan Boko Haram da ISWAP sama da 21 yayin wani samame a yankin Kopre Mountain na jihar Adamawa
- An kai farmakin ne yayin da sojoji ke gudanar da aikin ceto mutanen da ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su a Mussa da Lassa
- Dakarun sun lalata sansanin ’yan ta’addan tare da kwato bindigogin AK-47, harsasai da wasu kayayyakin da ake amfani da su wajen gudanar da ayyukan ta’addanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Hong, Adamawa - Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai sun kashe sama da ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP 21 a jihar Adamawa.
Dakarun sojojin sun kashe 'yan ta'addan ne a wani samame da suka kai kan sansanin ’yan ta’addan a yankin tsaunin Kopre Mountain da ke karamar hukumar Hong ta jihar Adamawa.

Source: Twitter
Sojoji sun farmaki sansanin ’yan ta’adda
Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Hedikwatar Joint Task Force North East, Operation HADIN KAI, Kyaftin Mohammed Goni, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa . shafin X.
Mohammed Goni ya ce sojojin da suka gudanar da aikin sun hada da jami’an Tactical Team na Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro, ONSA, da sababbin jami’an Bataliya ta 226 da aka tura Sector 4 a jihar Adamawa.
Ya ce sojojin sun samu sahihan bayanan sirri kafin su kutsa cikin yankin da ke da wahalar shiga.
A karkashin umarnin Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, sojojin sun kutsa cikin yankin a hankali tare da kai farmaki kan sansanin ’yan ta’addan da sanyin safiyar Alhamis, 27 ga Agusta 2026.
An yi aikin ceto Mutanen da aka sace Kyaftin Goni ya ce aikin ya kasance wani bangare na kokarin gano tare da kubutar da mutanen da ’yan ta’addan ke tsare da su.
Ya ce wadanda ake kokarin ceto sun hada da mutanen da aka yi garkuwa da su a kauyen Mussa a watan Mayu, da kuma daliban makarantar Lassa da aka sace a watan Yuni. A cewarsa, bayan da sojojin suka isa sansanin, sun yi arangama da ’yan ta’addan sau biyu.
“Bayan kazamin artabun, an hallaka ’yan ta’adda sama da 21, yayin da wasu da dama suka tsere dauke da raunukan harbin bindiga,” in ji shi.
An lalata sansanin ’yan ta’addan
Goni ya ce bayan kammala artabun, sojojin sun mamaye yankin tare da rusa sansanin ’yan ta’addan da kuma lalata kayayyakin more rayuwa da suke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu. Ya ce hakan ya kara raunana karfin ’yan ta’addan na gudanar da ayyukansu a yankin.
A yayin binciken wurin, sojojin sun lalata babura da dama, kekunan hawa da kuma jarkokin man fetur, wadanda ake zargin ’yan ta’addan suna amfani da su wajen safarar kayayyaki da zirga-zirga.
An kwato bindigogi da harsasai
Dakarun sun kuma kwato bindigogin AK-47 da dama, magazinan AK-47 da kuma dimbin harsasan 7.62mm Special.
Kyaftin Goni ya ce nasarar aikin ta nuna kwarewar dakarun wajen amfani da dabarun yaki, tattara bayanan sirri da kuma kai karfin soji zuwa yankunan da ke da wahalar shiga.
Ya kara da cewa aikin ya nuna yadda dakarun ke da damar gano tare da lalata sansanonin ’yan ta’adda, tare da hana masu tayar da kayar baya samun damar gudanar da ayyukansu cikin walwala a yankin.
Rundunar soji ta yaba wa dakarun
Babban Hafsan Sojin Ƙasa ya yabawa jami’an ONSA Tactical Team da dakarun Operation HADIN KAI bisa jarumtakarsu, kwarewa, juriya da kuma kyakkyawan hadin gwiwar da suka nuna yayin gudanar da aikin.
Rundunar ta ce irin wannan hadin gwiwa na daga cikin matakan da ake dauka domin ci gaba da matsa wa ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP lamba tare da kubutar da mutanen da suke tsare da su.

Source: Original
Amurka za ta janye sojojinta daga Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa ma’aikatar tsaron Amurka, Pentagon, na shirin janye kusan sojoji 200 daga Najeriya, yayin da aka sanya lokacin tafiyarsu.
Sojojin na Amurka na cikin waɗanda aka tura ƙasar a wannan shekara domin taimakawa wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.
Asali: Legit.ng


