Abin Tausayi: 'Yan Mata 'Yan Gida Daya Sun Rasu a Hatsarin Kwale Kwale a Kano
- ’Yan mata uku daga gida ɗaya sun mutu bayan kwale-kwalen da suke ciki ya kife a tafkin Tiga Dam da ke Kano
- Wadanda suka riga mu gidan gaskiyar Murjanatu, Atikatu da Bilkisu, wadda aka fi sani da Amira, ’yan asalin Yalwan Rugu-Rugu ne
- Hukumar kashe gobara ta Kano ta ce ba a sanar da ita hukumance game da hatsarin ba a lokacin da aka haɗa rahoton
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - 'Yan mata uku daga gida ɗaya sun rasa rayukansu bayan kwale-kwalen da suke ciki ya kife a Tiga Dam da ke Jihar Kano.
'Yan matan da suka riga mu gidan gaskiyar ’yan asalin ƙauyen Yalwan Rugu-Rugu ne, da ke ƙaramar hukumar Tudun Wada ta jihar.

Source: Original
An bayyana sunayen waɗanda suka rasu
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana ranar Asabar, 29 ga watan Agustan 2026 kamar yadda shugabar ƙaramar hukumar Tudun Wada kuma shugabar ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Kano, Hajiya Sa’adatu Salisu Soja Maijama’a, ta bayyana a shafinta na Facebook.
An bayyana sunayen ’yan matan da suka rasu da Murjanatu, Atikatu da Bilkisu, wadda aka fi sani da Amira.
An yi ta'aziyyar rasuwar 'yan matan
Shugabar ƙaramar hukumar ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayiyar da kuma al’ummar yankin bisa wannan babban rashi.
Ta kuma roƙi Allah Ya gafarta wa waɗanda suka rasu, Ya ba iyalansu da ’yan uwansu ƙarfin jure wannan babban rashi.
Ta rubuta cewa:
"Assalamu Alaikum, a madadin al’ummar karamar hukumar Tudunwada, na ke amfani da wannan dama na mika sakon ta’aziyya ta ga al’ummar garin Yalwan Rugu-Rugu musamman ga wanda ya rasa ‘ya ‘yansa: Murjanatu, Atikatu, da Bilkisu (Amira)"
"Bisa iftila’in kifewar Kwale-kwale a Dam din Tiga, muna addu’ar Allah ya karbi Shadarsu, ya jikan su, yayi musu Rahma. Muna adduar Allah ya kiyaye gaba, Allah Ya bawa iyaye da ‘yan uwa da abokan arziki hakurin rashin su. Amin!."
Hukumar kashe gobara ba ta samu rahoto ba
Daily Trust ta ce da aka tuntubi kakakin hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya ce hukumarsa ba ta samu sanarwa a hukumance kan hatsarin ba.
Ya bayyana cewa hukumomin ƙaramar hukumar Tudun Wada ko mazauna yankin ba su tuntubi hukumar ba domin sanar da ita faruwar lamarin.

Source: Facebook
A cewarsa, ma’aikatan hukumar sun samu labarin hatsarin ne kawai bayan ganin sanarwar da shugabar ƙaramar hukumar ta wallafa a kafafen sada zumunta.
Saminu ya ce hukumar za ta fitar da sanarwar hukuma tare da ɗaukar matakin da ya dace da zarar ta samu cikakken bayani a hukumance kan lamarin.
Kwale-kwale ya yi hatsari a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jirgin ruwa na kwale-kwale dauke da mutane da dama ya gamu da hatsari a jihar Sokoto.
Ana tunanin akalla mutum 40 sun mutu bayan kwale-kwalen da ke ɗauke da manoma zuwa gonakinsu na shinkafa ya kife a garin Gorau da ke ƙaramar hukumar Goronyo.
Asali: Legit.ng

