'Ba da Yawun Musulmin Najeriya ba': ADC Ta Soki Malamai kan Neman a Zabi Tinubu

'Ba da Yawun Musulmin Najeriya ba': ADC Ta Soki Malamai kan Neman a Zabi Tinubu

  • Jam’iyyar ADC a Jigawa ta yi watsi da goyon bayan da wasu malaman addinin Musulunci sama da 500 suka nuna goyon baya ga shugaban kasa
  • Jam’iyyar ta ce ba daidai ba ne a bayyana irin wannan matsaya ta siyasa a matsayin ra’ayin al’ummar Musulmin Najeriya baki daya
  • ADC ta kalubalanci Gwamnatin Tarayya kan batun tsaro da ayyukan raya kasa, tana mai cewa har yanzu hare-haren ta’addanci sun sako jama'a a gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jam’iyyar ADC reshen Jihar Jigawa, ta yi watsi da goyon bayan da sama da malaman addinin Musulunci, limamai da masu wa’azi 500 suka bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Malaman sun bayyana cewa suna goyon bayan yan Najeriya su sake zaben Bola Ahmed Tinubu ya yi wa'adi na biyu a mulkin Najeriya a zaben 2027.s

Kara karanta wannan

Kalaman Sanata Yari sun fusata ADC, ta yi zazzafan martani game da mulkin APC

ADC ta ga laifin malamai da ke goyon bayan Tinubu da yawun addini
Shugaban kasa Bola AHmed Tinubu, Bolaji Abdullahi mai magana da yawun ADC Hoto: Bayo Onanuga/Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

Arise News ta wallafa cewa Malaman sun bayyana matsayinsu ne a wani taro da suka gudanar a Dutse, jihar Jigawa a karshen makon da ya gabata.

Matanin ADC ga malamai kan Tinubu

Daily post ta kawo labarin cewa sai dai ADC ta bayyana matakin a matsayin abin takaici, tare da gargadin shugabannin addini da kada su bari muradun siyasa su rage musu ’yancin kai, mutunci da kuma tasirin da suke da shi a cikin al’umma.

A cikin wata sanarwa da Jakadan Matasa na ADC na Arewa, kuma mataimakin shugaban jam’iyyar a Jigawa, Ambasada Nuraddeen Suleiman Jidawa, ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce kowane malamin addini yana da damar yin zabin siyasa.

Sai dai ADC ce bai kamata a gabatar da irin wannan matsaya a matsayin hukuncin addini ko ra’ayin al’ummar Musulmin Najeriya baki daya ba.

ADC ta tabo matsalar tsaro

Jam’iyyar ta kuma kalubalanci wasu bayanai da aka bayyana a cikin sanarwar da aka fitar bayan taron, musamman ikirarin cewa gwamnatin Tinubu ce ta fara aikin layin dogo na Kano-Dutse/Kano-Maradi.

Kara karanta wannan

Gwamna ya dauki zafi da yan bindiga suka kai mummunan hari masallaci ana cikin Sallah

ADC ta ce har yanzu akwai tarin matsaloli da Tinubu ya gaza magance wa
Shugaban ADC na kasa, Sanata David Mark Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

A cewar ADC, an amince da aikin tare da bayar da kwangilarsa ne a shekarar 2021 a lokacin gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Jam’iyyar ta kalubalanci Gwamnatin Tarayya karkashin jam’iyyar APC da ta bayyana manyan ayyukan raya kasa da gwamnatin Tinubu ta fara tare da kammala su yadda ya kamata a Jihar Jigawa.

ADC ta kuma yi watsi da ikirarin cewa an samu gagarumin sauyi wajen inganta tsaron kasar, musamman a yankin Arewa maso Yamma.

Jam’iyyar ta kawo hare-haren satar mutane da na ’yan ta’adda da aka kai a jihohin Kaduna, Sokoto da Zamfara a matsayin hujjar cewa matsalar rashin tsaro har yanzu na ci gaba da zama babban kalubale ga ’yan Najeriya.

ADC ta hango matsala a Jigawa

A baya, kun samu labarin cewa jam’iyyar ADC ta yi gargadin cewa faɗaɗa harkokin haƙar ma’adinai a Jigawa na iya buɗe ƙofa ga ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa 6, malaman addini 500 sun bayyana dan takarar shugaban kasarsu a 2027

Jam'iyyar ADC ta buƙaci a dakatar da sababbin ayyukan haƙar ma’adinai har sai an gudanar da cikakken binciken tsaro tare da samar da isassun matakan kariya domin zaman lafiya.

Jam'iyyar ta ce zaman lafiyar da Jigawa ke da shi abu ne mai muhimmanci da ya kamata a kare, maimakon jira har sai ƙungiyoyin yan ta'adda da na 'yan bindiga su lalata shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng