Zaben 2027: Daliban Manyan Makarantun Arewa Sun Yi Matsaya kan Goyon Bayan Tinubu

Zaben 2027: Daliban Manyan Makarantun Arewa Sun Yi Matsaya kan Goyon Bayan Tinubu

  • Daliban manyan makarantun gaba da sakandare a jihohin Arewa sun cimma matsaya kan zaben shekarar 2027
  • Sun nuna goyon bayansu ga shirin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na neman tazarcen domin ci gaba da mulki a zaben 2027
  • Goyon bayan na su na zuwa ne yayin da wasu malaman jami'o'i a jihohin na Arewa suka nuna suna tare da Shugaba Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ɗaliban manyan makarantun gaba da sakandare daga jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ajandar Renewed Hope.

Sun yi alƙawarin ƙara wayar da kan ɗalibai da matasa kan shirye-shiryen gwamnatin tarayya gabanin zaɓen 2027.

Tinubu ya samu goyon baya
Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Legit Hausa ta fahimci cewa shugabannin ƙungiyoyin ɗaliban sun bayyana matsayinsu ne yayin ƙaddamar da A4A Students’ Wing.

Kara karanta wannan

Siyasar Kaduna ta dauki zafi, makusantan El Rufai sun koma wajen Uba Sani a APC

An bude dandalin matasa dalibai

A4A Students Wing wani sabon dandali ne da zai haɗa shugabannin ɗalibai daga manyan makarantun Arewa domin ƙarfafa tsarin jagoranci, wayar da kai, sadarwa da shiga harkokin siyasa tsakanin matasa.

A yayin taron, Shugaban SUG na Jami’ar Bayero Kano kuma jagoran A4A Students’ Wing, kwamared Abdulmudallib Kalli Sheriff, ya ce goyon bayan ɗaliban ga Tinubu ba na bikin ƙaddamarwa kawai ba ne.

Ya bayyana cewa za su gina hanyar sadarwa da za ta kai saƙon Renewed Hope zuwa cibiyoyin karatu a faɗin Arewa.

Hakazalika ya ce ɗalibai ba sa son ci gaba da kasancewa masu kallo a siyasa, sai dai su zama masu ruwa da tsaki wajen tsara makomar ƙasar.

An yaba wa shirye-shiryen Tinubu

Sheriff ya ce shirye-shiryen gwamnatin Tinubu kamar NELFUND, ayyukan raya manyan makarantu, bunƙasa fasahar zamani, sufuri da shirye-shiryen ƙarfafa matasa sun samar da sababbin damammaki ga ɗalibai.

Kara karanta wannan

Tinubu na ta samun goyon baya a Arewa, manyan malaman jami'o'i 600 sun bayyana matsayarsu

Ya ce shirin NELFUND ya taimaka wajen rage matsin kuɗin karatu ga ɗaliban da iyalansu ke fuskantar matsalar kuɗi.

Badaru ya yabi Tinubu

Da yake jawabi a wajen ƙaddamarwar, Darakta Janar na A4A kuma tsohon Gwamnan Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, ya ce ɗalibai su ne ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan makomar siyasar Arewa.

Ya ce A4A ba ta neman goyon bayan matasa bisa alkawura kawai, sai dai tana son a yi amfani da abubuwan da gwamnati ta riga ta aiwatar a matsayin hujjar bayyana ayyukanta.

Badaru ya kawo misalan tallafin NELFUND, inda ya ce sama da ɗalibai miliyan 1.5 sun samu damar cin gajiyar tallafin da ya haura Naira biliyan 282.

Dalibai sun amfana da Tinubu

Ya kuma ambaci ayyukan TETFund a jami’o’i da sauran manyan makarantu na Arewa, ciki har da cibiyoyin ICT, dakunan kwanan ɗalibai, dakunan gwaje-gwaje, gine-ginen koyarwa da cibiyoyin CBT.

Ya kuma yi nuni da shirin Energizing Education Programme (EEP), wanda ya samar da megawatt 36.2 na makamashin hasken rana ga jami’o’i bakwai a Arewa, da kuma shirye-shiryen matasa kamar 3 Million Technical Talent Programme (3MTT), Nigeria Jubilee Fellows Programme da Nigerian Youth Investment Fund (NYIF).

Kara karanta wannan

Kurunkus: Tinubu, Atiku da Peter Obi sun bayyana hanyar da suka samu dukiyoyinsu

A cewarsa, irin waɗannan shirye-shirye na nuna ƙoƙarin gwamnati wajen zuba jari a ilimi, ƙwarewar matasa da samar da damar aiki.

Tinubu ya samu goyon baya
Mohammed Badaru tare da shugabannin dalibai Hoto: Abdulmudallib Sheriff
Source: Facebook

Daga ƙarshe, shugabannin ɗaliban sun ce za su yi amfani da tsarin A4A Students’ Wing wajen haɗa ɗalibai daga cibiyoyin karatu daban-daban, wayar da kan matasa kan harkokin ƙasa da kuma ƙarfafa musu gwiwa su shiga siyasa cikin tsari.

Sun jaddada cewa miliyoyin matasan Arewa na da muhimmiyar rawa wajen tantance makomar siyasar Najeriya a 2027.

Malamai mata sun goyi bayan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa malamai mata na jihohin Arewa sun amince da sake zaben Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ce malaman sun yaba wa Tinubu saboda irin ci gaban da ya samu a bangarorin ilimi, ayyukan more rayuwa, kiwon lafiya da noma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng