Amurka Za Ta Janye Sojojinta daga Najeriya, an Sanya Lokacin Kwashe Su
- Pentagon na shirin janye kusan sojojin Amurka 200 da aka tura Najeriya domin taimakawa wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya
- Rahotanni sun ce kananan tawagogin masu horaswa da masu nazarin bayanan sirri za su ci gaba da kasancewa a Najeriya bayan babban rukunin ya bar ƙasar
- Amurka ta ce har yanzu za ta ci gaba da haɗin gwiwar tattara bayanan sirri da Najeriya, duk da rage yawan sojojinta a ƙasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ma’aikatar Tsaron Amurka, Pentagon, na shirin janye kusan sojoji 200 daga Najeriya, yayin da aka sanya lokacin tafiyarsu.
Sojojin na Amurka na cikin waɗanda aka tura ƙasar a wannan shekara domin taimakawa wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.

Source: Facebook
Jaridar New York Times ce ta ruwaito hakan ranar Alhamis, 27 ga watan Agustan 2026 bisa bayanan wasu jami’an Amurka da Najeriya.
Rahoton ya ce duk da ƙarancin adadin sojojin da aka tura, jami’an Amurka da na Najeriya sun bayyana cewa aikin nasu ya haifar da gagarumar nasara.
Wasu jami’an za su ci gaba da zama
A cewar rahoton, ana sa ran babban rukuni na sojojin zai bar Najeriya zuwa ƙarshen watan Satumba.
Sai dai ƙananan tawagogin masu horas da jami’an tsaro da masu nazarin bayanan sirri za su ci gaba da kasancewa a ƙasar domin tallafa wa ayyukan tsaro.
Jami’an Amurka sun bayyana yadda aka gudanar da aikin a Najeriya a matsayin wani tsari da za a iya amfani da shi wajen gudanar da wasu ayyukan soji na Amurka a nahiyar Afirka nan gaba.
An rage sojojin Amurka bayan kashe jagoran ISIS
A watan da ya gabata, Dagvin Anderson, kwamandan Rundunar Sojin Amurka mai kula da Afirka, AFRICOM, ya bayyana cewa Amurka ta janye da dama daga cikin sojojinta da ke Najeriya, cewar rahoton jaridar TheCable.
Ya ce hakan ya biyo bayan wani samame da aka gudanar a watan Mayu, wanda ya yi sanadin kashe Abu-Bilal al-Minuki, wanda aka bayyana a matsayin na biyu a shugabancin ISIS a yankin Tafkin Chadi.
Anderson ya ce samamen ya raunana shugabancin ISIS sosai a Najeriya da ma sauran sassan duniya.
Ya kuma bayyana cewa Najeriya ta kasance mai matuƙar himma tun bayan samamen, musamman wajen ƙoƙarin hana ’yan ta’addan dogaro da kansu wajen samun kuɗi da sauran abubuwan da suke buƙata. Sai dai ya ce Amurka za ta ci gaba da haɗin gwiwar tattara bayanan sirri da Najeriya.
Amurka da Najeriya na tattaunawa kan Tsaro
Wannan ci gaba ya zo ne makonni kaɗan bayan Amurka da Najeriya sun gudanar da zagaye na biyu na tattaunawa a Washington.
Tattaunawar ta gudana ne ƙarƙashin wani rukuni na haɗin gwiwa da aka kafa domin tattauna hanyoyin kare al'ummomin Kirista a yankin Middle Belt na Najeriya.
An kafa wannan rukuni ne bayan Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kira Countries of Particular Concern (CPC), bisa zargin fuskantar kisan kiyashin Kiristoci.
Waɗannan zarge-zarge sun kasance cikin abubuwan da suka sa Amurka ta ƙara mayar da hankali kan ayyukan tsaro a Najeriya.

Source: Twitter
Amurka na horar da sojojin Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojin Amurka ta fara horas da sojojin Najeriya kan amfani da jirage marasa matuka, kula da wadanda suka samu raunuka a fagen daga da sauran dabarun aikin soja.
An gudanar da horarwar ne a jihar Bauchi a matsayin wani bangare na yunkurin kara karfafa hadin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.
Asali: Legit.ng


