WAEC, UNN, NYSC: An Tono Sabon Batu Kan Peter Obi, An Tafi Kotu Kan Ingancin Takardun Karatunsa
- Mamba a jam’iyyar Labour Party (LP), Mista Abayomi Arabambi, ya shigar da kara a babban kotun tarayya da ke Abuja kan takaddun shaidar karatun Peter Obi
- Mai shigar da karar yana neman umarnin kotu domin tilasta wa WAEC, UNN, da NYSC fitar da sakamakon binciken takaddun shaidar karatun dan takarar shugaban kasar na NDC
- Arabambi ya bayyana cewa binciken yana da muhimmanci domin sanin gaskiya da rikon amana ga mutanen da ke neman mukaman gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
ABUJA — Sha'anin takaddun shaidan karatun dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Mista Peter Obi, ya sake ballewa. Wannan ya biyo bayan shigar da korafe-korafe uku a Babban Kotun Tarayya da ke Abuja.
Korafe-korafen suna neman umarnin kotun ne a kan Hukumar WAEC, Jami'ar UNN, da kuma Hukumar NYSC. Mai shigar da karar yana son kotu ta tilasta musu mika kwafin takaddun shaidar karatun Peter Obi, Vanguard ta ruwaito.
Mamban jam'iyyar Labour Party (LP), Mista Abayomi Arabambi, shi ne ya shigar da wadannan korafe-korafe. Ya yi hakan ne saboda zargin cewa, hukumomin da abin ya shafa sun ki amsa bukatar sakin shaidar karatun Obi, daidai da Dokar Yancin Samun Bayanai (FOI) ta shekarar 2011.

Source: Facebook
Lokutan da aka shigar da karar
An shigar da karar WAEC mai lamba FHC/ABJ/CS/2064/2026 da ta NYSC mai lamba FHC/ABJ/CS/2063/2026 a ranar 1 ga Satumba. Ita kuwa karar UNN mai lamba FHC/ABJ/CS/2144/2026, an shigar da ita ne a ranar 9 ga Satumba.
Mai shigar da karar ta bakin lauyansa, Mista Anderson Asemota, ya bayyana cewa ba ya bukatar kotu ta tantance ko takaddun na gaskiya ne ko na bogi. Yana neman a bayyana ainihin bayanan hukumomin ne kawai domin sanin gaskiyar lamarin.
Arabambi ya fada wa kotun cewa ya rubuta wasiku zuwa ga hukumomin yana bukatar bayani game da takaddun Obi. Ya bayyana cewa hukumomin ba su amsa bukatar tasa ba, kuma ba su ba da wani dalili na kin fitar da bayanan ba.
A cewar mai shigar da karar, bayanan suna da muhimmanci ga muradun jama'ar Najeriya. Suna kuma iya taimakawa wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana ga masu neman mukaman gwamnati.

Kara karanta wannan
2027: Yan takarar gwamna a Kano da jihohi 6 sun ɗauki matsaya kan dawo da tallafin fetur
Abubuwan da yake bukata kotu ta yi
Yana rokon kotu ta tilasta wa WAEC mika masa ingantaccen kwafi (CTC) na Takaddar WAEC mai lamba SC042560 ta Obi Gregory Onwubuase ta watan Yunin 1978.
Sannan yana rokon kotu ta tilasta wa UNN fitar da kundin rajistar takaddar jami'a da bayanan sakamakon karatu masu alaƙa da Takaddar Digiri mai lamba D000198.
Haka zalika, ya bukaci kotu ta ba NYSC umarnin ba shi damar duba bayanan "Takaddar NYSC mai lamba 203495," wadda aka bai wa Obi a ranar 1 ga Mayun 1986.
Wata kitimurmura da ta bayyana
Bukatar ta kuma nemi bayani game da hanyar da sunan "Peter-Onwubuase" a madadin "Peter Obi" ya bayyana a bayanan NYSC na dan takarar.
WAEC ta ki amincewa da bukatar sakin bayanan a ranar 11 ga Agusta bisa dogaro da sassan Dokar FOI. Su kuwa UNN da NYSC ba su amsa bukatar ba kwata-kwata.
Mai shigar da karar yana son kotu ta tabbatar cewa kin amincewar hukumomin kuskure ne, sannan ta ba da umarnin fitar da bayanan. A halin yanzu, ba a tsaida ranar da za a saurari korafe-korafen ba.
Asali: Legit.ng
