Abubuwa 10 da Ya Kamata Ku Sani kafin Sayen Hannun Jarin Matatar Dangote

Abubuwa 10 da Ya Kamata Ku Sani kafin Sayen Hannun Jarin Matatar Dangote

Akwai akalla muhimman abubuwa 10 da ya kamata masu zuba jari su fahimta kafin su saka kudin su a tayin da matatar Dangote ta yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos – Shirin sayar da hannun jarin Matatar Dangote ya jawo hankalin masu zuba jari a Najeriya, musamman bayan amincewar Hukumar Kula da Kasuwar Hannun Jari ta Najeriya (SEC).

Kamfanin na shirin sayar da hannun jari biliyan 4.1 a farashin N525 kan kowane guda, wanda zai iya samar da kusan Naira tiriliyan 2.15 idan aka sayar da dukkan hannun jarin.

Matatar Aliko Dangote
Wani bangare na matatar Dangote a Legas. Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Amma kafin mutum ya zuba kuɗinsa, akwai muhimman bayanai da ya kamata ya fahimta domin sanin damar da ke akwai da kuma haɗarin da zai iya fuskanta.

Kara karanta wannan

Bayani dalla dalla kan yadda za ku saye hannun jari a matatar Dangote

1. Hannun jarin na iya tara N2.15tn

A farashin N525 kan kowane hannun jari, sayar da hannun jari biliyan 4.1 na iya samar da kusan Naira tiriliyan 2.15.

Vanguard ta wallafa cewa wannan zai sanya tayin cikin manyan cinikin hannun jari da aka taɓa samu a tarihin kasuwar hannun jarin Najeriya.

2. Za ku zama masu hannun jari

Bayanai sun nuna cewa sayar da hannun jarin ga jama'a zai sauya dangantakar da ke tsakanin 'yan Najeriya da matatar.

Maimakon matatar ta kasance wani rukuni na mutum mai zaman kansa kaɗai ya mallaka, jama'a za su samu damar mallakar kaso a kamfanin ta hanyar sayen hannun jari.

Masu hannun jari na iya samun riba idan darajar hannun jarin ta ƙaru ko kuma kamfanin ya bayyana cewa zai raba riba ga masu hannun jari.

3. Saye ba ya nuna za a ci riba

Daya daga cikin muhimman abubuwan da mai son zuba jari ya kamata ya fahimta shi ne cewa farashin N525 na lokacin tayin ba yana nufin hannun jarin zai ci gaba da kasancewa a wannan farashin ba.

Kara karanta wannan

'Kowa zai iya saye,' Dangote ya bude kofar sayar da hannun jari a matatar shi

Bayan an fara ciniki da hannun jarin a kasuwa, farashinsa zai dogara da buƙata da yawan hannun jarin da ake son sayarwa, da kuma ribar kamfanin da yanayin tattalin arziki.

Farashin na iya tashi idan masu zuba jari suka ga kamfanin na samun ci gaba, amma kuma zai iya faɗuwa idan tsammanin samun riba ya ragu.

4. Yanayin karfin matatar

Matatar Dangote da rukunin masana'antun sinadarai da ke Ibeju-Lekki a Legas sun mamaye fili mai girman kusan hekta 2,635.

A halin yanzu, matatar tana da ikon tace ganga 700,000 na ɗanyen mai a kowace rana, abin da ya sanya ta cikin matatun da ke da mafi girman layin tace mai guda ɗaya a duniya.

Wannan girman aiki yana bai wa masu zuba jari damar shiga kasuwancin da zai iya sarrafa ɗanyen mai mai yawa tare da samar da kayayyakin man fetur ga kasuwannin cikin gida da na ƙasashen waje.

5. Batun fadada matatar

Kamfanin yana gudanar da shirin faɗaɗa matatar wanda ake sa ran zai ƙara ƙarfin tace mai daga ganga 700,000 zuwa ganga miliyan 1.4 a kowace rana.

Kara karanta wannan

Kamfanonin wuta sun karbi N1.2tr a hannun 'yan Najeriya cikin watanni 6

Idan aka kammala shirin yadda ya kamata, zai ninka ƙarfin matatar fiye da sau biyu tare da sanya ta cikin matatun da suka fi girma a duniya.

Ƙarin ƙarfin samarwa na iya haifar da ƙarin kayayyakin da ake samarwa, ƙarin kuɗin shiga da kuma damar samun kuɗin waje ta hanyar fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.

6. Kamfanin yana da fadi

Rahotanni sun bayyana cewa damar zuba jari da kamfanin ya ke da shi jarin ba ta tsaya kan tace man fetur kaɗai ba.

Rukunin masana'antun ya haɗa da masana'antar polypropylene mai ƙarfin samar da tan 900,000 a shekara, tashar samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 435, da kuma manyan wuraren ajiye kayayyaki.

Tsarin ajiya na kamfanin ya ƙunshi tankuna 177 da ke da damar adana kusan lita biliyan 4.742.

Kamfanin yana kuma da tashar ruwa ta musamman da aka tsara domin inganta sufuri da jigilar kayayyaki, ciki har da wuraren da jiragen ruwa masu girman Panamax za su iya amfani da su.

Alhaji Aliko Dangote
Aliko Dangote yana bayani a taro a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

7. Kasuwa za ta iya fadada

Najeriya na cikin manyan ƙasashen Afirka masu samar da ɗanyen mai, amma tsawon lokaci ta dogara sosai kan shigo da tataccen man fetur daga ƙasashen waje saboda ƙarancin ƙarfin matatun cikin gida.

Kara karanta wannan

Jamhuriyar Nijar ta faɗi ƙasashen da take zargi da yunkurin yi mata juyin mulki

Idan ta bunkasa, matatar za ta iya biyan wani babban kaso na buƙatar man fetur na Najeriya tare da samar da kayayyaki da za a fitar zuwa kasuwannin ƙasashen waje.

Sai dai ribar da kamfanin zai samu za ta dogara da abubuwa da dama, ciki har da samun ɗanyen mai, farashin man fetur, farashin duniya, kuɗin gudanar da aiki da yanayin kasuwar fitar da kayayyaki.

8. Fahimtar tsarin mallakar hannun jarin

SEC ta yi rajistar hannun jari na yau da kullum biliyan 120.13 da ke akwai, yayin da shirin tayin jama'a ya ƙunshi hannun jari biliyan 4.1.

Saboda haka, masu zuba jari ya kamata su duba takardar bayanin tayin hannun jarin kafin su yi rajista domin fahimtar kaso na kamfanin da za a bai wa jama'a.

Haka kuma ya kamata su duba haƙƙoƙin da ke tattare da hannun jarin, yawan hannun jarin da zai kasance a hannun jama'a da kuma yadda mallakar kamfanin za ta kasance bayan kammala tayin.

9. Ribar da za a iya samu

Duk da girman matatar da kayan aikin da take da su, abin da ya fi muhimmanci ga mai zuba jari shi ne yadda kamfanin zai iya samar da riba da kuɗin shiga masu ɗorewa.

Kara karanta wannan

Yadda aka jefar da jarirai a kango cikin ban tausayi bayan an haife su a Abuja

Daga cikin abubuwan da ya kamata a sanya ido akwai ƙaruwar kuɗin shiga, yawan man da ake tacewa, ƙarfin amfani da masana'anta, kuɗin gudanarwa, basussuka da sauransu.

Haka kuma akwai haɗarin samun ɗanyen mai, sauyin darajar Naira, farashin man fetur a duniya, sauyin dokoki, kuɗin gyaran masana'anta da kuma gasa a kasuwannin cikin gida da na waje.

Saboda haka, ko da yake matatar na da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin Najeriya, masu zuba jari ya kamata su yi nazari sosai kafin su tantance darajarta a matsayin jari.

10. Bunkasar kasuwar zuba jari

Wani muhimmin abu game da wannan tayin shi ne yadda zai iya sauya dangantakar 'yan Najeriya da manyan kamfanonin cikin gida.

Idan aka samu nasarar fara cinikin hannun jarin, daidaikun mutane, asusun fansho, manyan masu zuba jari da sauran masu ruwa da tsaki za su mallaki kaso a kamfanin da ke gudanar da ɗaya daga cikin manyan ayyukan masana'antu a Afirka.

Hakan na iya ƙara harkokin kasuwanci a kasuwar hannun jarin Najeriya tare da ƙarfafa wasu kamfanoni su shiga kasuwa domin tara jari na dogon lokaci.

Kara karanta wannan

Ana batun rahoton Tinubu, Amurka ta saki sunaye da hotunan 'yan Najeriya 4 da suka tafka laifi

Ga ƙananan masu zuba jari, wannan tayin na iya zama babban gwaji kan yadda 'yan Najeriya za su iya saka wani kaso na ajiyarsu a manyan kamfanonin cikin gida idan suka ga damar samun riba.

Matakan sayen hannun jari

A wani labarin, mun ruwaito cewa masu son sayen hannun jarin Matatar Dangote za su fara ne da buɗe asusun dillalin hannun jari tare da wani dillali da SEC ta amince da shi.

Bayan haka, ana buƙatar buɗe ko haɗa asusun CSCS, inda za a riƙa adana hannun jarin ta hanyar lantarki bayan an raba su ga masu saye.

Mai zuba jari zai kammala tantance bayanansa, ya saka kuɗin da ake buƙata a asusun, sannan ya gabatar da buƙatarsa ta hanyar hanyoyin da aka amince da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng