Gwamnati Ta Hango Matsala, Ribadu Ya Yi Gargadi kan Barazanar Tsaro a Wasu Wurare

Gwamnati Ta Hango Matsala, Ribadu Ya Yi Gargadi kan Barazanar Tsaro a Wasu Wurare

  • Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu ta yi kira ga ’yan Najeriya su ƙara taka-tsantsan da ɗaukar matakan kariya
  • Ribadu ya ce sanarwar ta biyo bayan ayyukan sojoji, tattara bayanan sirri da sa ido kan barazana, tare da haɗin gwiwar abokan hulɗa
  • Ofishin Ribadu ya bukaci jama’a su kai rahoton mutane ko abubuwan da suke zargi, su zauna cikin natsuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, ONSA, ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da taka-tsantsan tare da ɗaukar matakan kariya.

Hukumar ta bayyana cewa akwai buƙatar jama’a su kasance cikin shiri game da yiwuwar matsalolin tsaro a wasu wurare da ke cikin ƙasar.

Ribadu ya yi gargadi kan barazanar tsaro a Najeriya
Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu. Hoto: Nuhu Ribadu.
Source: Facebook

An bayyana hakan ne cikin wata sanarwar tsaro da ONSA ta fitar, da aka rabawa hukumomin tsaro domin ɗaukar matakan da suka dace, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Sojoji sun rutsa yan ta'adda masu karɓar kudin fansa a jihar Kebbi

Kwafin sanarwar da aka samu sun ce an fitar da ita ne sakamakon ci gaba da kai hare-hare da jami’an tsaro ke yi.

Haka kuma, sanarwar ta ce jami’an tsaro na ci gaba da tattara bayanan sirri da sa ido kan barazanar tsaro tare da haɗin gwiwar abokan hulɗa na cikin gida da ƙasashen waje.

Sanarwar mai kwanan wata 27 ga Agusta ta ambaci kashe mayaƙan ƙungiyar Islamic State West Africa Province, ISWAP, ciki har da kwamandansu, Abubakar Mainok.

An bayyana kashe Mainok a matsayin ɗaya daga cikin nasarorin da jami’an tsaro suka samu a cikin ayyukan da suka gudanar a watannin baya.

Legit Hausa ta ruwaito cewa an kashe Mainok, wanda aka fi sani da Abu Bilal al-Minuki, da mayaƙansa a wani samame na haɗin gwiwar sojojin Najeriya da Amurka.

An kashe mayaƙan ne a watan Maris, lokacin da dakarun haɗin gwiwar suka kai farmaki kan sansaninsu da ke wani tsibiri a Borno.

ONSA ta ce sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da hukumomin tsaron Najeriya ke ci gaba da gudanar da ayyuka a Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Amurka za ta janye sojojinta daga Najeriya, an sanya lokacin kwashe su

Hukumar ta ce ayyukan sun samu gagarumar nasara wajen tunkarar ISWAP da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka a sassan yankunan.

Ta ƙara da cewa ayyukan sun kai ga hallaka wasu kwamandojin ’yan ta’adda da ’yan bindiga, ciki har da Abubakar Al-Mainok, wanda aka fi sani da Abu Bilal Al-Minuki.

Haka kuma, an tarwatsa sansanoni, maboyar ’yan ta’adda da sauran wuraren da ƙungiyoyin masu aikata laifuka ke amfani da su a wurare daban-daban.

Dalilin fitar da sanarwar tsaro

ONSA ta ce ƙungiyoyin ta’addanci na iya ƙoƙarin kai hare-hare na daban domin haifar da fargaba ko kuma jawo hankalin jama’a.

Duk da irin asarar da aka yi wa ƙungiyoyin ta’addanci, rahoton ya ce har yanzu suna ci gaba da kai hare-haren ƙungiyoyin daba kan sansanonin sojoji.

Hare-haren sun haɗa da kai wa fararen hula da manyan tituna hari a sassan arewacin Najeriya, yayin da ƙungiyoyin ke ƙoƙarin faɗaɗa ayyukansu.

Saboda haka, ONSA ta shawarci jama’a da su kasance cikin taka-tsantsan a kowane lokaci tare da kula da yanayin tsaro a wuraren da suke zaune.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya ba Hausawa, Fulani shawara da alakarsu ke neman baci

Hukumar ta buƙaci gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi su ƙarfafa sa ido a cikin al’umma tare da tallafa wa matakan dakile barazanar tsaro.

'Mu na murkushe yan bindiga' - Ribadu

An ji cewa yayin da yan bindiga ke kai hare-haren kare dangi a wasu yankunan jihar Kaduna da wasu kauyuka a Najeriya, gwamnatin tarayya ta ce ta na kokari.

Mashawarcin shugaban kasa a kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya bayyana irin nasoririn da gwamnatin Bola Tinubu ta samu wurin kare rayuka.

Ya buƙaci al'umma su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro bayanan sirri domin suna da matukar muhimmanci wajen aikin kare rayukansu da dukiyoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.