Nasara daga Allah: Yan Bindiga da Yawa Sun Bakunci Lahira a Jihar Sakkwato

Nasara daga Allah: Yan Bindiga da Yawa Sun Bakunci Lahira a Jihar Sakkwato

  • Jami'an tsaro sun yi nasarar fatattakar yan bindiga da suka yi yunkurin kai hari kauyen Sifawa a karamar hukumar Bodinga ta Sakkwato
  • Rahotanni sun nuna cewa an kashe wasu daga cikin ’yan bindigar yayin musayar wuta da jami’an tsaro
  • Dakarun Sojoji biyu sun samu raunuka, yayin da ake ci gaba da farmakin sama kan ’yan bindigar da suka tsere

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto, Nigeria - An yi artabu tsakanin jami’an tsaro da ’yan bindiga a Sifawa da ke karamar hukumar Bodinga a Jihar Sakkwato a ranar Laraba, bayan maharan suka yi yunkurin mamaye garin.

Sifawa ce mahaifar tsohon Shugaban Rundunar Sojin Najeriya, Laftanal Janar Faruk Yahaya mai ritaya, da kuma Sakataren Gwamnatin Jihar Sakkwato, Barista Bello Sifawa.

Sojoji.
Dakarun rundunar sojin Najeriya a bakin aiki Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Rahotannin da Daily Trust ta ruwaito sun ce ’yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 10 na safe, amma sojoji da ’yan sanda da aka girke a yankin sun fatattake su.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gamu da matsala har a majalisa daga nadin kwamitin yakin neman zabe

Yadda aka fatattaki ’yan bindigar

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce maharan sun fito ne daga Horo, wani kauye da ke karamar hukumar Shagari, inda suka yi yunkurin mamaye barikin sojoji da ke Sifawa.

Ya ce an shafe sa'o'i ana musayar wuta kafin sojojin suka samu galaba a kansu.

“Sun yi fada na tsawon sa'o'i, amma daga bisani sojoji suka yi galaba a kansu. An raunata sojoji biyu kuma tuni aka garzaya da su asibiti domin yi musu magani.
“Muna ganin an kashe da dama daga cikin ’yan bindigar yayin artabun, yayin da wasu suka tsere ta cikin gonakin gero,” in ji mazaunin.

Shugaban kungiyar raya Sifawa, Dr Abubakar Boyi, wanda ya tabbatar da harin, ya ce mai yiwuwa ’yan bindigar sun kawo harin ne domin satar dabbobin jama'a.

“Akwai dabbobi da yawa da mutanen da ’yan bindiga suka raba da muhallansu a Shagari suka kawo Sifawa,” in ji shi.

Kara karanta wannan

An gano adadin mutanen da yan bindiga suka hallaka a harin masallatan Neja

Mahara sun yi kokarin shiga barikin sojoji

Wata majiyar tsaro ta ce babban abin da ’yan bindigar suka nufa shi ne barikin sojojin da ke Sifawa, kamar yadda Leadership ta rahoto.

“Sun so su mamaye barikin, amma sojoji suka yi galaba a kansu. An raunata sojoji biyu kuma aka kai su asibiti domin yi musu magani,” in ji majiyar.
Sojoji.
Jami'an rundunar sojojin Najeriya suna motsa jiki s fagen daga Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Majiyar ta kara da cewa an fara wani farmakin sama a dazuzzukan da ake kyautata zaton ’yan bindigar da suka tsere sun fake.

“Ana ci gaba da kai hare-haren sama a dazuzzukan da ’yan bindigar suka tsere. Na tabbata an kashe da dama daga cikinsu. Bayan kammala aikin, za mu gudanar da samame domin zakulo sauran,” in ji majiyar.

Sojoji sun kara zafafa hare-hare

A wani labarin, kun ji cewa Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta ƙara yawan hare-haren sama kan ’yan ta’adda, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Arewa maso Yamma.

Rundunar ta ƙara yawan jiragen yaƙi da sa ido a Jihar Sokoto domin tallafa wa ayyukan haɗin gwiwa na jami’an tsaro da ke kokarin kakkabe taaddanci

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262