Ta Faru Ta Kare: Sojoji Sun Shiga Maboyar Kasurgumin Dan Bindiga, Kachalla Muhammadu
- Dakarun sojojin Operation Fansan Yamma sun kara samun nasara a kokarin da suke yi na wanzar da zaman lafiya a Arewa maso Yamma
- Sojojin sun samu nasarar kama wasu mutum uku da ake zargin suna taimaka wa yan bindiga, sannan sun kai hari maboyar Kachalla Muhammadu Fulani
- Bayanai sun nuna cewa dakarun sun kwato mugayen makamai tare da lalata wuraren da yan ta'addan ke amfani da su a Kaduna da Katsina
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Sojojin rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation Fansan Yamma, sun cafke wasu mutane uku da ake zargin masu taimaka wa ’yan ta’adda ne.
Haka zalika dakarun sojojin sun kuma lalata maboyar ’yan ta’adda da dama a wasu samame daban-daban a jihohin Kaduna da Katsina.

Source: Twitter
The Nation ta ruwaito cewa a samamen da aka gudanar a ranakun 27 da 28 ga Agusta, 2026, sun cafke makamai da alburusai, tare da kwato bututun RPG-7, babur, wayoyin hannu da wasu kayayyaki.
An kama masu taimakon yan bindiga
A Jihar Kaduna, sojojin Sector 1 sun yi amfani da bayanan sirri wajen cafke wani mutum da ake zargin mai taimaka wa ’yan ta’adda ne.
An kama wanda ake zargin ne dauke da bindigogi biyu kirar gida da kuma harsasai 13 da ya boye a cikin jaka.
A cewar rundunar sojin, binciken farko ya nuna cewa an ba wanda ake zargin aikin kai makamai da alburusan ga wani mutum.
Bayan bayanan da wanda ake zargin ya bayar, sojojin sun kaddamar da wani samame na bibiyar lamarin, wanda ya kai ga cafke wasu mutane biyu da ake zargin suna da alaka da safarar makaman.
An mika mutanen ukun da kayayyakin da aka kwato ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da gudanar da bincike.
Sojoji sun shiga maboyar Kachalla
A Jihar Katsina, sojojin Sector 2 tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, sun gudanar da samamen share yankin a ranar 28 ga Agusta a Maharba da Karaduwa da ke Karamar Hukumar Matazu.
Samamen ya mayar da hankali ne kan maboyar ’yan ta’adda da aka gano, da kuma gine-ginen da ake zargin ana amfani da su wajen gudanar da ayyukan ta’addanci.
Sojojin sun share tare da lalata maboyar, ciki har da wata maboya da ake zargin tana da alaka da fitaccen shugaban ’yan ta’adda, Kachalla Muhammadu Fulani.
Rundunar sojin ta ce dabar Kachalla Muhammadu Fulani ta dade tana addabar mazauna kananan hukumomin Matazu da Musawa.

Source: Facebook
Sai dai rahotanni sun ce kasurgumin dan bindigan ya tsere yayin da sojojin ke ci gaba da matsawa zuwa maboyarsa, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.
Daga bisani, sojojin sun gudanar da sintirin yaki a yankin domin karfafa nasarorin da aka samu tare da hana ’yan ta’addan sake haduwa ko dawo da ’yancin yin zirga-zirga.
Sojoji sun kashe yan ta'adda 21
Kun ji cewa dakarun sojojin Operation HADIN KAI sun kashe ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram/ISWAP 21 a jihar Adamawa.
Sojoji sun samu wannan nasara ne a wani aikin samamen bincike da ceto da ake ci gaba da yi domin gano tare da kubutar da mutanen da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su.
Asali: Legit.ng


