Zargin Safarar Kwayoyi: Tinubu Ya Roki Kotun Amurka kan Shirin Sake Bayanansa

Zargin Safarar Kwayoyi: Tinubu Ya Roki Kotun Amurka kan Shirin Sake Bayanansa

  • Shugaba Bola Tinubu ya roki alfarma a bukatar Ma’aikatar Shari’a ta Amurka na neman karin kwanaki 10 kan zargin safarar kwayoyi
  • Alkalin kotun Amurka Beryl Howell ya amince da karin kwanaki hudu kacal, inda ta tsawaita wa’adin zuwa 21 ga Agusta
  • Lamarin ya samo asali ne daga bukatar Aaron Greenspan ta FOIA, yayin da kotun ta umarci FBI da DEA su fitar da bayanan bincikensa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya shiga cikin bukatar Ma’aikatar Shari’a ta Amurka na neman karin kwanaki 10 domin mayar da martani kan umarnin kotu.

Umarnin ya shafi sakin bayanan da suka shafi zarge-zargen da aka yi wa Tinubu na hannu cikin fataucin miyagun kwayoyi.

Tinubu ya roki kotun Amurka karin kwanaki game da sake bayanansa na binciken zargin safarar kwayoyi
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da ake zargi a Amurka. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Lauyan Tinubu, Christopher Carmichael, ya shigar da sanarwar shiga bukatar a madadin shugaban Najeriya a wata kotun tarayya da ke Amurka, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Tinubu ya dauki sabon mataki kan tsaro, ya ba da wa'adin kwanaki 90

Korafin da Atiku ya yi kan zarge-zargen

Kamfanin Von Batten-Montague-York L.C., wani kamfanin fafutukar siyasa da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya dauka, ne ya wallafa kwafin sanarwar.

A cikin sanarwar, lauyan Tinubu ya bukaci a ba da karin kwanaki 10 domin gabatar da martani kan bukatar yanke hukunci a shari’ar.

Sanarwar ta ce Tinubu ya shiga bukatar wadanda ake kara, inda ya nemi a ci gaba da tafiyar da martanin kowa bisa jadawalin guda.

Sai dai kamfanin ya bayyana cewa mai karar ya yi adawa da bukatar, yayin da wanda ake kara bai nuna adawa ba.

Kamfanin ya kuma yi zargin cewa Tinubu na son amfani da jinkirin wajen neman taimakon abokansa a Washington domin nuna cewa sakin bayanan zai iya lalata dangantakar Amurka da Najeriya.

Atiku ya taso Tinubu a gaba kan zargin fataucin kwayoyi
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Tun yaushe ake zargin Tinubu a lamarin?

A shekarun 2022 da 2023, Aaron Greenspan, wani Ba’amurke kuma wanda ya kafa PlainSite, ya gabatar da bukatun FOIA guda 12 ga hukumomin gwamnatin Amurka shida.

Kara karanta wannan

Umarnin da Tinubu ya ba EFCC game da kuɗaɗen da hukumar ke ƙwacewa

Greenspan ya nemi bayanan binciken laifuka kan wata kungiyar fataucin hodar iblis da ta yi aiki a Chicago a farkon shekarun 1990, cewar Punch.

Ya nemi bayanan bincike kan mutane hudu da ake zargin suna da alaka da kungiyar, ciki har da Bola Tinubu.

Sauran mutanen su ne Lee Andrew Edwards, Mueez Abegboyega Akande da Abiodun Agbele.

Zargin da ya shafi Tinubu da fataucin miyagun kwayoyi a Amurka a shekarar 1993 ya kasance daya daga cikin batutuwan da suka jawo ce-ce-ku-ce gabanin zaben shugaban kasa na 2023.

A shekarar 1993, Tinubu ya mika dala 460,000 ga gwamnatin Amurka sakamakon wani lamari da ya shafi zargin fataucin kwayoyi.

Atiku ya kalubalanci Tinubu kan batar N4tr

A wani labarin, an ji cewa Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da dora wa gwamnatocin baya alhakin matsalar matatun man fetur na Najeriya duk da shi ne a mulki.

Dan takarar shugaban kasa a ADC ya ce gwamnatin yanzu ta kamata ta yi bayani kan makudan kudin da aka kashe wajen gyaran matatun.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce bashin da matatun man Fatakwal, Warri da Kaduna ke bin NNPCL ya karu zuwa Naira tiriliyan 8.67 a 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.